tag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post9165976044023151803..comments2023-08-04T08:58:48.750+01:00Comments on Discourse with Dr. Tilde: Sako 3. Maraba da Dokar Hana Sadaka a LegasDr. Aliyu U. Tildehttp://www.blogger.com/profile/09289324801389455491noreply@blogger.comBlogger23125tag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-66594145709678219812011-05-20T16:50:42.500+01:002011-05-20T16:50:42.500+01:00Wannan doka da Fashola yayi kalubale ne kan gwamno...Wannan doka da Fashola yayi kalubale ne kan gwamnonin jihohin arewa ,da suke haduwa yau sama da shekaru talatin akan neman hanyar hana barace barace, amma hakan bai yiwu ba har yau. Yanzu ko dai shugabanin mu na arewa su tashi tsaye wajen shirin killata bakin da za mu samu nan da 'yan kwanaki domin kuwa Legas tayi musu zafi tunda babu na bati,ko kuma mu shirya kara tabarbarewar al amurran mu.Yakamata Gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu mu fara tunanin karfafa tarawa da raba dukiyar zakkat ta hanyar da a zamanance ake kira "STRATEGIC PHILANTHROPHY"Rabia Husaini Adamu -Eshaknoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-35820295301174386642011-05-20T12:32:05.344+01:002011-05-20T12:32:05.344+01:00Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da m...Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da musulmi. Allah Ya ba gwamnonin arewacin kasarnan karfin hali da kwarin gwiwar kafa dokar hana bara a wannan shashe, amin.

A.Y. Safana.A. Y. Safananoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-39139272526486756542011-05-20T12:29:35.156+01:002011-05-20T12:29:35.156+01:00Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da m...Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da musulmi. Allah Ya ba gwamnonin arewacin kasarnan karfin hali da kwarin gwiwar kafa dokar hana bara a wannan shashe, amin.

A.Y. Safana.A. Y. Safananoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-2030457042237263352011-05-20T12:27:15.392+01:002011-05-20T12:27:15.392+01:00Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da m...Ba shakka, bara na zubadda mutuncin musulunci da musulmi. Allah Ya ba gwamnonin arewacin kasarnan karfin hali da kwarin gwiwar kafa dokar hana bara a wannan shashe, amin.

A.Y. Safana.A. Y. Safananoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-84372546412713455782011-05-18T21:49:11.033+01:002011-05-18T21:49:11.033+01:00Wannan doka a kan hanya take, sai dai kamar kowace...Wannan doka a kan hanya take, sai dai kamar kowace doka a Najeriya, ba za ta taba yin tasiri ba, muddin dai ba tashi tsaye aka yi ba, aka nuna cewa da gaske ake yi.
Maganar bara kuwa, yau sama da shekara 50 ke nan da marigayi Malam Sa'adu Zungur ya gargadi al'ummarmu, da cewa mu kiyayi wannan mummunar ta'ada. Ya yi wannan gargadi ne a wakensa da ya sanya wa suna "Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya?" Ga shi mun yi biris da ita, muna ganin illar haka.
A shekarun baya, marigayi Janar Hassan Usman, shi da su Kanar Usman Jibrin sun taba turza hana bara, amma wasu rubabbun malaman Musulunci suka yi musu caa, suna dakile musu himma. Ni kuwa na ce idan mun ki ji, ba ma ki gani ba.
Allah Ya ganar da mu gaskiya kuma Ya ba mu ikon bin ta, amin.

Bashir Yahuza Malumfashi
byahuza03@yahoo.com
08065576011Bashir Yahuza Malumfashinoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-38946038527313069722011-05-18T15:23:38.324+01:002011-05-18T15:23:38.324+01:00Malam daidai ne wannan Dokar Allah ya kawo ta KANO...Malam daidai ne wannan Dokar Allah ya kawo ta KANO abin yayi yawa.

Kabiru Yakasai

Daily trust, kanoKabiruhttps://www.blogger.com/profile/04428683446255928672noreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-36025964596645421312011-05-17T12:19:14.662+01:002011-05-17T12:19:14.662+01:00Allah na kwana biyu bana bada sadaka a kan titi, a...Allah na kwana biyu bana bada sadaka a kan titi, akwai bukata a cikin 'yanuwa na da makota. Wannan doka na maraba da ita ya kamata Gwamnonin arewa su dauki irin wannan matakin. Amma maganar almajiranci da bara na yarda akwai banbanci, sai a zamaini yanzu almajiranci a manyan biraanan mu ya zama matsala, iyaye daga 'kauyuka na turo yara birane saboda su guji hakkin dake kansu na kula da su. Maganar tsangaya kamar yadda Gwamnati Mallam Shekarau suka fahinta a Kano na bukatar a duba, saboda tana tare da matsala. Tsangaya an san tun da a Kauye da daij take ba cikin birane ba. Allah ya sa mugane.Nuhu Abba Ibrahimnoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-14367888862864845902011-05-16T14:25:23.444+01:002011-05-16T14:25:23.444+01:00Allah SWT Ya numa nama ranar da za'a ce bahaus...Allah SWT Ya numa nama ranar da za'a ce bahaushe ya yi watsi da bara ta ko wace irin hanya. Watau Allah SWT Ya kau da akidar maula, tumasanci, raraka, banbadanci (roko),'Allah Ya baku mu samu','In an bamu a tsunkule hannu', 'samun ku shine namu' a cikin zukatan hausawa. Amin summa amin. Haza wassalam.Al-fazazinoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-44049185721735531792011-05-16T12:08:39.184+01:002011-05-16T12:08:39.184+01:00Yau da safe na yi fakin domin bawa masu bara kudi....Yau da safe na yi fakin domin bawa masu bara kudi. Sai da diya ta ta fita da gudu domin mun wuce su kadan, kuma sai da muka hada canjin mu da nawa da nata, har ma a ka yi ta mana horn domin mun tare hanya (a abuja). Amma ina kyautata zaton ba taimako bane, sam. Saboda haka na yarda da nazarin da Dr. ya yi. Sadaka fisabilillahi ba lallai sai a titi ba, Allah ya ba mu ikon gane wa, amin.halimahttps://www.blogger.com/profile/01752030752656961234noreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-91189590274821273792011-05-16T10:48:54.672+01:002011-05-16T10:48:54.672+01:00I am happy with what you say Dr Aliyu, and it will...I am happy with what you say Dr Aliyu, and it will be good for Nigeria if more people come out and speak and write the truth as they see it.Hajiya Laminoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-12994792380256714602011-05-16T10:48:54.251+01:002011-05-16T10:48:54.251+01:00I am happy with what you say Dr Aliyu, and it will...I am happy with what you say Dr Aliyu, and it will be good for Nigeria if more people come out and speak and write the truth as they see it.Hajiya Laminoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-20766940511245124172011-05-15T23:18:09.365+01:002011-05-15T23:18:09.365+01:00Yayi amma dai dokar tayi tsauri matuka. Kamat yayi...Yayi amma dai dokar tayi tsauri matuka. Kamat yayi a tunani kwarai.Ahmad Arab Abubakar Azarenoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-15186296307930594112011-05-15T17:41:18.558+01:002011-05-15T17:41:18.558+01:00Allah sarki na Tanko....( Bahaushe),yau takai a ka...Allah sarki na Tanko....( Bahaushe),yau takai a kaddamar da doka kanka a garin legas.To sai mun gani! yaya zakayi? zaka ci gaba da zamanne ana tsanarka,ko zakaci gaba da wulakantar da kanka kana gararanba a tsakanin masallaci da coci domin sadaka?...Allah ya karawa Danmasani( Dr tilde) basira, ya kuma karemu da wulakantar da kanmu amatsayin mabarata a kasannan.
wassalam,

Jamilu y. jegajamilu y jeganoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-31943160490383711192011-05-15T14:16:35.732+01:002011-05-15T14:16:35.732+01:00@aliyu, on yours "....Fasinjan da aka yi obal...@aliyu, on yours "....Fasinjan da aka yi obalod din da shi shi ne suke fitarwa suyi ta jibja sannan su hukunta shi", this is quite barbaric for anyone and for whatever cause to do. while overload is bad, jibgar anyone for it is utterly inhuman.Anonymousnoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-89147308698161600142011-05-15T02:49:53.198+01:002011-05-15T02:49:53.198+01:00Ni ma na ce Allah Ya sa Malam bahaushe ya farka da...Ni ma na ce Allah Ya sa Malam bahaushe ya farka daga barci, ya fahimci illar mayar da bara sana'a, domin ba a Lagos kawai ba, har Sa'udiyya da Sudan idan ka je za ka ga Bahaushe, abin kunya, yana yawon bara a kan titi, kamar tun da Allah Ya halicci duniya shi kadai ne maraya. Allah kuma Ya sa gwamnatocinmu a jihohin arewa su ma su farka su haramta yin bara a kan titi. Mai bukata ya je masallaci ko coci ko kuma a kafa gidajen marasa galihu su je su taru a can. Amma irin kaskantar da jinsin Bahaushe da bara ta ke yi, abin da ban haushi. Kai, Dr. Tilde ka burge ni da wannan bayani naka.Danbauchihttps://www.blogger.com/profile/18270201937209987274noreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-54863655237284998642011-05-15T00:52:05.493+01:002011-05-15T00:52:05.493+01:00Dokta aima da hadisan manzon tsira (S. A. W.) da s...Dokta aima da hadisan manzon tsira (S. A. W.) da suka hana lalaci, mutuwar zuciya, roko da sauran su. A yau kuwa barar ta za ma roko, mutuwar zuci da lalaci.Salihhttps://www.blogger.com/profile/12179139906167322910noreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-84271866635406258152011-05-14T23:25:59.208+01:002011-05-14T23:25:59.208+01:00Malam Tilde, Allah Ya saka da alheri. Ina ma shuga...Malam Tilde, Allah Ya saka da alheri. Ina ma shugabannin mu za su iya abin da Fashola yayi? A Kano, misali, akwai dokokin da suka hana bara da talla a titi. Amma, kash! Shugabannin baza su iya tabbatar da ganin an hukunta duk wanda ya saba wa dokokin ba. Allah Ya kawo mu zamanin da shugabanni suke tsoron gaya wa jama'ar su gaskiya. Kusan duk shugaban da ka zauna da shi, ka tattauna matsalolin bara, za ka same shi yana kin ta; amma bai isa ya fito fili ya kyamace ta ba. Na tuna wata hira da aka yi da marigayi Janar Hassan Usman Katsina a kafafen yada labaru; ya nuna bakin cikin sa akan yadda muke zubar da mutuncin mu sabo da bara. "Bahaushe" ne kawai ya ke yin ta, sai ka ce shi kadai ne ya ke talauchi a duniya. Watakila da shugabannin mu za su kamanta kyamar bara kamar yadda Janar Hassan ya yi, da watakila annobar ta ragu. An ce wani malami ma ya ce masu bara ne direbobin da zasu kai mu al-janna.

