Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

FURE, SANIYATA

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Madid: ( - v - - /- v - /- v - -)

1. Za ni fara tambayar Maisarauta
Ya Ta’ala gani zan yo yabonta
Saniyata Rab biyan duk bukata
Baitukan bahrin Madid ba yawaita
Don maso kiwo su zam fa’idanta.
2. Saniyata ya Fure kyautatawa -
Ce ta Allah gun Ali ba musawa
Tun da farko gun uwa an yabawa
Haihuwa duk shekara ba tsayawa
Har da nono mai yawa ba kamarta.
3. Ga ko ‘ya’ya masu sauri a girma
Ba kamarsu cib suke babu rama
Lafiya duk safiya har da yamma
Cin abinci duk kala babu kyama
Ga sumul ba kwarzano d’ai a fata.
4. Sai na ce wannan iri kyau gare shi
Ya kamata in yawaita kamar shi
Fa’idarwa ce a kiwo zan bido shi
In yi nono mai yawa, kasuwar shi
In ta kyawu zan biya duk bukata.
5. Nan wurin zan tsaya don bayani
Ga uwar bunaji ce “White Fulani”
Dole ne in ko yi baye ta ba ni
Karsanar nono yawa tai da launi
Haihuwa har ma ta zarce uwarta.
6. Ba Muturu ba Abore, Bunaji
Duk wadannan ba kamar Bokoloji
Ba da nono ko gida ko a daji
Ga yawan fata tuli nan a kirji
Za ta rayu ko ina don halinta.
7. Mun yi Anchau kasuwa ran Talata
Ya Ilahi! Na ga shanu dubata
Ga Gudale ga bunaji halarta
Mun yi zabe mun biya kan fahimta
Ya yi daidai don biyar duk bukata.
8. Nan gida shanu suna kan jirarsa
Saurayi dan santali duk jikinsa
Sun taho gunai su zam sunsunarsa
Karbuwa tai sun yabon hankalinsa
Kan jimawa ya biya duk bukata.
9. Haihuwarsu har Fure ba dadewa
Haihuwarta ga jiki zan na shawa
Ta yi “gold” launinta sai dai yabawa
Ta yi fata har da gashin abawa
Ga jiki girma da sauri a gunta.
10. Mun yi reno mun kula don salama
Cutuka duk don guje wa nadama
Ga abinci babu rama alama
Ga “Chloris” ga su dusa da “cake” ma
Ga ruwa nan har da gun kwanciyarta.
11. Za a gasa wa ka nono cikinsu
Na yi falgore, kwana kasuwarsu
Juma’a duk ci suke kowanensu
Bokoloji karsanu anka kamo
Kan kwabo Mansur ya kawo a mota.
12. An ciyarsu sun k’iba don a shirya
Za a bayensu na turai fiyayya
Don a sam shanu na nono ladayya
Frisiana an yi shaidar a dunya
Ba da nono ba kamarsu a mata.
13. Can Bokos ne“Milkway” an sayo shi
Kai! Baleri, yai jiki don da koshi
Ya tsaya cak duk sifa ba kamarshi
Shekaru kau shekara tak gareshi!
Sai ka ce yai bakwai ba kumaita.
14. Sai Fureta tai ciki har k’awaye
Mun watanni har tara kai a waye
Dukkaninsu haihuwa ba hawaye
Ga bijimmai karsanu duk a raye
Godiyata gunsa sarkin bukata.
15. Ga Fure nan ta yi ‘ya mai jikinta
Yar gajera! Ta yi launin uwarta
Ta yi hantsa tim da nono gare ta
Za a tatsa ai mayawa wajen ta
Ba tsayo, kyautarsa Sarkin halitta.
16. Sai Fure tai gardama: k’in tsayawa
Don a tatsa ko a kofi ba iyawa
Ta rike, nonon ba ta sakewa
Na yi roko gunsa Maiyassarewa
Zan kawarwa, Rabbi duk gardamarta.
17. Nai rubutun sha na bayar kan lalura
Basmala nai, fatiha har tabara
Nai K’urayshi, sai salati duk na k’ara
“War Fure am! Yardu bindi”, ishara
De’itin, Jooman a jaabo da simta.
18. Kan uku d’ai sai k ace yi laya!
Ta natsu ba gardama sai biyayya
Safiya duk sai tazo ba kiyayya
Babu dauri babu komai mad’iyya
Bar ta nono ta riba kan uwarta.
19. Masu kiwo kun ga sirri dukan ku
In kuna so sai ku ban hankalinku
Dan bayani zan yi don fa’idarku
Sai ku zabi don ku sa ka’idarku
Gun ukun nan kui guda don bukata.
20. In bukatar kiwata ne yawaita
Sai ku kiwo zan Fulani yawaita
In ko nono ko ko nama nufata
Sai ku inganta da baye ga mata
