Wednesday, January 17, 2018

Buhari Tsakanin Magabta Da Yanzumudi

Muna taya Shugaban Kasa da iyalansa da yan Nijeriya duka murnar dawowarsa gida bayan dogon jinya da ya yi a Landan. Allah ya kara masa lafiya. Amin.
Mutane kala biyu sun cancanci in ce wani abu a kan su dangane da rashin lafiyar Buhari da dawowarsa.
1. Bangaren farko na taba sukarsu da rashin yakamata. Wadannan sune masu masa fatar sharri musamman ta mutuwa don su samu nasu ya hau mulki ko ma a ce su da kansu dama ta bude su hau. Na ce ta Allah ba tasu ba. Ran kowa a hannun Allah yake. Duk lokacin da ya ga dama sai ya dau abinsa.
Don haka wauta ce mutum ya yi fatar aukuwar abinda ba yi da iko a kai. Da muna da iko da duk makiyanmu sun mutu. Abin yi in sun k'agara, shi ne su jira. Buhari bai ce ba zai mutu ba. Zai mutu tabbas. Amma sai lokacinsa ya yi. Suma kuma su jira ta su. Tana tafe, walau kafin ta Buhari ko bayan tasa.
وما جعلنا لبشر من قبلك الخلد. افان مت فهم الخالدون؟ كل نفس ذاءقة الموت ونبلوكم بالشر والخير فتنة والينا ترجعون.
2. Kashi na biyu su ne masu zumudin da yake wuce gona da iri a kan saukin da ya samu da kuma dawowarsa har suna jifar wasu bisa zato. Sun cika yanar gizo da arashi da maganganu na tankiya ga wadancan jahilan. A ganina murna yakamata a hada ta da tawali'u. Wannan muhalli ne na godiya ga Allah ba na takama ba.
Shawara
A cikin ciwon Buhari akwai wata hiking wacce Allah kawai ya santa. Bayan ya nemi mulki na tsawon shekara 13, ya samu ana murna cewa abubuwa za su kyatata, kwatsam sai matsanancin ciwo ya kama shi. Wannan lamari ne na ubangiji da yakamata a bar masa shi kadai. In ya kawo sauki a gode, in ya munana a yi ta addu'a.
Cigaba da yi masa addu'a cikin kaskantar da kai ga Ubangiji ya fi maganganun arashi da ake yi. Banda addu'a bisa lafiyarsa, yana bukatar addu'a ta ya fahimci kurakuransa na rayuwa da na mulki da rokon gafara wurin Ubangiji da wurin wadanda ya munanawa ko da a kan kuskure ne.
Idan ka yi wa wani gwalo, misali, kan ya dawo, me za ka ce gobe idan ya koma Ingila in ciwon ya sake tashi kamar yadda aka yi a baya? Abubuwa a hannun Ubangiji suke ba hannun dan'adam ba.
A karshe, muna fata Allah kara masa lafiya ta yadda zai samu ya yi aikinsa na shugabanci cikin kuzari. Allah kuma ya shiryi shugabanninmu duka zuwa ga abinda ya fi zamewa maslaha a garemu.
Dr. Aliyu U. Tilde
20 August 2017

No comments:

Post a Comment