Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

6. DOKA, TUSHEN ZAMAN LAFIYA (Mutadaarak)

Nazarin Aruli:
Bahari: Mutadaarak
Ƙafa Maimaitau:Faa’ilun faa’ilun faa’ilun (5, 5, 5)
Fiɗa: - v - / - v - / - v -
____________________________
1. Na yaba Rabbi mai jin kira
Jalla, Allahu mai gafara
Kauda duk muguwar ƙaddara
Ga ni bawa ina yin bara
Ba mu doka a Nijeriya.
2. Zamani ne na yau zan faɗa
Ƙin biyayya jahala daɗa
Zuciya har idan ta kaɗa
Ba abun yi awa ai faɗa
Babu zancen zaman lafiya.
3. Zan yi zance kamar shaguɓe
Yau fa doka mu san ta zube
Duk ƙasa ga shi an rarrabe
Masu mulki suna lalube
Yanda za mui zaman lafiya
4. Gaskiya zan faɗa ƙa’ida
Lalube ba shi yin fa’ida
Lafiya za ta zo har gida
Babu ƙarya bare za’ida
Gun Aliyu maso gaskiya.
5. In ka so zan kwatanta maka
Lafiyar duniya nan duka
Yin gini ne cikin ayyuka
Ginshiƙi tubali bincika
In da kyawu gini lafiya.
6. Tubali in ya bend ka jiya
Du gini za ya zam laulaya
Ko siminti a ce bai jiya
Babu ƙarfi tsayo zai wuya
Sai zubewa ga baki ɗaya.
7. Duk ƙasashe muhimmai gama
Masu yalwa da daɗin zama
Cigabansu a ƙas har sama
La sihir kullaha innama
Sun bi dokarsu ba zamiya.
8. Ƙa’ida ce suke bi duka:
Ɗora doka bisa kayuka
Martaba, dukiya, rayuka
In ka take su ka sha daka
Rayuwa yari ba lafiya.
9. Kowane gunsu daidai shi ke
Mai talauci biyayya ya ke
Maikuɗi, tajiri bai sake
In ya laifi hukunci ake
Martaba ba ta sa yafiya.
10. In ƙasa ka ga ta sunkuya
Ka ga manya suna yin tsiya
Ba tsaron rai bare dukiya
Cin mutuncin mutum ba wuya
Kar ka sa ran zaman lafiya.
11. Gu da dama a Ifriƙiya
Sa kudanci na Sudaniya
Har ƙasar tamu Nijeriya
Libya sa Santa Ifriƙiya
Babu doka bare gaskiya.
12. Larabawa mutan Eshiya
Ga Yaman nan zuwa Syria
Afghanistan haɗo Chechniya
Ran mutum sai ka ce kurciya
Hargitsi ba zaman lafiya.
13. Mun daɗewa da shubka ƙasa
Mun zata cigaban duk ƙasa
An gina mu ko mun farfasa
Mun ɓarar ba rabo mun rasa
Sai nadamar marar gaskiya.
14. Farfaganda ta ƴanci: Ruwa!
Munka sha har muna yin rawa
Mun yi tatil muna yin juwa
Nan da nan munka wo mantuwa
Mun yi waƙa ta sharholiya:
15. “Yau talauci fa zai ɗaukaka
“Dukiyarmu rabon muduka
“Maida sarki abin caccaka
“Malami, tajiri su duka
“Martaba sai a jamhuriya.
16. Keta doka ya zam ƙa’ida
Gun mutane da yanci guda
Kangarewa adon maigida
Kan jimawa gari sai kiɗa
Rusa mulki muna fariya.
17. Ɗan talakka kamar tsautsayi
Ya yi mulkinsa mai laulayi
Tangaɗi, magiya, ga layi
Babu kishi abin tausayi
Cin amana da son danniya.
18. Babu doka ta kaya da rai
Martaba babu sai dai garai
Maguɗi ba shi zaɓen kwarai
Jahili ga shi nan sakarai
Ba shi ƙaunar maso gaskiya.
19. Da yana son zaman lafiya
Sai ya zamto riƙon gaskiya
Sanya doka da yin tarbiya
Masu laifi su zam sun biya
Ka ji tushen zaman lafiya.
20. Sai mu bunƙasa duk ayyuka
Baiwa yara abin ɗaukaka
Babu gilla da ƙwaya duka
Sai biyayya, rashin laifuka
Duk ƙasa kwance sai lafiya.
21. Mu talakka batun gaskiya
Inda son rai cikin zuciya
Hargitsi za shi zo ba wuya
Bin mu doka zaman lafiya
Ka ji kalma batun gaskiya.
22. Mas’ala ko idan ta zaka
Kar mu saurin zama harzuƙa
Mui ta haushi kamar karnuka
Keta doka muna hallaka
Rayuka, dukiya kun jiya?
23. Yanda doka ta ce ƴan’uwa
Za mu tai inda mai unguwa
Hakimi ba bari har zuwa
Can ga sarkin ƙasa mui kuwa
Don muna son zaman lafiya.
24. In ko laifi akai wa ƙasa
Dukiya ko ko rai an rasa
Kotu ce za ta yanke masa
Rayuwa ƙa’ida ce musa
Hankali za mu zam lafiya.
25. Mui ta watsi da duk rarraba
Mui haɗewa da juna gaba
Mu jama’a zuwa shugaba
Rayuwa babu ko fargaba
Za ta dawo kamar can jiya.
26. In ko cewa muke mun ƙiya
Kowane zai bi son zuciya
Yi da gangan muna fariya
Babu doka a Nijeriya
Ture zancen zaman lafiya.
27. Masu laifi iri ɗai suke
Masu biro kisa ma suke
Shi da harbi ka bar bincike
Zuciya mai biɗar mallake
Duniya ba zaman lafiya.
28. Dukiya, martaba, rayuka
Kar mu ɓata ukun su duka
Gun kalami mu bar zantuka
Duk amana mu zan mun riƙa
Mui ta himmar zaman lafiya
29. Nai kira yau ga Sarki ɗaya
Kai salama ga duk duniya
Agazawa ga Nijeriya
Don mu zamna cikin lafiya
Dukkanin mu ga baki ɗaya.
30. Zan taƙaita a gun nan haka
Ga talatin da ɗai baituka
Fa’ilun, Fa’ilun bincika
Gargaɗi gun mazo laifuka
Masu rushe zaman lafiya.
31. Nai kira Rabbi kai sallama
Kansa manzo daɗo sallama
Kan iyaye ka zan ka gama
Har da mu duk cikin sallama
Duniya, Lahira duk ɗaya.
Tammat walhamdulillah.
24 ga Fabrairu 2015

No comments: