Friday, April 29, 2011

Sako 2. Murnar Cin Zaben Kwankwaso

Aliyu U. Tilde 9:11am Apr 29
Labaru sun zo mana kan irin murnar da wasu mutane ke yi a Kano ta cin zaben Kwankwaso ta hanyoyin da ya ke nuna suna maraba da shi don zai kau da Shari'a. Wannan zai sa in kura ta lafa mu yi dogon tattaunawa kan tarbiyyar al'umma a tsarin demokradiya na wannan zamanin.

Su wadanan da ke murna ta hanyar yin wadannan abubuwa, kar mu dauka da addini su ke ja. Hasali ma, sau da yawa in aka wa addininsu kalubale, ko da a gidan giya ne, to wallahi kaca-kaca ake da su. Sai su tashi su pasa kwalba, su yi ashar, su ce za su kara da duk wanda ya baci addininsu.

Wancan satin a kauyenmu, Tilde, akwai 'yan wiwi da ke busa sigarinsu a bayan gidana, da unguwata da nake shugabanta, da kuma makarantar firamare da ke kusa da ni. Mutane sun aza sun addabemu. Nakan ce mu rika hakuri da su. Suma akwai ranarsu. Don ina da sanin amfaninsu a fadan zangon kataf da sharia a Kaduna. Ile kuwa. Wancan satin, da aka ce ga kabilu can sun kawowa Tilde hari daga duwatsu, su wadannan yan wiwin su ne kan gaba wajen kare garin. Kowa sai sa musu albarka ya ke. Akwai yara da suka rika yawo suna barna suna kona gidajen kirista bayan an ce Buhari ya fadi zabe. Ko mutanen gari sun musu magana, ba sa saurarensu. Amma da zarar sun hango 'yan wiwin nan, sai su ruga, su bar wurin. To, shege ma da ranarsa!

Watau, dan Adam yana da wuyar sha'ani. In ya yi wani abu yakamata mu nazarce shi, mu gano dalilansa. Akasari sai ka ga ba abun da muke tsammani ba ne. Zai yiyu, mun tsananta wajen gudanar da sharia ta yadda ta saba da asalinta ko da zamaninmu. Zan ba da misalin shan giya.

In ka duba batun shan giya, ni a raayina an zafafa. Ko a Madinar Manzon Allah ana sai da barasa a wasu unguwanni har zamanin khalifofinsa. Haka kuma a manyan biranen musulunci irin su Damascus, da Bagadaza, da Kufa, da Seville, da Cordoba, da Alkahira. Ban taba jin inda aka yi dokar hana sai da ita ba tamaman tunda a ko yaushe, saboda sassaucin muslumci, akwai wadanda ba musulmi ba tattare da musulmi. Kai! Har a kasar Hausa, su Shehu Usumanu basu damu da su yi doka da zata hana samar da giya ba kwata-kwata. Shi ya sa kusan ake da bauda a daukacin kasar Hausa, birni da kauye. Amma tanadin sharia shi ne duk musulmin da aka kama ya sha, to a masa bulala 80. Shike nan. Akwai wanda Umar ya sa aka wa bulala don an same shi a bauda, duk da cewa an tabbatar ba giyar ya ke sha Ba. Umar ya ce to me ya kaishi zama a inda ake shanta? Wannan, a maimakon Umar ya yii dokar hana sai da giya ba.

Kuma burin sharia ba wai ta maida mutane mala'iku ba ne da za su zam ba sa laifi kwata-kwata. Sam. Allah ya fi son ya gansu a 'yan Adam dinsu, masu laifi lokaci-lokaci, amma kuma masu reman gafararsa a kullum. Ina jin akwai ingantaccen hadisi qudusi a kan wannan. Malamai suna iya binciko mana. In burinsa marasa laifi ne, ai yana da mala'iku da ba sa sabama umarninsa, suna masa tasbihi ba dare ba rana.

Don haka, yana da wuya a kauda dan Adam daga wannan dabi'ar da aka halicceshi a kanta, dabi'ar laifi da zunubi. Dama shi mai sabone asalan. Aikin addini shi ne ya kira shi ga alheri, in ya amsa sai ya ribanta da kyautata sabon nan da aikin alheri da hali nagari, kamar yadda za a hana shi mummunan aiki ta hanyar da ta dace da lokacinsa da abunda nassi ya kawo na wa'azi da ladabtarwa yadda ya fi dacewa.