Allah Ya sawake.Maliki K. Umarnoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-59388318326690492162011-05-14T22:22:17.275+01:002011-05-14T22:22:17.275+01:00Haka ne,Aliyu Sarkin yakin Sarkin Musulmi.Amma ba ...Haka ne,Aliyu Sarkin yakin Sarkin Musulmi.Amma ba na soja ba.Mainasaranoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-17425362399836867442011-05-14T22:04:05.238+01:002011-05-14T22:04:05.238+01:00Babu shakka Dr. Sheikh Aliyu Tilde ya sosa min ind...Babu shakka Dr. Sheikh Aliyu Tilde ya sosa min inda ke yimin kaikai! Duk in da mutum yaje, Hausa/Fulani ne mabarata. Saboba haka, Gwamna Fashola yayi abinda yaddace. Kasashe da dama na musulmin duniya sun yi Allah waddai da bara tuni, domin yin hakan, babu shakka yana zubadda mutuncin Musulmi da Musulunci, kanar yadda yake faruwa garemu musulmin Nigeria. Da fatan gwamnonimmu zasu doki irin wannan mataki da Fashola ya dauka, amma su kara da baiwa talakawansu, musamman mabukatan gaske, da hakko- kin su. Allah (SWT) Shi tabbatadda khairinSa, ameen. M. D. Magaji.M. D. Magajinoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-89042676051035077392011-05-14T15:23:46.349+01:002011-05-14T15:23:46.349+01:00Well I don't speak Hausa, but Fulfulde, and I ...Well I don't speak Hausa, but Fulfulde, and I am happy to see intellectuals like Dr Tilde is writing in an African language, this will definitely give our languages more prestige.

For those who may like to read article in Fulfulde, please go to: www.peeral.com

Keep up the good job, Dr Tilde.

Mi yettii ma masin.amadu sajohhttps://www.blogger.com/profile/04497694243974095240noreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-20667244074432795542011-05-14T14:23:15.082+01:002011-05-14T14:23:15.082+01:00Wannan abin yabo ne gwamnan Legas yayi. Da gwamnon...Wannan abin yabo ne gwamnan Legas yayi. Da gwamnonin arewa zababbu ne da sunyi koyi da Fashola a samu ci gaba.

Tilde kayi kokari wajen rarrabe bara da almajirci, Allah yasa hakan tasa a samu waraka.

Tilde wasu abubuwan bahaushe da aka maida addini kuma suke hana mu ci gaba sune MISALI MUTUM YAYI HADARI DA MOTA (KO DA BISA GANGANCI NE) AMMA SAI KAJI ANYI WUF ANCE "HAKA ALLAH YASO" KO KUMA "AI KADDARA CE". Saboda haka ba'a bincike bare a samu gyara.
Menene bambancin GANGANCI da KADDARA?Abdulrahman Abdulsamad Kankianoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-60659056632796973242011-05-14T14:03:01.147+01:002011-05-14T14:03:01.147+01:00Assalamu alaikum Malam Aliyu,
Ni dai na goyi baya...Assalamu alaikum Malam Aliyu,

Ni dai na goyi bayan wannan raayi naka dari bisa dari, musamman matsayin da ka dauka duk lokacin da ka shiga Legas. Nima ka koyar dani.

Allah sa jamaar kasar hausa ta farka ko zata dawo da mutucinta, amin.

Abdulkadir JibrilAnonymousnoreply@blogger.comtag:blogger.com,1999:blog-3522281603276666782.post-51420275509272368612011-05-14T13:17:49.482+01:002011-05-14T13:17:49.482+01:00Assalamu Alaikum,
Ina rokon Allah suhnahu wata...Assalamu Alaikum,

Ina rokon Allah suhnahu wata'ala ya sa mu fahimci sakon Dr. Tilde, gwamnatocin mu kuma su farka.

Abunda yake mafi muhimmanci a cikin wannan rubutu na Tilde shine bambanta Almajiranci da Bara.

Jazakumullah.Muktar Baturenoreply@blogger.com