Total Pageviews

Saturday, January 20, 2018

PMB Da N,5000 Na Marasa Aikin Yi

Na Dr. Aliyu U. Tilde
Dazun nan na fito daga gewaya sai na iske wasu 'yanmata da na sani sun fito daga wata unguwa mai nisa wacce ba tasu ba. Ba a jima ba sai na ga wasu kuma. Sai na tambaya ina suke ta zuwa haka da sassafen nan. Sai suka ce mun za su rijistar N5,000 din da Buhari zai rika rabawa ne duk wata, wai haka aka aiko daga Bauchi. Waɗanda na yi magana da su sun ce mun an ɗau sunayensu yau amma sai ranar Laraba za a dawo don kammala yi musu rijista.
To ko maganar ta dubu biyar din Shugaba Buhari ne ko ma wani ne yake son ya damfari mutane, abin ya tuna min da wani dan majalisar jaha a mazaɓata da na taɓa bashi shawara bai ɗauka ba, hakan kuma ya haifar masa da matsala.
A lokacin, ɗan majalisar ya yi niyyar raba babura da wasu kayaki ga matasa a daba daba da muke da su a mazabarsa. Na ce masa kar ya yi haka don zai jawo masa baƙin jini. Dalilina shi ne in a daba guda mai mutum goma ya baiwa matashi guda babur, masalan, to ya fa sani sauran taran za su ƙi shi kuma ya rasa goyon bayansu ke nan. A ƙarshe in ya sake dawowa neman ƙuri’a ba za su goyi bayansa ba. A maimakon haka, gara ya yi wani abu da kowane matashi zai amfana da shi sannan in ya gamu da matasa ya riƙa musu ɗan alherin da ba a rasa ba yana basu haƙuri.
Haka kuwa aka yi da ya ƙi bin shawara ta. Nan da nan baƙin jini ya bi shi kuma kujerar da bai sake dawowa ba ke nan don wannan da wasu dalilai.
Ina guje wa Buhari faruwar irin wannan matsalar. Tabbas muna da matasa da tsoffi da yawa waɗanda basu da aikin yi. Suna cikin wahala da yawan ƙunci. Sun cancanci a taimake su. Amma a ganina duk shirin da za a taimaka musu da shi ya kamata ya kasance ya cika waɗannan sharuɗɗa biyar:
1) Akwai isassun kuɗin yin shirin musamman a cikin wannan lokacin da ake kukan ba kuɗin biyan ma’aikata
2) Tsarinsa shirin mai gudanuwa ne ba tare da ya gagara ba don yawan jami’an da ake buƙata ko yana da wata ƙofar-rago da ɓata gari za su yi amfani da shi wajen wawushe dukiyar jama’a ba
3) Mai ɗorewa ne ba wanda ba za a fara shi a daina ba don nauyinsa ko rashin kuɗi ko wasu matsaloli a wannan gwamnati ko waɗanda za su biyo ta.
4) Kowa zai amfana da shirin cikin waɗanda aka nufa da shi; in marasa aikin yi ne dole ya zame duk marasa aiki za su amfana da shi ba masu satifiket ba kadai, ko wasu su samu wasu su rasa; in matasa ne haka; in tsoffi ne haka. In ba haka ba, gwamnati za ta jawo wa kanta baƙin jin mai yawa.
5) Ba abin da zai jawowa wannan gwamnati ko wata mai zuwa matsala na siyasa ko tattalin arziki ba ne a yanzu ko wata rana.
In muka duba halin da wannan gwamnati ta samu asusun ƙasan nan, da yawan yan Nijeriya da ke cikin buƙata, da rashin gaskiya da ya wanzu a al’umma ta yadda hatta gwamnati da kanta ta kasa hana jami’an tsaronta karbar cin hanci da aikata zalumci balle in an kawo wani tsari da ya shafi kusan jama’a duka, ina ganin ba laifi ba ne ta jingine wancan alƙawarin da ta yi, ta yi wa mutane bayanin dalilan da ya sa ba zai yu ba, sannan ta duƙufa wajen yin abubuwan da kowa zai amfana da su kuma masu yiyuwa, kamar ci gaba da gyara wutar lantarki da zai sa masana’antu su dawo, tabbatar da an sai da kayayyakin makamashi kamar gas, fetur da kananzir a kan rahusa da kowa zai amfana, ta haɓaka ayyukan ma’adinai da aikin noma, da sauransu, kamar yadda take da niyya.
Wasu magoya bayan Shugaba Buhari za su ga kamar wannan shawara bata kamata ba don suna ganin duk abin da APC ta yi alƙawari a kai abin da zai yu ne kuma kuskure ne a ba shi shawara kar ya yi. A ganina da kuma ganin manyan marubuta kan siyasar mulki, ba laifi ba ne shugaba ya karya alƙawarin da ya ɗauka in ya ga cika alƙawarin ba zai yu ba ko zai jawo wa mulkinsa fitina. Hasali ma, yin haka na nuna kwarewar shugaba din wurin mulki. In APC ta yi alƙawari kafin ta karɓi mulki lokacin kamfen don bata san yadda tattalin arziki zai taɓarɓare haka ba, to yanzu ta sani. Ya kamata a mata uzuri ba a mata ingizata mai kantu ruwa ba kamar yadda ƴan PDP a majalisa suka so su yi kwanakin baya.
Hakaza alƙawarin da Ministan Gona ya yi kwanakin baya cewa gwamnatin Buhari za ta riƙa shayar da ƴan firamare lita guda na madara duk wayewar gari. In an duba yawan ɗaliban wanda ance sun kai miliyan talatin, da yawan kuɗin wanda ya kai N600 million a kowace ranar karatu, da yawan buƙatu da suka fi wannan muhimmanci a fannin aikin gona da ilmi, da rashin shanun da za su ba da wannan madarar, dss, sai a ga wannan shawarar ba abinda ya kamata ministan ya doshi Buhari da shi ba ne. Ya kamata gwamnatin Buhari ta yi watsi da tunani irin na gwamnatocin Obasanjo da Jonathan. Duk wanda ya san matsalolin ilmi a ƙasan nan ya san ciyar da yara a makaranta balle kuma shayar da su madara ba abin da za a tsaya a ɓata lokaci a kai ba ne balle kuɗi wanda babu su a yanzu.
Shawarata ga gwamnatin Shugaba Buhari ita ce ta duƙufa wajen gano matsalolin rayuwar ‘yan Nijeriya a fannuka dabam-dabam kuma ta azuma wajen warware waɗanda suka fi muhimmanci kafin lokaci ya ƙure. Haka kuma ta kiyayi maimaita kurakuran baya irin na ciyar da yara a makarantu daga matakin tarayya kamar yadda gwamnatocin su Obasanjo da Jonathan suka gwada amma suka watsar a ƙarshe. Wasu abubuwan kuma a bar wa gwamnatocin jahohi su yi in sun ga za su iya. Balle kuma baiwa marasa aikin yi N5,000 duk wata wanda daga dukkan alamu ba zai yu ba balle ya ɗore.
4 Janairu 2016

No comments: