Friday, January 19, 2018

Adalci Biyar Da Za Su Kawo Sauki A Harkar Mai

Karamin Ministan Mai, Kachikwu, da NNPC sun ce a yan kwanakin nan komi zai yi kyau. Sun ba mu hakuri kan akasin da aka samu kuma sun yi alkawari hakan ba zai sake faruwa ba.
Mun ji kuma za mu mance in man ya wadata. Amma muddin ba tsari aka canza ba, wallahi da sauran rina a kaba.
Tsarin da za a canza kuwa shi ne a yi a adalci a harkar mai a kasar nan. Duk abinda ba adalci a cikinsa ba zai yi kyau ba.
Adacin farko, a mai da duk yan Nijeriya daya, a yi mana bugun goro. Me ya sa a tsarin yanzu Lagas da Abuja aka dauke su shafaffu da mai, aka ce kason shigo da mai da aka baiwa NNPC nasu ne, mu sauran yan Nijeriya aka bar mu a b'atan-b'aka-tantan a hannun yan kasuwa?
Shin Lagos da Abuja sun fi sauran jihohi yawan kuri'un zaben Buhari ne? Sun fi Kano ne ko menene? Da me suka fita in ba da gaggan barayi ba? Da sakel. Wallahi ba mu yarda ba. Daya ke nan.
Rashin adalci na biyu shi ne a baiwa NNPC canjin Dala a farashin gwamnati na N198 amma yan kasuwan mai a ce su je su nemo tasu Dalar a kasuwar bayan fage, watau black market, kuma su zo su sayar mana da man, mu boran yan Nijeriya, a kayyadadden farashi. Ai wannan almara ce. Dalar Nijeriya ta Legas da Abuja ce kawai?
Nan ma wallahi dole a fada wa Yaya Buhari gaskiya. Amarya fa in bata hau doki ba, to fa ba za a aza ma ta kaya ba. Man fetur a rayuwar wannan zamani ba nishadi (luxury) ba ne; ba kuma tsinken sakace (toothpick) ba ne. Wajibi ne.
Tunda Yaya na son wanzuwar mai, a halin da ake ciki yanzu, dole ya baiwa yan kasuwar mai canjinsu a farashin gwamnati kuma ya kara musu da rangwame (subsidy) in ya kama, da kudin dako daga bakin teku har bakin tafkin Chadi in ya zama tilas. Menene amfanin Dalar? A rika baiwa bankuna a N199 su kuma su sayar a N320 kamar yadda ake yanzu?
Wannan ita ce gaskiya, daga kinta sai bata. Rashin binta shi ne babban dalilin rashin man da muke ciki a yau.
Kuma dole gwamnati ta ci gaba da himma kan gyaran layin mai kamar, yadda ta fara, da gyara rumbunan mai wanda shi Yaya Buhari ya gina tun muna samari.
Sai kuma, babbar magana: yaki da masu zagon kasa don haifar da yanayi na tsanani don bakanta wannan gwamnati da tunzura talakawa su yi mata bore. Na yi murna da na ji Yaya Buhari ya ce zai daka su kamar yadda daka Boko Haram. Allah ka taimake shi ya yi haka.
Adalci na hudu shi ne Yaya ya yiwa kansa adalci. Haba! Ya dau duk nauyin Nijeriya ya dorawa kansa. Ina aka taba yin haka? Ya kamata a samu babban ministan man fetur da karamin ministansa. Shi Chikwu ya tsaya a matsayi guda: ko dai ya dauki mukamin shugaban katafaten kamfanin NNPC ko ya tsaya a matsayin karamin minista. A yanzu dai ba zaunannen minstan mai. Duk part-time suke yi, alhali kuwa taura biyu ba ta tauno aka ce, ko bakin bakin kura ne, inji Shata.
Aiki a matsayin shugaban kasa kawai ko an baiwa mutum awa dari a wuni ya yi shi, wallahi sai ya ga awoyin nan sun kasa. Balle kuma Allah ya ba mu awa 24 ne kacal. Ciki sai mun ware na barci, da da'ami, da bahaya, da wanka, da iyali, da hutawa, da sauran abubuwan tilas na dan adam, sannan da aiki.
Yoto ko saurayi aka ce ya yi aikin shugaban kasa ai zai wahala, balle Yaya mai shekara 73. Wallahi ina ganin kokarinsa. Sai dai mu ce Allah ya taimake shi. Amma yana da kyau ya tuna shi dan Adam ne, ya yi wa kansa adalci.
Adalci kuwa shi ne ya karbi daman da tsarin mulki ya ba shi ta yadda zai samu fiye da awa 24 a rana. Tsarin mulki ya ba shi dama ya nada ministocin mai, babba da karami wadanda za su yi ta kai goro da kai mari a harkar mai. Bayan haka, an ba shi dama ya nada SA, SSA, PA, kai har da mai ba da shawara a harkar mai. In da Yaya ya yi haka, da awa nawa zai amfana da su a rana guda? Awoyi barkate!
