Wednesday, January 17, 2018

Buhari: Ayar Tambaya Kan Matsayinsa Game Da Malaman Kaduna da Makiyaya a Benue Da Taraba

A gaskiya yau da na ji muryar Maigirma Shugaban Kasa kan cewa abinda El-Rufa’i zai yi na korar malaman da ba su sami 75% a jarrabawar da aka musu ba ya yi matukar tayar min da hankali.
Banda labarin da aka taba bayarwa na mummunan halin da yan’gudun hijira suke ciki a Borno, ba abin da ya kai wannan labari girgiza ni a wannan gwamnati.
Duk shawarar da za a bayar da zai kyautata lamarin mun bayar ta yadda wadanda za a kora din ba za su yi yawa ba, amma duk a banza.
Saura da me, da wannan tambarin yarda da Shugaban Kasa ya buga wa kudirin raba magidanta 21,000 da aikinsu, Maigirma Gwamna zai ci gaba da cin karensa ba babbaka.
A gaskiya yadda Shugaban Kasa yake goyon bayan Gwomnoni don ya ji zakin bakinsu zai ci gaba da jefa mutane da yawa cikin hadari. Mutumin da bai biya malaman manyan makarantun da ke jaharsa ba na tsawon wata tara ko fiye, shi ke ikirarin inganta ilimi a jaharsa.
Makiyaya
Tabbas halinsa na yanke hukunci bayan sauraren bangare guda kawai ba adalci ba ne kuma zai ci gaba da jawo mana damuwa sosai.
Wani misali shi ne Gwomnonin Benue da na Taraba duk sun same shi a kan azzalumar dokar hana kiwo a sarari a jihohinsu. Na Benue yana buga kirji cewa ya sanar da Shugaban Kasa. Har da Kautal Hore suka ce ba za su bi dokar ba, ya kai kararsu wajen Shugaba Buhari.
Na Taraba kam har sojoji ya je nema gun Shugaban Kasa jiya wadanda za su taimaka danne makiyaya ko da za su yi bore idan ya fara dabbaka dokar. Har ma yana murna ya fito daga wajen Shugaba Buhari ya gaya wa yan’jarida cewa zai ci gaba da dabbaka dokar farkon shekara mai zuwa.
Toh, in damuwa ta zo a Benue da Taraba, kar Shugaban Kasa ya ce bai san da batun ba. Haka aka loba shi a sha’anin Maina. Da ta tashi masa, ya ce bai sani ba. A firgice, din matsi, ya ce ya kori Maina daga aiki. Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta fito fili ta karyata shi. Ta ce da sanensa.
A matsayinsa na uba, a wautata, na aza Shugaba Buhari zai saurari makiyaya su ma sannan ya kira taron zaman fahimta tsakanin bangarorin biyu ba tare da an kai ruwa rana ba. Allah ya ba shi matsayi a zukatan makiyaya da akalla za su saurare shi. Amma ina? Kamar yadda ya saba, sai dai ya zura ido yana kallon su.
Tabi’arsa ce yin gum a kan abu koda kuwa zai cabe wai don kar a ce ya goyi bayan wani. Haka aka sha fama a jam’iyyar CPC. Tun a lokacin na ce idan ya samu mulki wannan shirun nasa zai jawo wa kasa matsala. Don Allah idan manoma da makiyaya - daga Zamfara da Kaduna har zuwa Benue da Taraba - ba a sulhunta su ba lokacin mulkin Buhari wanda ya fi kowa sanin matsalolin kuma aka fi girmamawa, kuma Wanda ya taba rike mukamin Shugaban Makiyaya Fulani na Afirka gaba daya, yaushe za a sulhunta su a zauna lafiya?
Amma nan aka kashe mutane a Mambila, har yau ba abinda Gwamnatin Tarayya ta yi duk da ita ce take da yan’sanda da sauran jami’an tsaro. An kashe banza. Banda don yunkurin da GOC 3 Div ya yi na dakatar da kisan ba, da Allah kadai ya san inda abin zai tsaya. Waye aka hukunta cikin wadanda suka yi wannan kashe-kashe? Ba ko daya.
Amma har yanzu ba a yi latti ba, da zai karbi shawararmu. A kasa irin Nijeriya idan aka ce za a bar gwomnoni su yi rawar gaban hantsi, wallahi ba za a zauna lafiya ba a wurare da yawa. Zalunci za su yi na ina-naha.
Ni kam ahir! Ba na goyon bayan amfani da jami’an tsaron Gwamnatin Tarayya wajen dabbaka kowace azzalumar doka. Idan Obasanjo zai hana yan’sanda marawa dokar Shariah baya a jihohi, ban ga dalilin da zai sa Buhari ya bar su su marawa dokar hana kiwo ba a jahohi.
Kamar yadda na taba fadawa Shugaba Jonathan lokacin da ya kira mu kan rikicin Filato a 2012, Gwamnatin Tarayya ita ce gatan tsiraru a jihohin da ake nuna musu fin karfi. Idan kuwa duk da azabar da mutanenmu suka sha na shekara 16 a wadannan gurare, shi ma Buhari bai gane haka ba, to ba abinda za mu ce sai hasbunallahu waniimal wakeeli.
Allah sarki malaman Kaduna da abin ya shafa! Sai ku dau dangana. Abin ya zame gobara daga kogi, magani nata Allah.
😭

No comments:

Post a Comment