SHARHI 4
Na Dr. Aliyu U. Tilde
SHARRIN LASIFIKA GA ADDINI DA AREWA
Malam Idi Mijin Maikoko wani mai kiran sallah ne da aka tabayi a garin nan, Tilden Fulani. Duk wanda ya kai shekara 45 zai tuna lokacin da yake kiran sallah a masallacin kofar gidan Alhaji Sarki Mudallabi. Banda shi akwai ladanai biyu a garin lokacin nan: Malam Maikobi da ke kiran sallah a masallacin 'yan Tijjaniyya a gidan malam Baba dan Malam Hasan, uban su Malam Maikano Tilde; sai kuma Malam Dabura da ke kiran sallah a masallacin juma'a. Dukkansu ukun mutane ne masu murya. Kowa yai kiran sallah Tilde duk za ta ji. Har kiran sallar Juma'a wanda a lokacin shi kadai ne, da rana, in ba ranar kasuwa ba. Haka za ka ji shi radau a kunnenka balle kuma assalatu da ake kira da dare kafin a farka daga barci. Allah ya jikansu.
In dare ya yi kuwa, har alfijir ya keto, ba abun da za ka ji banda haushin karnuka ko kukan jakkai ko carar zakaru. Kome zai yi tsit. In za ka tashi yin sallar dare sai kayi ta yi, ba mai damunka da holo kowane iri ne, daga nan har assalatu.
Da rana kuwa, masu wa'azi kuwa suna amfani da muryarsu a masallaci. Ana haka har lasifikar hannu, Ta rataye, mai batir biyu ta zo. Ina tuna raka mahaifina masallacin Juma'a ina dauke da ita in ranar da zai yi wa'azi ne kafin zuwan liman. Wannan lasifika ta taimaka wajen sadar da sautin wa'azin ga masu zaune a harabar masallacin.
Ana haka sai lantarki ya iso Tilde a zamanin Shagari. Sai likkafa ta yi gaba, aka sayi lasifika mai aiki da lantarki, zaunanne dindindin a masallaci. Sannu a hankali, masallacin Juma'a ya rabu kashi biyu, 'Yan Izala suka bude nasu. Wa'azi fa na takaddama sai ya fara samun gin din zama a ko'ina, a kasuwa ne da masallaci. Da ma rediyo mai daukan magana ya shigo tun zamanin Gowon, ya bada damar daukar magana ana yadata a kaset. Masallacin Izala sai suka shiga sa wa'azin su a masallaci a ranar kasuwa da lokacin da ba sallah ba, musamman ranar juma'a tun karfe 12 na rana ko da dare in sun kira taron wa'azi na mako mako. Da abun ya zama salo, sai 'yan babban masallaci suma suka shiga sawa ranar juma'a.
Suma Izalar suka dare biyu. 'Yan sallama daya suka ware suka kafa nasu masallacin a kofar Alhaji Hamidu. Su ma suka shiga danna kaset a lasifika. Gari ya yi ta kara yawa, musamman da Aka fara rikicin Jos, aka yi ta gina masallatai kota'ina har ya kai yanzu dai masallatai a garin nan sun wuce 50! Kowanne kuma da lasifika. Da yawa daga cikinsu kuma suna wa'azi bayan sallar asuba kafin mutane su watse, wasu kuma sukan danna kaset din wa'azi tun kiran sallar farko har lokacin da za a tada ikama.
A da duk wadannan abubuwan ba su damar ba sossai don lasifikokin lokacin ba su da amo mai karfi. Amma fa a shekarun baya bayan nan, abun ya zama azimun. Ka duba girman Tilde, wanda ya ya kai kilomita biyu, masallatan nan in suka kunna wasu rantama rantaman lasifikokinsu, malam sai dole ka farka daga barci. In ko kiyamullaili kake ko wata addu'a, kana munajati da Allah, dole ka daina ko ka yi aikin banza. In sautin karatun kur'ani ko na wa'azi da ke caccakar kunnenka daga masallatan nan ya danno, sai ka nade buzunka ka koma gado ka yi lib a mayafi. Kai ba ga sallah ba, ba kai ba ga bacci ba. Dole ka saurari abun da ake cewa, dau'an au karhan.
A lokacin azumi kuwa abun ya fi kamari. Lokacin da sararin samaniya da kunnuwan mutane za su huta kadan ne, na yan sa'o'i kalilan tsakanin karfe 11 na dare da karfe 3 na safe. Amma in ba a wannan lokacin ba, to fa duk garin a hargitse yake da sauti kala kala, a wasu masallatan an danna karatun kur'ani, a wasu tafsiri, a wassu wa'azi. Toh, tunda masallatan da yawa, sai ka rude ma ka rasa wanne za ka ji, wanne za ka bari. Wannan holon in ya yi yawa, sau da yawa sai ya zame alheri saboda hankalinka ba zai iya kama abu daya ba, don haka sai ka yi ta sallarka, da addu'o'inka. In ka kare, sai ka ci sa'a ma har ka samu damar rintsawa kafin asuba. In gari ya waye za a sake kwatawa, don lokacin ne masallatai dabam dabam ke gudanar da tafsiri. Wani ya yi bayan asuba, wani da hantsi, wani da rana, wani da yamma, wani bayan magariba, wani bayan 'isha'i kafin kare 11. Haka dai. Mu da samun sakat sai an ce an ga wata.
Akwai matsaloli sosai wajen gurbata sararin samaniya da sauti mai karfi a lokuta dabam dabam. Akwai takurawa, da cutarwa, da cin hakkin mutane, da wulakanta Kurani, da fallasa sirrin al'umma da haddasa fitina. Wannan magana haka take koda kuwa wane irin sauti ne. Ka ga dai akwai maras lafiya da ke bukatar rintsawa. Akwai tsoffi da wadanda shekarunsu ya fara nisa da basa iya barci mai zurfi na lokaci mai tsawo, akasari sai gab da asuba barcin ya ke dawo musu bayan ya yanke na awoyi da yawa. Akwai wadanda sun kwana kiyamullaili suna bukatar gyangyadawa kafin asuba. Akwai masu karatun K'ur'ani da ke bukatar natsuwa kan abun da suke karantawa. Akwai yan lambu, da masu sana'ar itace, da lodin tipa, da magina da duk masu aikin karfi da ke bukatar barci mai tsawo da dare don su samu karfin samun kuta yaumin din gobe. Akwai..akwai… abun ba iyaka. Duk wadannan an shiga hakkinsu ta hanyar amfani da lasifika da karanta ya wuce masallacin da aka kunna ta.
Banda takurawa da shiga hakkin mutane, babban sharrin da lasifikokin masallatai da masu sa wa'azi a cikinsu ke yi shi ne haddasa fitina tsakanin musulmi su kansu, da kuma tsakanin musulmi da makobtansu kirista ko masu addinin gargajiya, musamman a manyan birane da gurare irin Tilde inda ake zaune a cakude da juna. Ka sa kaset din wa'azi a lasifika kana kiran wasu musulmi kafirai, ka ga kana kara ruruta wutar gaba da haddasa rarraba a tsakaninku.
Ka sa kaset din wa'azin da aka yi a Barno ko a Kano wanda a ciki ake zagin kirista ana ce musu arna da sauran bakaken maganganu wanda sam bai dace ba ajisu a bakin mai wa'azi Ba. Me kake tsammani zuciyarsu za ta dauki addininka? Wa'azin zai kara jawo su ne ko zai kara sa suki addininka? Kasa kaset na wa'azi a Tilde, Bauchi, Jos, Mangu, Kaduna, Riyom, Kuru, Pankshin, Zangon Kataf, Kafanchan, ko Zonkwa, wanda a ciki ake kira ga musulmi su yi shirin yaki da arna, kowa na ji, kai ko ka koma gida ka kwanta kuma a gidan nan naka ko wukar yanka akuya baka da ita. Shin kana jin wanda kake kira arna, wadanda ka zo ka zauna a kasarsu, sai su koma su kwanta su yi biris da maganarka? Duk ranar da wanda kake kira arne ya zarta maka wuka a wuya ko ya daba maka ita a ciki, ko ya auna maka alma a ka, ai ka san kai ka jawo.
Sannan kuma ka dau sirrin addininka da na mutanensa duk kana ta yadawa a banza duniya na ji. Addinin ka taimakawa ko dan siyasan da kake yiwa kamfen? A wannan garin wani yaro ya dau lasifika da asuba ya kafirta wanda duk ya zabi Jonathan, ya ce ranar zabe kowa ya fito da makami. Sarki ya ce a kawo masa shi. Da ya dukufa a gabansa, aka tuhumeshi sai ya ce shi abun da yake nufi makamin addu'a ne. Nan kuwa duk abokan zamanmu sun ji sun fahimta cewa shirin fada ake yi. Meye amfanin wannan? Don haka Ba mamaki da aka yi fad an addini a garin kwana uku bayan zaben shugaban kasa.