A'a. Bai yi haka ba wai shi yana tausayin Nijeriya don ba ta da kudi da zata biya wadanda za su yi mata aiki a wannan matsayin. To ai da ruwan ciki ake jan na rijiya, Yaya am. In an yi magana sai masu makauniyar soyayyarsa su ce wai aiki ya masa yawa. A ganina wannan ba hujja ba ce tunda dai shi ya ce zai iya. Ganin abin da hakan ya haifar yanzu muke ba da shawara ya sassautawa kansa. Allah ba ya dorawa rai kaya fiye da abinda za ta iya.
Cewa kuma da yake yi wai ana da wahalar samun yan Nijeriya masu gaskiya ita ma ba hujja ba ce na dankara wa kansa ayyuka da yawa. Alal hakika, alama ce ma ta gazawa ya ce ba zai iya aiki ba sai ya samu wani Buharin su yi tare. Buhari daya ne kawai a duniya, tabbas, kamar yadda kowane dan Adam daya ne shi ma. Amma yana daga cikin kwarewar shugaba, ya iya aiki da mutane masu hali dabam dabam. Akwai masu gaskiya da yawa, kowa da irin tasa. Salon mukin da Shugaba ya dauka shi ke sa ya amfana da wasu ko ya hana shi amfana da su.
Dole Shugaba ya yi aiki da irin mutanen da yake shugabanta. Yadda zai yi haka har ya cimma nasara alama ce ta kwarewarsa. Don haka, Yaya ya tsaya a matsayinsa na Shugaban kasa kawai. Ya sau ministan man fetur ga wani.
Hakaza Kachikwu. Yana rike da matsayi uku: matsayin babban ministan man fetur tunda babban akasari ba ya gida; in ma yana nan, yana ta fama da matsayin Shugaban Kasa. Chikwu ne kuma aka nada karamin ministan man fetur; kuma, har ila yau, shi ne babban shugaban NNPC. Sana'a goma maganin mai gasa! Tabdi jam. Yaro in ba ka yi ba ni wuri.
Ba Inyamuri ba, ai ko aljani ne, zai ce abin da kamar wuya, fidda rakumi ta kafar allura. Ya kamata, a masa adalci, a bar shi a karamin ministan mai kadai, a nada wani shugabancin NNPC. Wannan ita ce gaskiya.
Wasu masana a fannin mai har cewa suke harkar mai a yanzu haka ta kai a yi ma ta minista uku. Na sama (upstream), na tsakiya (mid-stream) da na kasa (downstream). Mu ko biyun zaunannu aka samu sai mu hakura da haka, ya fi a ce ba ko daya takamamme wanda aikinsa kadai ke nan.
Adalci na karshe namu ne. Ganin yadda muka yi ta caccakar wannan gwamnati don gazawa wurin samar da mai a kwanakin nan, yana da kyau in man ya samu a garin da muke, mutane su rika fada a dandulan sadarwa don mu san gwamnati ta cika alkawarinta kuma an fara samun cigaba.
Ba tabi'a ba ce mai kyau a ce caccaka kawai muka iya. Don haka nake yabawa kanwata Mairo Haruna Halliru. Kwanaki da aka samu mai a wasu gidajen mai a Kano ta fada har ta kara da shawara.
Mu dai a nan jiya na sayi mai a N225. Amma a Magama, Jingir yana sayarwa N200. Allah ka kara kawo sauki.
Wai in duka ya yi yawa, na ka ake karewa. Wahalar mai ta sa mun mance da wahalar rashin wutar lantarki. Allah ya kawo mana saukinsa tun kafin mu iso gunsa mu fara kokawa a kansa shi ma. A nan ma dole a karbe wasu ayyuka daga hannun Fashola. A bar shi ya yi na lantarki kadai. Ayyuka da gidaje wani ya rike. Sannan a baiwa wani ayyukan ma'adinai. Kowannensu, aiki ne mai yawa a matsayin gwamnatin tarayya in ana son adalci.
Ya zama wajibi a kanmu mu ba da shawara ta gaskiya wa Yaya Buhari. Ba za mu yi ta malam Bahaushe ba, mu ce: Bar shi kawai. Ai kowa ya ce zai hadiye garma, sake mar kotar!
Hakkin Yaya ne mu ba shi shawara. Mun bayar. Hakkinsa ne wadanda suka ji kuma suke da iso a gunsa su mika ma sa shawarwarinmu. Shi kuma damarsa ce ya karba ko ya yar. Kowa yana aiki ne a matsayinsa.
Madalla.
Dr. Aliyu U. Tilde
16 Afrilu, 2016.

No comments:

Post a Comment