Thursday, January 28, 2016

Sansanonin Ƴan Gudun Hijira Sun Zamo Fursuna

Sansanonin Ƴan Gudun Hijira Sun Zamo Fursuna

Na Dr. Aliyu U. Tilde

Dazu da yamma na saurari shirin VOA na karfe hudu da rabi wanda a ciki suka bayyana halin ha’ula’i da ƴan gudun hijira ke ciki a sansanoninsu a Jahar Borno. Kafin nan, da safe, BBC su ma sun tatttauna da Dr. Jibrin Ibrahim wanda ya bayyana irin wannan halin ni-ƴasu a wasu sansanonin da ya ziyarta a Jahar Adamawa. Haƙiƙa, waɗanan ƴanuwa namu na zaune a cikin wani halin tausayawa na ƴunwa, cunkoso, fursuna da taɓarɓarewar zamantakewa tsakaninsu.

Wannan ba soki burutsu ba ne. VOA sun sa hirar da wakilinsu ya yi da mazauna waɗannan sansanoni na Jahar Borno. A cikin hirar, dukkansu sun koka kan yadda ake barin su da ƴunwa wanda da kyar suke samun abinci sau ɗaya kacal ko sau biyu kaɗai a rana, da yadda ake baiwa mutane da yawa mudun garin masara ɗaya wai su yi abincin dare da shi alhali ba yadda za su dafa shi kuma ba kayan miya, da yadda ake ajiye fiye da mutane arba’in a daki guda, da yadda sojoji ke hana su fita daga sansanin ko a doki maza da mata waɗanda suka yi ƙoƙarin fita, da yadda mata da ƴanmata ke ɗaukan cikin shege a kullum, da dss.

Ƴan gudun hijirar sun koka da yadda gwamnatin jahar Borno ta yi banza da su bayan zaɓen da ya wuce alhali kafin zaɓe tana ba su abinci mai kyau da yi musu goma ta arziƙi. Ƴan gudun hijirar sun ɗora alhakin wannan hali na ko-in-kula ne a kan gwamnatocin tarayya, da jaha da ƙananan hukumominsu. Duk da cewa sun koka da hukumar NEMA ita ma, amma sun fi zargin gwamnatocin Jaha da na Ƙananan hukumomi waɗanda suka kasa ba da kayan cefane bayan ta Tarayya ta sayi hatsi.

Ƴan gudun hijiran suna fatar Shugaban Ƙasa Buhari zai taimaka ya fidda su daga cikin wannan matsanancin hali. Yakamata ya duba halin da suke ciki da gaggawa musamman a fannin rashin abinci da tsare su da ake kamar ƴan fursuna da muzgunawar da sojoji suke musu. Kar a mance, a baya, mun ga lokutta da yawa da sojoji ke muzgunawa farar hula musamman waɗannan ƴan Baga da sojoji suka ƙone garinsu ƙurmus kamar yadda Aljazeera ta nuna hotunan shekaru biyu da suka wuce. Yakamata Shugaban Ƙasa ya ɗau koken waɗannan bayin Allah da dukkan muhimmanci.

Yakamata da gaggawa ya ɗora wa hukumomi da masu ruwa da tsaki cikin lamarin nauyin fito da ingantacciyar hanya ta lura da waɗannan bayin Allah. Ba mabarata ba ne su. Mutane ne da aka zalunta. In ba a mance ba, cin hanci a gwamnati da rashin lura da aiki shi ya jawo rikicin Boko Haram ɗin tun farko.

Daga cikin hanyoyin warware matsalar, ƴan gudun hijiran sun nanata ba da shawarar a gaggauta buɗe garuruwansu don su koma su ci gaba da rayuwarsu ba tare da neman taimako ba. “Za mu zauna a bukkokinmu, mu je kamun kifi da rana, mu ciyar da kanmu, ba tare da neman taimako daga wajen kowa ba”, inji ɗaya da cikin ƴan gudun hijiran. Wahalar waɗannan ƴan gudun hijiran abin kunya ne ga Nijeriya wacce ba-da-mama ce ga Afrika gaba ɗaya.

Wanzuwar wannan hali a ƙarƙashin gwamnatin da aka sani da ƴaƙi da cin hanci ya zama wani abin fallasa da bai kamata a bari ƙasashen waje su ji ba. Kamar yadda ƴan gudun hijiran suka ce, ƴanuwansu da ke sansanoni a Kamaru ba su da matsalar abinci ko rashin lura. Damuwarsu kawai, tunanin gida, inji su.

Lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai yi wa hukumomin Gwamnatin Tarayya garambawul don ya ɗora nasa mutanen da za su tsai da gaskiya a harkar gudanar da su. Ina mamakin yadda zai iya samun nasara alhali mutanen tsohon shugaba Jonathan ne ke shugabantar waɗannan hukumomi har yau, wata goma bayan cin zaɓensa.

Hakaza, ya kamata Shugaban Ƙasa ya fara taka wa gwamnonin jihohi da jami’ansu birki saboda ana yawaita kuka da cin hancin da ke gudana a ƙarƙashinsu. A hana aikata ɓarna ya fi a horar bayan yinta. Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnatocin jihohin da ake da waɗannan sansanu suke kankange duk wanda zai je ya gano haƙiƙanin halin da sansanun ke ciki.

Mun shaida Buhari ya yi himma wajen yaƙi da Boko Haram. Allah saka wa dogo Ɗan Daura. Amma akwai sauran rina a kaba… Kai, bari mu yi ta gwari-gwari. Cin hanci da rashawa shi ne ummul haba’isin taɓarɓarewar halin da ƴan gudun hijira ke ciki a akasarin sansanoninsu a sashin Arewa-maso-gabas. Akwai babbar ayar tambaya a kan jahar Borno musamman. Mutane da yawa sun ce akasarin maganganun gwamnan jahar Borno game da ƴan gudun hijira ƙarya ce miraran. Ya kamata yaƙi da cin hanci wanda gwamnatin Buhari ta ke yi a yanzu ya isa can, tunda yaƙi da boko haram ya fara sauƙi. In ba za a ɗaure gwamnoni ba yanzu don suna da rigar kariya, ana iya kamawa da hukunta jami’an da suke amfani da su ba tare da ɓata lokaci ba. Rigakafi ya fi magani.

Mu kuma – da muke faɗi ba a tambayeka ba – ba za mu yi shiru ba sai ran da aka yi abin da ya kamata.

27 January 2016

No comments:

Post a Comment