Monday, June 6, 2011

Sharhi na 6. Lalacewar Arewa (1) Watsi da Ilmi

SHARHI NA 6.
Na Dr. Aliyu U. Tilde

LALACEWAR AREWA (1):
WATSI DA ILMI

Ra’ayi tsakanin masu sharhi kan al’amuran yau da kullum ya daidaita kan cewa ganin yadda Arewa ta sha kaye a zaben da ya wuce, yakamata ‘yan Arewa suyi dogon nazari kan matsalolin da suka addabi wannan sashi na Najeriya da niyyar samun mafita a nan gaba. Ganin haka na yi niyyar jera sharhi kan al’amuran da nake ganin sune kan gaba wajen mai da Arewa baya. Kamar yadda aka saba, a ciki za mu tsage gaskiya ba tare da son rai ba ko tsoro. Sai mai karatu ya biyoni mu je zuwa…

Abu na farko da zan tattauna a kai shi ne yadda ‘yan Arewa suka yi watsi da ilmi. Wani zai ce “Ka ji dokata kuma. Ya zai ce mun yi watsi da ilmi bayan gashi jiddin wala hairan muna fadi tashi wajen ilmantar da yaranmu a makarantun addini da na boko, daga firamare har jami’ia? Yaya za a ce an yi watsi da ilmi idan a yau ana samun yawan masu digiri fiye da a kowane lokaci a cikin tarihinmu? Yaya za a ce ana watsi da ilmi bayan ga ma’aikatun ilmi suna gudanar da shi, ana daukar malamai aiki, masu wa’azi da kungiyoyin addini suna karuwa fiye da da?

Irin wadannan tambayoyi tabbas suna iya bijirowa a zukata kuma su makantar da mai nazari ga tunanin cewa in yara na zuwa makaranta, ana samun masu takardun shaida kala kala ko mahaddata kur’ani da malaman hadisi da malamai masu wa’azi shi ke nan al’umma tana baiwa ilmi hakkinsa. Abun ba haka yake ba.

Watsi da ilmi da muka yi shi ne mun mai da shi abun samun abinci. Ba ma nemansa don mu bunkasashi ta hanyar sabunta shi, da bincikensa da aiki da shi. Da zarar mun samu takardar shaidar fita daga makaranta, shi ke nan, mun jingine karatu. Ba sauran sayen littafi a fannin da muka karanta, ko bin diddigin sabon ilmin da ake wallafawa a ciki koda yaushe. Wanda muka karanta din ma ba ruwanmu da bitarsa, in dai ba abunda ya zama dole ba kamar ga malaman makarantu don koyarwa.

Haka kuma ba ruwanmu da fadada saninmu ta yadda za mu karanta wasu fannunnuka banda wandada muka kware a ciki koda kuwa wanda ke da dangantaka ne da su, wanda abu ne da ya zame wajibi ga dukkan wanda ke son sanin abunda duniya ke ciki ko ina ta nufa.

Hakanan kuma bamu damu da bincike kan ilmi ba don karuwarmu da duniya baki daya. Yan Arewa da suka yi fice don gano sabbin abubuwa na ilmi ko kirkiro fasaha wace duniya bata san da ita ba kalilan ne kwarai, in akwai ma.

A karshe, ba ruwanmu da aiki da ilmi. Hasali ma, mai ilmi gaba ake da shi a nan Arewa. Shi ba komai ba ne da za a waiwaya in matsala ta taso, ko za a saurari ra’ayinsa akan muhimman al’amura da za su yi tasiri bisa rayuwar jama’a. Abun da aka sa gaba bin son zuciya. Kudi sune komai. Sai a jingine ilmin a gefe, musamman a gwamnati, a karya doka, a take hakkin mutane, a tafka ta’asa wacce za ta hallaka al’umma don amfanin mutum daya ko biyu.

Ga misali, duk masu sata a gwamnati sun san komai game da illar satar da suke ga al’umma, walau ta kudi ko ta kayan morewar jama’a idan. Malami ya san satar alli, da takardu, da na’urorin bincike abu ne da zai gurgunta ilmi a makarantarsa, amma akasarin shugabannin makarantu sai su yi biris da ilminsu su yi ta dauke dauke a makarantun da aka basu amana. Haka jami’an asibiti da ke sace naurorin binciken likita da magunguna. Haka injiniyoyin da ke aiki a ma’aikatar ayyuka, wadanda ke aringizon kwangila ta yadda a maimakon kudin da ake da su su gina asibitoci shida, sai a bada su a ginin asibiti guda. Haka masu daukan ma’aikata, sai su dau maikatata bisa sanayya ko cin hanci su bar kwararru. In a makaranta ne sai a bar wanda yake da ilmi a dauki wani jaki wanda zai hallaka rayuwar yara akalla arba’in duk shekara tunda bai san abun da zai koya musu ba. In ka ce ayi amfani da sani, to ka zama abokin gaba.

