Saturday, January 20, 2018

Farfesa Dangambo Da Sauran Farfesoshin Arulin Hausa: Godiya Nake!

Dazu da rana na karbi gyararren kofi na littafina, Waka A Kan Baharinta, daga shahararren malamin adabin Hausa, Farfesa Abdulkadir Dangambo na Jami'ar Bayero ta Kano.
Ya duba littafin, ya yi gyare-gyaren da suka kamata sannan ya rubuta gabatarwan littafin watau Foreword.
A cikin gabatarwarsa, Farfesa ya yaba da aikin da kuma ambaton gudunmawar da littafin zai bayar wajen masu nazarin adabin Hausa da masu rubuta wakar Hausa. A karshe sai ya yi wani abu da ya ban mamaki, ya sa jikina ya yi la'asar.
Farfesa Dangambo ya ce mun bai taba rubuta waka a rayuwarsa ba sai dai nazarinta. Amma saboda ganin muhimmancin littafin da na rubuta, ga waka ya mun mai baitoci bakwai a cikin gabatarwar da ya rubuta. Wannan karramawa daga babban malamin adabi kamar Farfesa Dangambo ta ba ni tsoro da mamaki. Ba abinda zan ce sai in yi hamdala da godiya ga Allah Ta'ala.
Ba Farfesa Dangambo ne kadai ya duba littafin ba. Cikinsu akwai Farfesa Bello Sa'id, da Farsfesa Ahmadu Bello, da Farfesa, da Dr. Yakubu Azare, duk na Jami'ar Bayero, da Malam Ibrahim Isa na BBC Hausa Service, da Farfesa Balarabe Zulyadayn na Jami'ar Maiduguri, da Dr. Alhasan Bello, da Dr. Muhammad Imam, duk na Jami'ar Jos, da marubucin littafin Arulin Hausa Mal. Isa N. Sheshe, da Dr. Sheriff Almuhajir, da sauransu.
Wasu sun gama dubawa amma ban samu damar karbo kofi din da suka gyara ba tukuna.
A nan kusa zan shiga shirye-shiryen buga littafin don al'umma su fara amfana da shi.
Ga shi Farfesa Dangambo da dukkan wadannan gaggan malamai nake mika godiyata don hannun da suka sa wajen gyara wannan littafi wanda nake fata zai kawo gagarumin canji a salon yadda ake rubuta wakar Hausa ta ilmi.
Hakaza ina godiya ga Malam Ibrahim Sheme da ya fara gutsurawa mutane wakokin a shahararriyar mujallarsa ta FIM. Ina fata shi zai yi gyare-gyaren maibugawa in Allah ya yarda.
Madalla, madalla. Na gode.
Mi yetti on.
Dr. Aliyu U. Tilde

No comments:

Post a Comment