Hakanan kan abubuwa da yawa wanda harkar film na cikinsu. Fasaha bata wanzuwa sai cikin 'yanci da walwala. Ai ido ba mudu ba ne amma ya san kima. Da yakamata a duba yanayin kasarmu, da matsayin tarbiyyarmu, a fara da sassauci hatta kan abubuwan da musulunci ya tsananta, kuma a yi sassauci har abada kan abunda bai tsananta ba...a bimu sannu sannu har mu fahimta, mu daidaita sahu.

Don haka, a takaice, wadannan 'yan'uwa namu ban yi tsammani wai yaki da addini suke yi ba. Hanyar da muka bi wajen d'abbaka shariar ce kila bai dace da zamaninsu ba ko d'abi'arsu. Kila mun gaggauta wasu abubuwan, mun tsananta a wasu. Don haka suka nuna bijirewarsu ga tsarin amma ba ga addinin ba.

In an tuna ai a zamanin Kwankwaso aka fara shariar, irinta wannan zamanin. Ina tuna lokacin da mataimakinsa, Ganduje, da Malamina, Aminuddeen Abubakar, suke yawo otel otel suna farautar kilakai a cikinsu. Don haka ba bakinta ba ne. Kwankwaso na da nasa malaman. Ba ni da haufin za su bari ya goyawa abunda zai maida musulunci baya.

Kamar yadda na fada jiya, sabon gwamnan sai ya gina kan abunda Malam Shekarau ya yi;ya yi gyara inda ake bukatar gyara; ya cigaba da duk abu mai kyau; ya kuma jingine, bisa shawara, abunda yake ganin kuskure ne. Amma kashedi kashedinsa, kar ya bibiye ma ashararai da za su kai shi su baro. Shekara hudu kamar gobe ne.

Haza wasalam.

Aliyu

11 comments:

  1. Salam Mal. Aliyu,
    Abin tunani da nazari, ko da mutum bai yarda da ra'ayin ka ba dari-bisa-sari.
    Na kuma yaba ma rubun zuben ka cikin Hausa. Da ina ganin 'yan boko ba za su iya yin rubutu da Hausa mai kyau kamar na ka din nan ba (mai kura-kurai kadan).
    Allah ya kara basira, amin.
    Baban Yara.

    ReplyDelete
  2. ASSALAMU MALLAM ALIYYU.
    NA JI DA'DI DA KA FARA YIN RUBUCE RUBUCENKA DA HARSHEN DA AL'UMMARMU KE FAHIMTA, WANNAN HANYAR ZATA SAU'KA'KA MAKU ISAR DA SA'KONKU NA GYARA ZUWA GA ADADI MAFI YAWA NA AL'UMMARMU, SA'BANIN AMFANI KOYAUSHE DA HARSHEN TURANCI, WANDA BAI FI 15% 'DIN AL'UMMA BA NE SUKE AMFANUWA DA SHI.
    HA'KI'KA SHARI'AR MUSULUNCIN DA AKA KAFA A MAFI YAWAN JAHOHIN AREWACIN NIJERIYA, KO DA AN YI SU NE DA MANUFOFI NA SIYASA, SUN KAWO GYARE GYARE DA DAMA, SUN RAGE WANI KASO MAI YAWA CIKIN ABUBUWAN 'BARNA DA AKE AIKATAWA A WA'DANNAN JAHOHI, ALAL MISALI, A KANO SHARI'A TA RAGE DABA, WURAREN DA SUKA SHAHARA DA KARUWANCI SUN ZAMA TARIHI, AIYUKAN BORI DA MAKAMANTANSU SUN RAGU A WURARE DA DAMA, HAKA ABIN YAKE A SAURAN JAHOHIN IRIN SU ZAMFARA, YOBE,SOKOTO, DA SAURANSU, SAI DAI KAMAR YADDA MUKA SANI, BA WANI AIKIN 'DAN ADAM DA BA YA RABUWA DA KURA-KURAI, DUK DA CEWA ALHERIN DA TA HAIFAR YA FI KURA-KURAN NESA BA KUSA BA.
    RUBUTUN NAN NAKA YA 'KUNSHI ABUBUWAN DA YA KAMATA A LURA DA SU MUSAMMAN DON RAGE KURAKURAN DA AKA AIKATA YAYIN TABBATAR DA SHARI'AR, SAI DAI HANKALINA YA TASHI SOSAI GANIN YADDA MUTANE SUKE MURNAR TAFIYAR SHARI'AR MUSULUNCI DUK DA KULLUM KIRA SUKE YI DA KOWANE GWAMNA YA YI MUSU ITA.
    NA YARDA DA UZURIN DA KA YI MUSU NA CEWA BA ADDININ SUKE MA TAWAYE BA, YANAYIN 'DABBA'KAWAR NE BA SU SO, SAI DAI ABIN DA SUKA YIN NAN ALAMA CE TA BABBAN AIKIN DAKE GABAN MASU SON GYARA, TA HANYAR ADDINI NE SUKE SON KAWO GYARAN KO TA WATA HANYA DABAN, DON JAMA'ARMU BA SU SHIRYA KAR'BAN GYARA BA,WANDA A MAFI YAWAN LOKUTA YANA BU'KATAR 'KARFI MUSAMMAM A IRIN WANNAN AL'UMMA TA MU.
    BA ZAN MANTA DA IRIN RASHIN JIN DA'DIN DA MAFI YAWAN AL'UMMA SUKA NUNA BA YAYIN DA AKA FARA TANTANCE FINAFINAI A JAHAR KANO DON A KARE MUSU TARBIYYARSU, AL'ADUNSU DA ADDININSU, FINAFINAN DA MAFI YAWAN MASU SHIRYA SU 'YAN TASHA NE, DROP OUTS NE NA MAKARANTU, WANDA SU KANSU BA SU DA TARBIYYA BALLANTANA SU BA MA WASU.
    LALLE SHUWAGABANNINMU NA DA JAN AIKI A GABANSU MATU'KAR GYARAN SUKE SON KAWOWA.
    ALLAH YA TAIMAKEMU GABA 'DAYA, YA KUMA 'KARA MA MASU SON KAWO GYARA 'KARFIN GWIWWA.