Wannan hali namu na watsi da ilmi ta hanyoyi dabam dabam shi ya sa muke gagara fahimtar abubuwa idan suka taso mana, shi ya sa tattalin arzikinmu yake ja da baya ko yaushe, shi kuma ya sa al’ummomi da suke baiwa ilmi muhimmanci suke tsere mana a dukkn fannonin rayuwa.

Ashe ba abun mamaki ba ne muka zame al’umma wace ba ta son karatu. Ko mai karatu zai tuna yaushe ya je kantin litattafai don ya duba ya ga ko an kawo wani littafi da zai amfaneshi inba wanda yaransa za su yi amfani da shi a makaranta ba? Yaushe ne in ya je kasar waje zai dawo da akwati guda na sabbin litattafai da aka buga a cikin fanninsa?

Wannan sakaci shi ya sa aka samu karancin dakunan karatu da kantunan sai da litattafai da masu mawallafa a nan Arewa. A Arewa kaf, zai yi wuya ka samu kantin da, alal misali, ke sai da sabbin litattafai da aka wallafa a shekarar da ake ciki, koma a shekaru biyu da suka wuce. Duk litattafan ko dai na ‘yan makaranta ne ko tsoffi ne da aka yi gwanjonsu a kasashen waje don sun yi kwantai tun shekara goma ko talatin da suka wuce.

Akwai ranar da na nemi kundin tsarin mulkin Najeriya a Gombe da gaggawa don in yi amfani da shi wajen rubutu amma na rasa a kantunan garin kaf. Muhimmancin wannan kundi kuwa ya kai ace akwai shi fassare cikin hausa a kowane gida, bama a kanti ba. Hakaza kudayen dokoki dabam dabam. In an buga na zabe, ga misali, ya kamata a ce kowa na das hi, don mu san tanadin da zamu yi wajen cin zaben. Amma haka muke tinkarar abubuwa cikin jahilci. A karshe a mana zarra saboda lalaci wajen neman ilmi. Ina ga yayana Jega zai iya yin dogon sharhi akan wannan, tunda shi ganau ne ba jiyau ba.

Haka kuma ga dokar ‘yancin tambayar bayanan gwamnati an sa hannu a kanta satin da ya wuce. Yanzu haka za mu zauna tsawon shekaru ba wanda ya mallaketa in ba wasu kalilan daga cikin ‘yan jarida ba. Alhali kuwa yakamata ace mun fassarata da Hausa nan da nan (kamar yadda su Shehu Usumanu suke juyen litattafai da wakokin a da) don kowa ya san hakkinsa na samun bayanan da zai yi amfani dasu wajen yakar kasassabar da ake a gwamnati daga karamar hukuma har ta tarayya. Wannan hali na ko in kula ba zai haifar mana da alheri ba. Don haka yau ake juyin masa damu a Najeriya yadda aka ga dama. A karshe sai a barmu da fargar jaji da tunzuri na babu gaira babu dalili.

To da me muka dogara in bamu dogara da littafi ba? Akasarin lokacinmu muna bata shi ne a hira – mu maza. Mata kuwa suna gida suna ta girki, ko kallon fim, ko tadi da gulmace-gulmace irin nasu. A kowane gari, mutum zai kirga daba ta hira bila adadin. A nan ake sharhi kan siyasa, da gulman duk wanda ya wuce – mace ko namiji – da yada sharri cikin al’umma. Hatta wasanni malam bahaushe ya daina yi. Ga filayen nan an gina masa amma sai lalacewa suke, ko wasu su mora, shi ko ya yi ta fama da ciwon hawan jini, sa suga da sauransu.

In ko yana son sanin abu sabo, to sai ya dauki rediyo ya saurari shirin safe, ko na rana ko na dare a Muryar Amurka, Ko ta Jamus, ko BBC. A ganin malam bahaushe nan ne zai samu ilmi kan al’amura. Har ma yana yiwa kansa kirari cewa ya fi kowace al’umma sauraren rediyo a duniya. Amma abun kunya ba zai iya yiwa kansa kirari da cewa ya fi kowace karatu ba. Ya dogara da rediyo ne don tsabar lalaci tunda ba zai iya fidda kudi ya sayi littafi ko jarida ba. Ita kanta jarida ba zata ilmantar da mutum ba fiye da labarai da ra’ayi balle rediyo da ke fadin abu a takaice, a gurguje, ba tare da zurfafawa ba kamar yadda littafi ke yi. Ilmi sai a littafi, wanda dole a koyawa kwakwalwa abota da shi a koyaushe.

Ya kamata ‘yan Arewa su fara baiwa ilmi muhimmancin da ya kamaceshi. Su azuma wajen nemansa da farko, sannan su ci gaba da ingantashi ta hanyar karanta sabbin abubuwa da duniya ke ganowa. Daga nan sai su zurfafa wajen tunanin yadda za su yi amfani da ilmin wajen warware matsalolin da suka addabesu, daga nan har ma su yunkura wajen gano sabin abubuwa da duniya bata sani ba.

