Saturday, January 20, 2018

Ga Arziki Na Mana Gwalo Amma Cin Amana Ya Hana

Dazu na gama tattaunawa mai matukar amfani da babban sakataren ma'aikatar ma'adinai ta jahata kan harkar ma'adinai a jahar.
Da nake dawowa gida na yi ta wuce duwatsu shimfide tsawon kilomita 100 daga Bauchi zuwa Tilden Fulani. Haka za ka same su birjik daga Tafawa Balewa har Ningi, daga Ningi har Tiga, a Jahar Kano. Wannan ya kai murabba'in 15,000.
Arziki sama. Arziki kasa. Amma yunwa a cikin dan adam.
Ko dutsen da ake cema aggregate stone, watau kamar granite, da ke cikin wannan murabba'in zai kai na tiriliyoyin dala. Za mu yi ta diba har tattaba kunnen tattaba kunnenmu. Bar ta ma'adinan da ke karkashin kasa irin gems, kuza, da sauransu, bar ta wadanda suke sa cebur ka diba irin su kaolin, lead-Zinc da sauransu da ke gabashin Bauchi.
A Takandar Giwa na dau hoton wadannan duwatsun granite da ke mun gwalo. Ba damuwa, watarana Allah zai nuna mana ana sarrafa su.
Ga arziki a zube amma yanboko da aka danka wa iko da su mun ci amana, don haka talauci ya yawaita. Kuma in ba mu yanboko mun cire cin amana a zukatanmu ba, wallahi, wallahi, har abada ba za a rabu da talauci ba. Cin amana da arziki ba sa haduwa wuri daya.
Ga abinda na ce bara a wakar Bulalar Gaskiya:
13. Tamkar ka ba almajirai nama tuli
Kome yawa tai bai isa sai gaskiya.
14. Don gaskiya ce za ta sa ai yo rabo
Kowa ya samu har ya zam yin dariya.
15. Ƙarya ko warwaso ta ke sa wa ku ji
Manya su ƙwashe sui ta holewar tsiya.
16. Yara suna kuka suna wayyo niya
Da mun yi loma ko guda ko ƴar miya!
17. Yara su zam tsinewa manya har abad
Dole a zamna babu canji duniya.
18. Mu ma na ƙas din kar ka zancen gaskiya
Don mun rasa ne mun ka koka ka jiya.
19. Da za a kawo ƴar amana adana
Cinye ta za mui nan da nan ba gaskiya.
20. Ƙirga a gwamna babu sarki ko guda
Duk mu talakkawa muke wannan tsiya.
Aliyu U. Tilde
15 January 2016

No comments:

Post a Comment