Saturday, January 20, 2018

Assignment Kan Tattalin Arzikinmu (1)

Na Dr. Aliyu U. Tilde
Ni din nan da nake b'ab'atu a kan tattalin arzikinmu, za ku sha mamaki in na ce ban san kome ba game da ma'adinan da suke karamar hukumata ko jaha ta, balle Arewa gaba daya. Ta yaya to zan iya taimaka wa raya tattalin arzikin yankina da wannan tarin jahilci a wannan fannin?
To na yi wa kai na karatun ta natsu. Gobe zan fara da karamar hukuma ta. Gobe ko jibi zan je in tambaye su duk bayanan da suka kamata game da ma'adinanmu kamar haka:
1. Wadanne ma'aidnai muke da su?
2. Wadanne ne ake hak'a wadanne ne ba a fara hak'a ba?
4. Ina shaidar lasisin masu hak'ar?
5. Menene adadin hak'ar da ake yi kama daga yawan ma'adinan zuwa yawan kudinsu?
6. Nawa hukumomi suke samu daga hakar duk wata ko shekara?
7. Menene matsalolin da hukuma take samu game da ayyukan ma'adinai a yankin?
8. Yaya za a warware matsalolin?
9. Menene rawar da kowane mataki na hukuma ke takawa wajen ayyukan ma'adinai?
Wannan farko ne. Daga nan zan wuce matakin jaha, suma in tike su da tambayoyi.
Mataki na uku shi ne in nemi ganawa da shugaban chamber of commerce na jahar a kan abinda na gano, su ma in ji ta su.
Mataki na hudu, sai Abuja, inda zan nemi bayanai kala-kala kan ayyukan ma'adinai a nan Arewa irin wadanda na shata a sama.
Zan rika ba da rahoton bincikena a kowane mataki ga jama'a da fatar haka zai bude idon jama'a ga wannan fanni da zai habaka tattalin arzikinmu.
To ba ni kadai ba. Ina ba da shawara mutane da yawa su yi haka a wurarensu don mu samu cikakken bayanai a wannan fannin, da zaburar da mutane, da yan kasuwa da hukumomi kan yin abin da ya kamata.
Wannan assignment din nawa ne da naka, kai mai karatu in kana da sha'awa.
Ni dai na diba wa kaina wata daya wajen kammala wannan bincike da fitar da kai na daga cikin duhun jahilci a wannan fannin.
Wa ya sani, kila ma a garin haka in gano wata rawa da zan iya takawa wajen harkar, ko ma in zama hamshakin dankasuwan ma'adinai?
Ina masoya Arewa? Ina masu neman halal? Ku zo mu hada kai kan wannan harkar.
11 Janairu, 2016

No comments:

Post a Comment