Sai ku san ba ya Boklo wadata.
21. Don Gudale na da nono da nama.
Kan Bunaji ko Abore ya kama
Karsana ce za ta nono da dama
In miji ne za ya nama da himma
Kowane ne anka yo ba talauta.
22. Masu karfin aljihu za su shawa
Su bijimman nan na Turai bidowa
Ko aluran nan ta A. I. bayawa
Kan Bunaji ko Gudale, Aborwa
Inda lura nan da nan a rabauta.
23. Ga misali gun Fure yar amana
Gun jinninta barbarar “Boklo-Buna”
Can uwarta Buna ce in ka auna
Ga diyar “Buna-maso-Frisiana”
Za a nono mai yawa du a gunta.
24. Gun uwa an tatsi lita biyar ne
Gun Fure litarta har sha biyar ne
Gun diyar kau za ya d’ora ka gane
In da kiwo ai ka ce nan da nan ne
Yan watanni ka ga ta kai bukata.
25. Shekara d’ai ka ga ta kai a bi ta
In miji ne za shi girma ya bi ta
Saniya duk in ta zam mai maraita
Babu nono mai yawa zan cire ta
Kai wa bangaro ya yanka Talata.
26. In ko ka san ba ka kurdi da tsoka
Ko ko ba loto na lura da kanka
Kar giyar Naira da buri su kaika
Yin “cross”, kai tanadin yan-k’asarka
In da cuta ko ko rani za su data.
27. Ka gane ni na yi kiwo a yara
Yau da girma na yi garke da yara
Dukkaninmu za mu mike mu gyara
Shan ruwansu kwanciyarsu da shara
Za mu shubka can a gona hakinta.
28. Masu aiki kowane zai ta nema
Ga Sulena zai yi tatsa da himma
Zai yi feshi zai yi ban magani ma
Za ya ba su ba shi ki ba nadama
Dan amana ka ji pullo halitta.
29. Masu kiwo tun su Tsalha a goge
Sun yi aiki sun kula babu coge
Ba na yau ba tun na da can su Tounge
Tun su Sayid, shi da Langtang ka kirge
Sun kulawa na yaba godiyata.
30. Yau da Rayyan sa da Shamsu da Baba
Ga su Anwar jarumi bai tsaya ba
Ci da shanu damina ko da rab’a
Ko da sanyi ko dare bai gushe ba
Za su aiki saniya ba maraita.
31. Dukiya ce in da lura habakka
Ko halal ce babu lura ta barka
Duk yawanta ko dubu ta gujeka
Bar haramun ko da so ba ta barka
Sai ka tara sai ta tai duk yawanta.
32. Zan halalun kulla yaum duk wuyarsa
Ko kadan ne zai dadu banda wasa
Ba da hakki banda cuta ka rusa
Ko halal ce in da tir za ta kasa
Kyautatawa ba da hakki yawaita.
33. Zan kulawa ga misali gare mu
Dukiya ce za a tara ta k’aumu
An yi sata ba zaton ran kiyamu
Kan jimawa babu jari nadamu
Sai ko hakki sai hisab ba kubutta.
34. Rabbi njooman men ‘yami kulla khairu
Hisnumen fuu juul6e maa duuniyaaru
Fo6 kebal men hokku men barkid’eru
Guika shoyal jaudi fuu na du hairu
Hisnumen fuu, yaafoyaa yende fotta:
35. “Rabbi sarki taimaka man da khairu
“Zan tsaremu muslimai duniyaru
“Dukka nema sa halal babu sharru
“Dukiya duk in ta sata mudirru
“Zam tsare mu, gafara kan wafata.
36. Saniyata ba ta barka yawaita
In yi nono in yi nama rabauta
Kyan jininta har na yad’a makwabta
Har na nesa duk su zo don bidarta
In ko ba su taimako godiyata.
37. Ya mutane nai kira sai ku dawo:
Mu Arewa nai tuni mui ta kiwo
Duk sana’a ba kamar masu kiwo
Annabawa su duka sun yi kiwo
Tarbiya ce gun sa Sarkin kamata.
38. Na yi roko gun sa Allah mubini
Duk fitinnun masu kiwo mu’ini
Kau da su duk gun manoma Fulani
Sui fahimta sui zama fi amani
Lafiya ce inda kowa wadata.
39. Zan tsaya nan saniya nai wa waka
Baituka kau arba’in ne hakika
Kan Madid ne baitukan munka tuk’a
Fa’ilaatun faa’ilun faa’ilaata
Godiyata gun Sa Farkon-Gabata.
40. Zan salati sallama kan Muhammad
Har da ahlih har iyalin Muhammad
Har sahabbai har mabiya Muhammad
Kai iyaye har Ali gun Muhammad
Dada (Zainab) har Amira Muhammad
Ran da Allah ne kad’ai Maisarauta.
Tammat bihamdillah!
11 March 2015

No comments: