Sunday, December 20, 2015

Arewa: Idan Ba Za Mu Girmama Doka Ba, Ba Za Mu Daina Ganin Bala'i Ba

Arewa: Idan Ba Za Mu Girmama Doka Ba, Ba Za Mu Daina Ganin Bala'i Ba

Duka rikice-rikicen da muke gani a Arewacin Nijeriya da talaucin da ya yi katutu a cikinsa ba za su kau ba sai ran da muka gane muhimmancin doka da bin ta.

Ba yadda za a yi a ce za a bar jama'a da kungiyoyin addini kowa ya yi ganin damansa kuma kasa ta zauna lafiya. In mun yi magana game da tauye hakkin sauran jama'a da ake yi ta fuskar addini a yi caa a kanmu kamar mun aikata kaba'ira.

Don Allah menene amfanin toshe hanya ga matafiya da kowane dalili balle da sunan addini? Wañnan wulakanta bil'adama ne da rashin ganin kimarsa. Ga shi muna gani kullum a muzaharori da tawagar malamai a manyan tituna da tarukan kasa na addini kala-kala. Mutane da ke da'awar karatu amma tunaninsu kamar wadanda ke rayuwa a kungurmin daji? Wallahi wannan abin takaici ne.

Yanzu menene amfanin abin da ya faru a Zaria jiya, yake faruwa yanzu haka a Gellesu? Menene amfanin taron addini in zai jawo salwantar rai guda daya tak ma? Shin dole ne? Salla ne ko azumi ko aikin hajji? Wañnan abin an yi shi ba sau daya ba ba sau biyu ba, rayuka suna hallaka. Meye amfanin kwakwalwar da take kanmu idan ba za mu yi tunani da ita ba mu gane abu mai amfani da maras amfani, abu mai cutarwa da kuma maslaha, ko kuma cewa zaman lafiya ya fi komai? Me ya sa ba mu dau zubar da jini a kan komai ba har ta kai a ko yaushe ba mu damu da janyo falilin zubarsa ba alhali muna da'awar addini?

A ce har Shugaban Sojojin Kasa na Nijeriya zai wuce a ki ba shi hanya bai da ce da dabi'armu ta girmama na gaba da mu ba. Kuma a kasa gane cewa haka yana iya jawo salwantar rayuka kamar yadda ya jawo a baya abin mamaki ne ga kowane mai hankali, balle kuma an hada da jifa da sauransu.

Ina ga ba inda haka zai faru a kudu. Sam. Amma mu siyasar tawaye ta yi karfi a tsakaninmu har muna ganin babu babba ba yaro. Kowa muka ga dama za mu ci mar mutunci babu damuwa. Balle kuma an yi wa addini fassarar tawaye. Shi ke nan, mahaukaci ya hau kura.

Su mutanen da ke da matsala da tsarin da ake ciki yanzu suna iya yin kaura zuwa inda za su yi rayuwa irin wacce suke so. Wannan haka ya ke ko a nassi. Amma ka ce ba za ka yi biyayya ga hukuma ba kuma kana zaune a kasarta, ko a zamanin da wannan almara ce kawai. Zabi biyu ne kawai: ko dai ka yake ta ko kuma ka zauna lafiya da ita. Period. Wannan dokar duniya ce tun fil azal kuma ba za ta canza ba har ta nade.

Allah sarki! Ga yanki mai mutane masu basira amma barandanci na addini da rashin wayewa ya tukuikuye tunaninsu sun kasa yi wa kansu tanadin alheri ko sa samu cigaba su fita daga kangin talauci. Ga yanboko - manyansu da yaransu - su kuma barayi, bakaken azzalumai kuma maciya amana. Su ma ba su dau doka a kan komai ba. Ka rasa ina za ka waiga ka ga sa'ida.
Mu sani doka ita ce zaman lafiya. Zama lafiya kuma shi ne komai. In kowa ya yi kokarin bin ta sai a ci gaba. In an ki, oho, mu ne dawaman cikin bala'i alhali sauran kasar na cigaba.

Wannan sharhi nawa kila wasu su gan shi ya yi zafi. Zafi ne da ta bijiro daga takaickn halkn da wadanda kake so suke ciki. A ui hakiri. Wannan kuma kamar yadda Al-Mutanabbi ya ce abin da ya kamaci duk tsayayye ke nan. Ba Dan Arewan da ke jin dadin taasar da ake tafkawa na kashe-kashe a Zaria a yanzu haka. Amma dole ya yi takaicin yadda ko yaushe muke tsaga bango don kadangaru su shiga.

Na ga wasu har sun fara karkata maganar zuwa zancen kisan da ake yi wai ko bai fi tsare hanya laifi ba. To ba haka maganar take ba. Na yi sharhi ne kan rashin bin doka da yin abubuwa wadanda suke haddasa tashin hankali. Tabbas kisa babban laifi ne. Amma me zai sa mutum ya yi tsokanan da zai jawo kisa? Tsokana kadai na iya jawo yakin duniya. Mutum ya kafa kungiyarsa ya je Oran ko Saudia ya tsokani Babban Hafsan Sojar kasar ya ga abin da zai same shi. Kungiyar ma idan bata yarda da gwamnati ko doka ba ba za a bari ta wanzu ba bare har ta yi karfin da za ta yi tsokana a fili.

Allah mun tuba. Allah mun tuba. Ka fid da mu daga wannan annoba ko na bayanmu za su samu su rintsa.

Aliyu

Friday, December 18, 2015

Doka Tushen Zaman Lafiya

6. DOKA, TUSHEN ZAMAN LAFIYA (Mutadaarak) ______________________________________

Nazarin Aruli:

Bahari: Mutadaarak
Kafa Maimaitau: Faa’ilun faa’ilun faa’ilun (5, 5, 5)
Fiɗa: - v - / - v - / - v -
____________________________

1. Na yaba Rabbi mai jin kira
 Jalla, Allahu mai gafara
 Kauda duk muguwar kaddara
 Ga ni bawa ina yin bara
   Ba mu doka a Nijeriya.

2. Zamani ne na yau zan faɗa
Kin biyayya jahala daɗa
Zuciya har idan ta kaɗa
Ba abun yi awa ai faɗa
  Babu zancen zaman lafiya.

3. Zan yi zance kamar shaguɓe
Yau fa doka mu san ta zube
Duk kasa ga shi an rarrabe
Masu mulki suna lalube
Yanda za mui zaman lafiya

4. Gaskiya zan faɗa ka’ida
 Lalube ba shi yin fa’ida
Lafiya za ta zo har gida
Babu karya bare za’ida
Gun Aliyu maso gaskiya.

5. In ka so zan kwatanta maka
 Lafiyar duniya nan duka
Yin gini ne cikin ayyuka
Ginshiki tubali bincika
  In da kyawu gini lafiya.
 
6. Tubali in ya bend ka jiya
 Du gini za ya zam laulaya
Ko siminti a ce bai jiya
Babu karfi tsayo zai wuya
Sai zubewa ga baki ɗaya.

7. Duk kasashe muhimmai gama
Masu yalwa da daɗin zama
 Cigabansu a kas har sama
La sihir kullaha innama
Sun bi dokarsu ba zamiya.

8. Ka’ida ce suke bi duka:
 Kora doka bisa kayuka
Martaba, dukiya, rayuka
In ka take su ka sha daka
  Rayuwa yari ba lafiya.

9. Kowane gunsu daidai shi ke
 Mai talauci biyayya ya ke
Maikuɗi, tajiri bai sake
In ya laifi hukunci ake
Martaba ba ta sa yafiya.

10. In kasa ka ga ta sunkuya
Ka ga manya suna yin tsiya
 Ba tsaron rai bare dukiya
Cin mutuncin mutum ba wuya
  Kar ka sa ran zaman lafiya.

11. Gu da dama a Ifrikiya
Sa kudanci na Sudaniya
 Har kasar tamu Nijeriya
 Libya sa Santa Ifrikiya
Babu doka bare gaskiya.

12. Larabawa mutan Eshiya
 Ga Yaman nan zuwa Syria
 Afghanistan haɗo Chechniya
Ran mutum sai ka ce kurciya
Hargitsi ba zaman lafiya.

13. Mun daɗewa da shubka kasa
Mun zata cigaban duk kasa
 An gina mu ko mun farfasa
 Mun ɓarar ba rabo mun rasa
  Sai nadamar marar gaskiya.

14. Farfaganda ta kanci: Ruwa!
Munka sha har muna yin rawa
Mun yi tatil muna yin juwa
Nan da nan munka wo mantuwa
Mun yi waka ta sharholiya:

15. “Yau talauci fa zai ɗaukaka
 “Dukiyarmu rabon muduka
 “Maida sarki abin caccaka
“Malami, tajiri su duka
  “Martaba sai a jamhuriya.

16. Keta doka ya zam ka’ida
 Gun mutane da yanci guda
 Kangarewa adon maigida
Kan jimawa gari sai kiɗa
Rusa mulki muna fariya.

17. Kan talakka kamar tsautsayi
 Ya yi mulkinsa mai laulayi
Tangaɗi, magiya, ga layi
Babu kishi abin tausayi
Cin amana da son danniya.

18. Babu doka ta kaya da rai
 Martaba babu sai dai garai
Maguɗi ba shi zaɓen kwarai
 Jahili ga shi nan sakarai
  Ba shi kaunar maso gaskiya.

19. Da yana son zaman lafiya
Sai ya zamto rikon gaskiya
 Sanya doka da yin tarbiya
Masu laifi su zam sun biya
Ka ji tushen zaman lafiya.

20. Sai mu bunkasa duk ayyuka
Baiwa yara abin ɗaukaka
Babu gilla da kwaya duka
Sai biyayya, rashin laifuka
  Duk ƙasa kwance sai lafiya.

21. Mu talakka batun gaskiya
Inda son rai cikin zuciya
Hargitsi za shi zo ba wuya
Bin mu doka zaman lafiya
Ka ji kalma batun gaskiya.

22. Mas’ala ko idan ta zaka
Kar mu saurin zama harzuka
 Mui ta haushi kamar karnuka
Keta doka muna hallaka
Rayuka, dukiya kun jiya?

23. Yanda doka ta ce kan’uwa
 Za mu tai inda mai unguwa
Hakimi ba bari har zuwa
Can ga sarkin kasa mui kuwa
Don muna son zaman lafiya.

24. In ko laifi akai wa kasa
Dukiya ko ko rai an rasa
Kotu ce za ta yanke masa
Rayuwa ka’ida ce musa
Hankali za mu zam lafiya.

25. Mui ta watsi da duk rarraba
Mui haɗewa da juna gaba
Mu jama’a zuwa shugaba
Rayuwa babu ko fargaba
Za ta dawo kamar can jiya.

26. In ko cewa muke mun kiya
Kowane zai bi son zuciya
Yi da gangan muna fariya
Babu doka a Nijeriya
Ture zancen zaman lafiya.

27. Masu laifi iri ɗai suke
Masu biro kisa ma suke
Shi da harbi ka bar bincike
Zuciya mai biɗar mallake
Duniya ba zaman lafiya.

28. Dukiya, martaba, rayuka
 Kar mu ɓata ukun su duka
Gun kalami mu bar zantuka
Duk amana mu zan mun rika
Mui ta himmar zaman lafiya

29. Nai kira yau ga Sarki ɗaya
Kai salama ga duk duniya
 Agazawa ga Nijeriya
 Don mu zamna cikin lafiya
Dukkanin mu ga baki ɗaya.

30. Zan takaita a gun nan haka
Ga talatin da ɗai baituka
Fa’ilun, Fa’ilun bincika
Gargaɗi gun mazo laifuka
Masu rushe zaman lafiya.

31. Nai kira Rabbi kai sallama
Kansa manzo daɗo sallama
Kan iyaye ka zan ka gama
Har da mu duk cikin sallama
Duniya, Lahira duk ɗaya.

Tammat walhamdulillah.

24 ga Fabrairu 2015

Monday, December 14, 2015

Ban Hakuri, Nadama da Shawara Ga Professor Bogoro

Ban Hakuri, Nadama da Shawara Ga Yayana Prof. Bogoro. Dara Ta Ci Gida.

Na dawo daga Kano sai na iske takarda da ke nuna yayana kuma Shugaban Asusun Raya Manyan Makarantu (TETFUND) ya damu kwarai kan rubutun da na yi a kansa satin da ya wuce lokacin bayyanarsa gaban Majalisar tarayya don bayanin wasu kudade masu yawa da ake zargin an salwantar a karkashin hukumar ta TETFUND. Ya yi kukan na zubar masa da mutunci a idon duniya.