Wannan shi zai zama mataki na farko wajen fahimtar duniyar da muke ciki har ya kaimu ga tafiya kafada da kafada da sauran mutane, walau a nan gida Najeriya ko a kasashen waje. Dole ne mu raya al’adar karatu da magabatanmu suka bar mana, wacce ita ta sa muka kere saura a da har muka kafa dauloli da aka assasa akan ilmi lokacin da wasu suke rayuwar dabbobi a daji, suna cin mutane suna gudanar da mugayen al’adu. A yau, sun wucemu don sun baiwa ilmi muhimmanci, sun yi tsayin daka wajen gano shi, da kirkiro abubuwa dabam dabam da suka yi amfani da shi suka mamaye duniya.

A nan gida Najeriya ma idan bahaushe bai maida hankali kan ilmi ba, to zai zame leburan sauran ‘yan Najeriya wadanda suke kokarin kwarewa a fannoni dabam dabam na cigaba, shi kuwa an barshi da daba, inda yake gulma da yada sharri.

Yakamata dukkan ‘yanbokonmu su kasance suna sayen sabbin litattafai don wayar da kanunsu da al’ummarsu. A koyaushe, yakamata a samu danboko da sabon littafi ko’ina zai je yana karantawa wanda daga ciki zai fito da abubuwan da al’ummarsa zata amfana da shi. A shekara akalla kar ya gaza karanta litattafai 12, sabbi da nufin cigaba.

Hakanan kuma, duk danbokon da ke son amsa sunansa, yakamata ya daure ya tabbatar da yana amfani da dabarun rayuwar yau da kullum da aka koya masa a makaranta ko wandanda yake karantawa yau da kullum. Yakamata al’umma ta zame alkiblarsa, ba jin dadinsa da iyalansa ba kawai. Sauraren rediyo da karanta jaridu suna da amfaninsu, amma ba za su wadatar ba wajen baiwa al’umma alkibla da jagoranci da ke bukatar nazari mai zurfi.

In mun yi kokari, a lokaci kankani litattafai da karatu za su dawo Arewa, hakaza ilmi mai amfani da wanzar da shi a ko’ina. Ilmi shi ne kadai zai sa mu gane matsalolinmu da hanyoyin da zamu warwaresu. Wannan shi ne babin farko na jawo arziki wanda in ba shi aka bude ba, fatara kam za ta ci gaba da samun gindin zama har illa masha Allahu. Abun da za su biyo mata kuma na kasakanci, da lalacewa, da cututtuka, da zalunci, da bauta, za su cin mana, ko bajima ko badade.



6 June 2011

5 comments:

  1. Dr. ka fadi Gaskiya Allah ya sa mu gyara.

    ReplyDelete
  2. Babu shakka Aliyu ka fadi gaskiya. Lokacin da muna Yara kowace en'e (native authority) tana da Dakin Karatu gun da Ake kawo mujallai da littafai dabam dabam don amfanin jamaa. Kowacce makaranta tana da dan karamin dakin karatu. Ya kamata kananan hukumomi da jihohi su dawo da irin wannan tsarin.

    ReplyDelete
  3. Dr, Kayi gaskiya game da wannan sharhi kan sakacin Mallam Bahaushe wurin neman ilimi.

    Muna da sakaci so sai, kuma wannan ba zai kaimu ko ina ba, illar ga halaka. Mallam Bahaushe baya son karatu balle rubutu. Mafi yawanci, mun gwammace muyi shiru, ko da ko muna iya bada gudum mawa wurin fadakar da yan uwan mu.

    Ina main fatan zamu farga daga wannan halin na ko inkula na mu. Allah yasa mu gane, amin.

    Bissala,

    Shariff Ghali

    ReplyDelete
  4. Allahu akabar amfanin ilmi anfani dashi,mal Ali kayi anfani da naka, Ina fatar sauran masu zurfin ilmi irin naka su tashi haikan su dunga fadakarwa da kalubalantar masu mulkin yankunan su, mai makon neman mukamai don barin koyarwa azo aci daula,kuma a koma kauyuka a azamar da matasa zuwa naiman ilimi da aiki dashi, domin yanzu abin da ake nuna masu shine labarin mulkin sarakunan gargajiya na zamanin kakanninsu da cewar sune azzalumai,an manta cewar lokacin ne aka tilasta ma yayan talakawa shiga makaranta su zauna aji daya da yayan sarakunan,wadda yanzuko da wuya ka taras da dan chairman ko councillor da wani maaji ko head of personnel na LG na zuwa makaranta daya da yayan talakawan da yake mulka, hasali ma sun sace kudin habbaka ilimin,
    Allah sa talakawan da yayansu su gane masu cutar su a yanzu, domin yin magani ciwonsu ba na ciwon da ya sami kakaninsu ba.
    Hadi M Ruma

    ReplyDelete
  5. Mallam Aliyu wannan sharhi gaskiya ne kam. Mu kam akn wannan akida muka girma, kuma yanzu duk ta watse. Allah yayi jagora , Amin.
    Amina Husain

    ReplyDelete