Don yawan sa karatun Kur'ani barkatai har kunne ya saba da shi bai dauke shi a kan komai ba. Haka wa'azin. A da, kadan za ka ji sai hankalinka ya kama ya kara maka tsoron Allah, yanzu kuwa sai ka ji mai yawa qmma ko a jikinka tunda abun ya zama gashi ko'ina kamar jampa a Jos. Wannan shi ya sa sahabbai suka ce Ma'aiki (SAW) ya kasance yana kaffa-kaffan yi musu maganar addini don kar ya gunduresu. Amma mu da muka fi Annabi iyawa, maganar addini muke ko'ina, a mota, a kasuwa, a masallaci, a hanya, a rediyo, a telabijin, da sauransu. Don haka ilimi yai yawa, amma tsoron Allah ya karanta.
A nan, za mu ambaci masu sai da kaset a tashoshin mota, kasuwanni da shaguna, zaunannu ko wadanda ke kan babura. Hakaza lima man masallatan guraren kasuwanni da tashoshi, da kuma, a karshe direbobin motocin haya da ke long jani, watau masu jigila tsakanin garuruwa. Duk wadannan gurare me da basu kamata a rika sa wa'azi a cikinsu barkatai ba. In kuwa za a sa, dole a san wane iri za a sa.
Toh. Ina ga yakamata mutanen Arewa Musulmi su yi wa kansu fada. Mu san cewa in mutum ya bar daji ya zo gari ya zauna to dole ya rabu da halin dabbanci, ya san cewa sauran mutane suna da hakki, kuma akwai doka da ta hana cin hakkin mutane koda kuwa ta hanyar holo da Kur'ani ne. Kuma in don Allah ake wa'azin, to Allah bai ce a yi haka ba. Idan kuwa kungiya ake yiwa, toh ladan yin wa'azin nan da aka sa shi na gun mutane. Shi ya sa ba kasar duniya da za ka je ka samu ana irin wannan mugunyar tabi'a sai Najeriya. Ko a kasar Makka inda nan ne tushen addinin basa sa wa'azi a lasifika yadda muke sawa.
Ko a sallah ne, Allah ya cewa Annabi ya sassauta karatu. Mai shahararren littafin nan Madkhalu, Ibnul Hajj, ya yi bayani mai tsawo akan al'adar yin wa'azi da daga murya a masallaci. Ka ko san a kasar Hausa, ba littafin da Shehu Usumanu ya cirawa tuta irin Madkhalu, don na taba ji wajen malamina Malam Isa Talatan Mafara na Sokoto a 1987 cewa lokacin da Shehu Usumanu ya samu littafin sai da ya daga shi a bainar jama'a ya yi masa kirari ya ce, "Wallahi ina murna da samun littafin nan fiye da murnar cin Alkalawa." Haba Malam. Ka ji masu yi don Allah. Haka kuma Yyida Sabiq a cikin shahararren littafinsa na Fiqhus Sunnah, a babin kiran sallah, ya nuna yadda magabata suka ce wa'azi da sauti mai karfi kafin sallar asuba bidi'a ce mummuna.
Akwai abubuwa biyu da suke damunmu a nan Arewa har harkar addini na nema ta zame mana matsala. Da farko dai bamu da gwamnatoci masu karfi da za su tsaya a wanzar da doka yadda aka shimfidata. Duk hukumominmu masu rauni ne. Wannan raunin shi ya sa kowa yake abunda ya ga dama. Muatane Lamar ruwa suke, kan aka barsu sai su malala su koma rayuwar da Ba doka, irinta dabbobi su kuma suna ganin 'yanci aka basu. Sai ka ji mutum ya ce: "yoto ai in masallacin kaza sun yi lasifika suna sa wa'azi muma sai mu nemi Alhaji wane ko mu yi karo-karo mu saya mu rika sa namu." Sannan kuma in da wani gwamna zai yunkura don tsai da doka balle kan abunda ya shafi addini, toh, duk malamai sai su tsangwameshi, su kafirta shi, su ce yana yaki da Allah. Su kuma gwamnoni tunda suna son mutane lokacin zabe sai su kyale al'umma ta yi ta lalacewa. Subhanallah.
Na biyu shi ne malaman addini da almajiransu sun gagara yiwa addinin musulunci gata. Yau ko matarka ce kana son ka boyeta a gida sai ya kama tilas ta fita. In ko za ta fitan, sai ta yi lullubi, ka sa ta a motarka ku tafi tare don kar wasu su ganta su yi sha'awarta ko su ci mutuncinta. Wannan shi ne kishi Wanda Annabi ya ce maras shi ba yi da imani. Amma mun gagara yiwa addini wannan gatan. Ai ya kamata malami da almajiransa a samu sune suke kishin addini da al'ummar annanbi da yi mata lullubi ta yadda wasu ba za su ji sirrinta ba. Sai ka ce ba ma karanta surar "la tattakizu"?
Kuma ai yakamata mu ne zamu tallata addininmu mu yi masa ado don wasu su so shi. Ta haka kakanninmu maguzawa suka karbi addinin. Kanda da kaulasen addini ya zo kasar Hausa, billahillazi da har yanzu muna nan muna bugun giya tare da su Shehu Nasoba, Dan Ille Arne, da Narana, da Jikan Taru, da Alu Nabagara. Sannan bai kamata malamai don sun dau hanyar kungiyanci da son duniya ba su rika tsoron gayawa mabiyansu gaskiya. In yaro ya dauko al'adar sa kaset a masallaci, ayi masa fada a hana shi a nuna masa sharrin yin haka. Amma a rika kyale mabiya suna abun da suka ga dama don kawai su ci gaba da zama a kungiya ni a ganina ba daidai ba ne.
Ra'ayina game da lasifika a masallaci shi ne ayi amfani da shi wajen kiran sallah, da isar da sautin wa'azin da ake ga wadanda ke nesa da mai huduba. Duk wanda a gari yake son jin wa'azi ya zo masallaci ya ji. A masallacin ma sai in ba mai sallah kafin a sa wa'azin, koda kuwa nafila ce. A duba Madkhalu. Duk abunda aka yi fiye da wannan ya zama sharri. Muna fata malamai da ahugabannin kungiyoyi da almajirai Za su taimaka isar da wannan salon da aiki da shi.
Allah ya rabamu da sharrin shaidan da zai zayyana mana munanan aikinmu ya ce mana addini ne. Allah ya hada kanmu bisa alheri ya kuma bamu ikon yiwa addininsa sutura, ya ficce mu cin hakkin jama'a. Allah ya shirye mu duka. Allah jikan su Malam Idi, da maikobi, da Malam Dabura da suka yiwa addini hidima da muryarsu mai albarka a wancan karnin har muka wadatu da ita. A lokacin ba lasifika, ba takara tsakanin kungiyoyi da masu wa'azi wajen burge jam'a.
Haza wasalam.
Tilden Fulani,
16 May 2011
Babban matsala shi ne yanzu alummar Musulmin Najeriya babu jagoranci. In ba rashin jagoranci yaya za'a yi masallati su yi yawa da kuma salla a mabanbanta lokuta ba? ya kamata ne ace malaman sun yi fatawa a kan yadda ake amfani da sifika. Allah ya sakawa Alyu Tilde da alheri.
ReplyDeleteALHAMDU LILLAHI, DR TILDE Allah ya saka maka da alheri.
ReplyDeleteLalle wannan batu ne mai muhimmanci wanda ya kamata duk wanda ya karanta ya isar da sako, musamman Manyan gari wadanda suka gina masallatai akofar gidajensu ko kuma suke jagorancin komitocin masallatai, su tabbatar sun tsawata akan yin amfani da lasifika barkatai.
Yan uwa masallata mu rinka tunatarda juna akan hakkin alumma dake kammu.
Shugabannin kananan hukumomi ko na kusa da su, su sanarda su aka muhimmancin su tsawatar akan haka. Allah ya shiryemu, ya kuma bamu ikkon yi saboda shi.
A huta lafiya,
Abubakar Yamusa
Assalamu Alaika Dakta Tilde,
ReplyDeleteAllah saka da alkhairi da wannan fadakarwar da kayi. Ina tunanin da zai yi kyau idan ka bude gidan rediyo ko wata kafa ta watsa bayanai cikin sauki inda wannan sako naka mai amfani zai dinga isa zuwa ga al'ummarmu wanda basu samu damar karatu ba.
kungiyar izala itace babbar matsalar da ta jawo duk wata musiba da take damun alummar musulmai a nigeria.domin sune kowa malami a cikinsu.sunfi kowace kungiya alaka da azzalumai.