In za a tuna da farko na ce EFCC ne suka cafke shi amma nan da nan na janye rubutun da na kara bincike sai na gane ba haka ba ne, maganar ba ta kai can ba. Amma a yanzu gayyata kawai majalisa ta masa kuma maganar ta shafi tsawon 2011 ne zuwa 2015, ba zamaninsa kadai ba a wurin. In za a tuna da na samu tabbacin EFCC ba su kama shi ba, nan da nan na shafe wannan post din a Facebook na maye shi da bayanin cewa EFCC ba su kama shi ba, ya bayyana ne kawai gaban Majalisar Kasa kamar yadda sabon post din ya nuna a kasa.

Allah ya san ban yi da niyyar cin mutuncinsa ba. Hasali ma, in an tuna, a post din farko na nuna damuwata ne kan yadda ake takurawa manyan jami'an gwamnati sai sun ba da kudi don harkar zabe a zamanin da ya shude. Kuma a ciki na ba da kyakkaywar shaida ga shi yayan nawa kan halinsa na kwarai da taimakawa al'umma. Wannan shi ne ake cewa "fair comment" da Turanci wanda kowane dan kasa na da dama ya yi. Maganar kudi kuwa, wata majiya a TETFUND din cewa ta yi akwai wasu biliyoyi kudaden TETFUND da tsohon shugaba Jonathan ya yi kwana da su kafin su iso hanun hukumar. Hukumar ta rubuta masa a zamaninsa cewa tana bukatar wannan kudaden amma bai ba da izinin a biya ba sai kwana daya kafin ya bar mulki.

Ni, Aliyu, ban ji dadin yadda ta kasance haka ba. Ina fata zai gane cewa shi shugaba ne wanda irin wannan zai ci gaba da faruwa da shi. Rayuwar Shugabanci dabam ne da rayuwar Jami'a. Sai ya dau hakuri in ba haka ba, a inda aka dosa din nan, mutane za su haukata shi.

Dalilin fadin haka kuwa shi ne sabon Ministan Ilmi, Malam Adamu Adamu, ya nuna gwamnati ta yi haramar binciken wasu manya manyan kwangiloli a manyan makarantun kasar nan. Fatarmu kawai kar abin ya shafi TETFUND. Haka kuma, ba mu san abinda majalisa za ta gano ba a cikin bincikenta. Shin za ta gano akwai badakalar ne, daga nan ta mika wa EFCC maganar, ko kuwa za ta wanke TETFUND gaba daya. A tsakanin nan maganganu za su yi ta yawo.

Zan ba da misali da kai na. Lokacin da muke Transition Committee na Jahar Bauchi, an yi zargin cewa an ba ni N560 million wanda wai na tura account din Gwamna M.A. Abubakar. Na san wanda ya buga labarin, ina ma da wayarsa. Amma ko kadan ban yi zaton in damu ba tunda na san ba daidai ba ne. Sai kawai na yi rubutu a shafina na Facebook cewa maganar ba daidai ta ke ba kuma kudin da aka ba mu don gudanar da ayyukan kwamiti din bai kai kashi daya bisa goma na abinda ake zargi a kai ba. Na kuma yi alkawarin zan lissafa kowane kwabo da muka kashe in mika wa gwamnati lissafin a karshe don wanda ke sin gani ta je ta gani. Haka kuma aka yi. Ba na jin akwai wani mahaluki yau da ya yarda an ba ni N560 million.

Professor Jega har waka aka yi ana zagin uwarsa an yi amma shi m bai nuna irin wannan damuwa ba. A karshe, gaskiyarsa ta bayyana. In kana da gaskiya, zargi ba zai dame ka ba kuma a karshe Allah zai tabbatar da gaskiyarka. Don haka in shugaba bai sa hakuri ba ya biye wa yan koren da ke gabansa wadanda burinsu su tatse shi ne, to a gaskiya zai shiga fitina da yawa hannun yan jarida da jama'ar gari. Shawarata ke nan.

Karshe, kowa ajizi ne, tun ba marubuta ba. Sau da yawa na ga manyan marubuta, kamar su Muhammed Haruna, suna kuskure. Asalan abin yana biyo kuskure ne wajen.rahoton da.ya zo maka. Sai dai doka ta ba da dama na janyewa, watau retraction. Allah ka raba mu da girman kan jin mu mun fi karfin kuskure. La sa mu cikin masu karbar kurensu kuma su gyara! Allah huci zuciyar yayana, Professor Bogoro, ya sa ya gama da fitinar TETFUND lafiya, ya baiwa mahassada kunya. A nan dai Dr. Tilde ya kobsa, don kuwa dara ta ci gida.

Dr. Aliyu U. Tilde

Please share.