Saturday, January 20, 2018

An Kuma. Allah Ya Sake Karbar Addu'a

Kamar yadda aka yi da saniyata Fure, wata minaye ta haihu tana da madara mai yawa to amma fa ba a isa a tatse ta ba. Harbi ne, birgima ne, rike nonon ne da sauran artabu.
Mun yi imani da addu'a, mashaallah. Kuma Kur'ani mai girma magani ne ga damuwoyinmu. Jiya, da aka rubuta mata ayoyi ta sha, aka shafa mata, kuma aka tofa mata su, sai Allah ya karbi addu'a. Yau da safe ana shirin za kuma dargar da aka saba amma sai ga shi ta zama ruwan sanyi, ta tsaya cik, aka dabaibaye ta aka yi tatsa ba tashin hankali. Alhamdulillah.
Duk lokacin da ake da matsala, sai mu doshi ubangiji da ayoyinsa, da sunayensa da salati ga Annabinsa, ko a karance, ko a rubuce, ko a tofe. Daga nan sai mu sami waraka.
Allah ka ci gaba da nuna mana sirrorin da ke cikin littafinka mai girma, da.na sunayenka wadanda ka ce a kira ka da su. Ka ci gaba da amsa addu'o'inmu, ka dade mu sa halal duk matsawar rayuwarmu. Aamiina, ya rabbal aalamiiiiiiiiiin.

No comments:

Post a Comment