ReplyDeleteDr Tilde,ka sosa min inda ke min kaikayi. Dole a yabi mutane irin su Nasiru El-rufa'i wanda lokacin da yayi minister a abuja ya hana masallatan khamsa salawati kunna lasifika haka kuma chochina. Idan za'a kunna to iya sipikun cikin masallacin kawai za'a kunna. Wannan yayi aiki,domin kafin ya zama minista,kirista,ganin yadda musulmi suke cika samaniya da sautin lasifika sai suma suka fara,da assussuba sai su dauko irin lasifikar hannu su rinka bi layi layi wai suma suna wa'azin asuba. Idan har Nasiru El rufa'i ya hana kuma ya hanu to kenan shuwagabannin mu suma zasu iya.
ReplyDeleteWani abun ban haushi dadin dadawa ma shine toshe hanyar mota idan ana wa'azi ko za'a yi sallah.
Dr.Tilde Allah Ya saka ma da alherinSa Ya kuma kara ma basira da hazaka.Da fata wayanda aka yi domin su sun ji.
ReplyDeleteMalam Allah ya sa kar kai ma a kafirta ka sabo da gaskiyar da ka fada. Duk mun san kungiyar da ta yi fice wajen kafirta musulmi, ballan ta na mabiya wasu addinai.
ReplyDeleteSheikh, Allah Ya saka da alheri. Kayi tsokaci akan daya daga cikin manyan matsalolin Musulmi a Nigeria to Arewa. Harkan lasifikoki din nan da kuma tare hanyoyi lokutan Sallar Jumma'a abubuwane dake ci mana tuwo a kwarya. Shin karamin sanine ko rashin wayewane? Nasan dai ba izgilanci bane, kuma ba mugunta neba.
ReplyDeleteAllah Ya ba Musulmi ganewa rayuwatai.
Malam Allah ya saka da alheri. Amma ka manta baka tabo masu damun mutane da kade-kade ba da sunan son manzon Allah(SAW) musamman lokacin mauludi.
ReplyDeleteMalam,
ReplyDeleterabona da jin sharhi na tsage gaskiya komin dacinta, in ban da wannan, sai wanda ka rubuta a kan maganar ganin watan azumi a jaridar turanci ta daily trust can a shekarun baya.har yanzu ina tare da hard copy a cikin akwatina.
ALLAH ya jikan almajirinka kuma yaya na Ismaila Adamu.
Ahmad Isa Hassan
Allah Ya ba da lada. Hakika wannan fadakarwa ta yi, sai dai abin da ya rage shi ne, mu taru mu rungumi gaskiya, mu kuma yi aiki da ita. Idan ba haka ba kuwa, lallai za mu yi batan-baka-tantan.
ReplyDeleteMalam Tilde, idan Allah Ya yarda, zann ari wannan sharhi naka, in makala shi a Shafin Gizago, na Jaridar Aminiya, domin dimbin makaranta su amfana.
Allah Ya amfanar da mu gardin gaskiya kuma ya kiyaye mu daga kurbar gubar karya. amin.
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
byahuza03@yahoo.com
08065576011
Lallai Idan rana tafito tafin hannu baya taba iya kareta. Malam Aliyu Tilde, wallahi kasosa mun abunda keyimun kaikayi. Ala kulli hali, idan na tuna da yarda kasan nan take musamman (Arewacin kasannan) akan harkan Addini sai addu'a wallahi. To Alhamdu Lillahi da wannan sharhi, kuma in Allah ya yarda za'a isardashi. Allah yayi mana muwafaka, ameen
ReplyDeleteLallai Idan rana tafito tafin hannu baya taba iya kareta. Malam Aliyu Tilde, wallahi kasosa mun abunda keyimun kaikayi. Ala kulli hali, idan na tuna da yarda kasan nan take musamman (Arewacin kasannan) akan harkan Addini sai addu'a wallahi. To Alhamdu Lillahi da wannan sharhi, kuma in Allah ya yarda za'a isardashi. Allah yayi mana muwafaka, ameen
ReplyDeleteAllah ya saka da alheri malam. Amma sai dai ka manta baka tabo bangaren masu damun mutane da kade-kade da sunan addini ba, musamman lokacin MAULUDI.
ReplyDeleteTo ka fadi gaskiya amma na ga ka fake ta wani gurin ka nuna IZALA ce ta kawo lasifika da sa wa‘azi a masallatai
ReplyDelete