Thursday, January 18, 2018

Amsa A Kan Wakar Soyayya


Akwai wanda dazu ya tambaye ni dalilin rubuta wakata ta baya bayan nan, Begen Nijer: Ga amsata gajeruwa:
1. Gazal ne na kawo kawai mui raha
Da dadi na kalma cikin zuciya.
2. Idan ta yi ma sai ka mun addu'a
Ka ce jalla yafe wa dan Rakkiya.
3. Zunubbanshi amdan da kan kuskure
Ka share su jalla gaba ki daya.
4. Ka ba shi fasaha da lugga duka
Hazaka kaza har ya zam ya iya.
5. Ya raya adab din Fulani da Hausa
A kullum su kallai suna godiya -
6. Ga Allah da yai yo shi zamne cikinsu
Cikin so da kamna a duk safiya.
7. Ka karo irinai a duk zauruka
Birane da kauye na Nijeriya.
8. Du'a'in da ya yi gadon Bubakar
A Kwarbai gabanin ya zam ba shiya.
9. Ya ce jalla in za ka dau Bubakar
Maye shi da ni Rabbana ka jiya?
10. Ashe kau Sami'u ya na ji duka
Rakibu, Atidu suna bibiya.
11. Mujibu ya karba ya ce "kun" a gun
"Fa kana" gabanin ya bar Zariya.
12. Gabanin watanni kadan ya gama
Ya wake buhur duk gaba ki daya.
13. Ta'ala ka sa ya zame mai wasila
Na tsira ga sharrin mutan duniya.
14. A yaumul kiyamati in ya zaka
Ka sa shi a tutar mijin mariya.
14. Salatun ala man bihi nahtadi
Wa kana lana uswatan baqiya.
9 Agusta 2016
----------
"Bubakar" a nan ina nufin Abubakar Ladan Zaria. Na cire "a" din ne don ya dace da baharin mutaqarab da wakar take kai.

No comments:

Post a Comment