    ReplyDelete
  3. Salam Sheik,
    Lallai ba a rasa kura kurai da shuwagabanni ke yi ba yayin da suke mulki ta yadda za a samu wasu sun kuntata. Amma galiban in har shugaba yana nufin yin adalci akan fahimci hakan kuma mafi yawa ba za su yi korafi ba. Matsalar ita ce, kamar a kano wasu alamu sun nuna cewa kamar shi kwankwaso ya na nufin ramuwar gayya ne don irin maganganu da ya fada a kafafen watsa labaru kafin zaben. Lallai ne a samu masu ja masa linzami da tabbatar da shi bisa turbar adalci da kyautatawa dukan mutane a jiharsa. Wanda hakan shi zai nuna cewa shari'a ko zata karfafa ko raunana a jihar. Fatan mu dai Allah ya yi musu jagora tare da hadasu da mutanen kwarai masu basu shawarwari da suka dace.

    Basheer

    ReplyDelete
  4. Allah saka da alkhairi da wannan rubutu mai amfani

    ReplyDelete
  5. Allah saka da alkhairi da wannan rubutu mai amfani

    ReplyDelete
  6. Salam Mal Aliyu,
    A ra'ayi na a bar yabon dan kuturu! Hakika zaben bai nuna son sharia ko kinta ba a jihar Kano. Kuma idan ka duba,alkalumman zaben zaka ga mafi yawan mutanen Kano basu zabi Kwankwaso ba. Ya samu kashi 46% cikin dari, Mal Takai kuma nada kasi 45%. Don haka sabanin hankali ni a nuna cewa mutanen Kano na bukatar a dawo da shan giya a sarari, ko gidan karuwai da yan daba shi yasa suka dawo da Kwankwaso. Wannan a ra'ayina ba yabo bane ga Kwankwaso, wand ko ba dade ko ba jima zai koma wajen mahaliccinsa kamar ko wane mahaluki.
    Muhammad N

    ReplyDelete
  7. na yi matukar farin ciki da wannan rubutun. maganar shari'a ba ta tsaya a kan giya da kilakanci bane kawai. Shawarar da zan bawa mai girma sabon Gwamna ita ce ya duba kansa ya yi jagora irin ta turbar musulunci saboda shi musulmi ne. Yayi adalci. Na san zai fuskanci kalubale wajen tafiyar da Malamai a Kano don ko sun dandana a mulkin Shekarau, ban san ba ko suma zasu yi "azumi", su fuskanci fadakarwa, su nesance harkar mulki. Allah yas mu dace, ameen.

    ReplyDelete
  8. Assalamu alaikum. Ni a tawa fahimtar hanyar da kwankwaso yabi wajen aiwatar da sharia ita ce mai tsanani ba ta shekarau ba, tunda ko bulalar shan giya yanzu ba'ayi, amma kamar yadda ka fada lokacin kwankwaso mataimkinsa (ganduje) shine yake zuwa kamen giya da karuwai, shi kuwa shekarau cewa yayi ma gyaran zukatan jama'a zai fara yi ta hanyar shirin sa na adaidaita sahu, kuma shi kansa kwankaso acikin kamfendinsa yana cewa a dena amfani da sharia ana yaudarar mutane. Ba don uziri na jahilci ba, maganganun da mutane su ke fadi akan sharia saboda murnar kwankwaso yaci zabe wallahi sun fitar dasu daga musulinci. Fitina ce babba zakaga mata suna rawa a kan titi ko riga babu a jikinsu suna cewa sharia ta kare! To mu kiyayi fushin ubangiji, Allah ya shirye mu ya kare daga afkawa cikin fushinsa, ameen. Ma'assalam - Mahmud Wada

    ReplyDelete
  9. Gaisheke da kyau Malam Tilde.
    Da dad'ewa kai da malam Adamu Adamu ina alfahari daku wajen kare mutuncinmu da addininmu a wannan kasa. ALLAH ya saka da alheri. Hakika maganar shari'a da aiwatar da ita a wannan yanayi na dimokrad'iyya abune da idan za'a fadi gaskiya duk d'acinta, shine mun bar gini tun ranar zane. Musulunci ba ra'ayin wani bane, sako ne na ALLAH kuma ya aiko manzo bayan manzo har kusan 313, domin su tabbatar kuma su aiwatar da shari'arsa. Tunda ALLAH ne ya halicce mu shike da hakkin zaba mana yadda zamu rayu (shari'a). Idan manzo ya aiwatar da shari'a a madina ne kafin makka, to lallai sai mun tsarkake Gari kafin mu aiwatar da shari'a. Don ita shari'a mai gadi ne don kada tsarkakakken gari ya lalace. Da farko ba yadda shari'a zat yiwu karkashin Tsarin mulkin Nijeriya saboda a mahangarsa shi gaba yake da shari'a. Na biyu dole ka gyara gari kafin aiwatar da shari'a. Sheikh Usmanu Dan Fodio da duk wani mujaddadi da ka sani a tarihin musulunci wannan hanyar yabi ta Jihadi wadda yanzu ita muke gudu saboda muna son mu rayu sumul kalau a duniya kuma mu shiga aljanna sumul kalau a lahira. Idan kwankwaso yace a daina amfani da shari'a wajen kamfen to adalci yayi wa shari'a domin duk wanda aka zaba zai rantse ne don kare constitution ba shari'a ba. Kuma ni na bawa malamai laifin koma me ya faru ga musulmi a yanzu don sunfi kowa sanin cewa hanyar da aka d'auko ba itace da aiwatar da shari'a ba. ALLAH ya sa mu dace.

    ReplyDelete
  10. Salam,
    Ni a gani na Shekarau bai zafafa gudanar da shari'a ba don ya hana sai da giya. In haka ne sai mu bari a sai da kwaya da sauran miyagun shaye-shaye don kar a matsa ma mutane masu shan su ke nan. Ni na dauka nufin shari'a itace ta kare al'umma daga gurmacewa don haka shi yasa take hana sa'bo a bayyane. Ai ba'a kama mutanen da ke shan giya a cikin gidajen su ba. Masu saida giyan ma ai na dauka Gwamnati tayi ta tattaunawa da su ba wai ta farmusu ne ba kawai. kuma ai ba'a hana shan giyar ba a wurare kamar su sabon gari ba don komaiba don yanayir kasar tamu kamar yadda ka ce. Kuma na ga gwamnati ta yi ta nasiha dai dai gwargwado ga jama'a a redio.
    Abinda Kwankwaso zai yi sai dai ya dora kuma a ga aiki a bayyane ba a baki kawai ba. Allah Ya taimaka masa. Ameen

    ReplyDelete
  11. Bashir Yahuza MalumfashiMay 18, 2011 at 10:03 PM

    Allah Ya sanya sakon nan ya isa ga kunnuwan wadanda ya kamata su ji. Saura da me, ruwa a cokali, ya ishi mai hankali wanka!

    Daga Bashir Yahuza Malumfashi
    byahuza03@yahoo.com
    08065576011

    ReplyDelete