Saturday, January 20, 2018

GA TA DA ...

Kaya a kanta
Goyo a bayanta
'Da a cikinta
Sanda a hannunta
Jakuna uku a gabanta
Silifas a kafafunta
Hawan Panshanu
Kishiyoyi na biye
Girki da yamma
Miji na tafe
Tafiya mai nisa a kasa
Hadarin tafiya bisa titi
Hadarin 'yan fashi
Kisan muggan kabilu
Haka za ta kaura da rani
Ta dawo da damina
Tsawon kilomita 700
Duk saboda neman halal...
Allahu akbar!
Wasu kuwa...
Wai 'wayayyu'
Da aka ilmantar
Da dukiyar al'umma
'Yanboko irina
Na can cikin sanyi
Suna sace dukiyar jama'a
Suna cin amanarsu
Don kawai su da iyalansu su ji dadin duniya...
Kuma su ce su ne manya
Ka fada musu gaskiya su ce ka zage su
Ka ki musu fadanci su ce ka cika girman kai...
Hakkin matar can na wuyansu.
"Ce: mummunan aiki da kyakkyawan aiki ba za su zama daidai ba ko da yawan mummunan ya ba ka mamaki..."
Allah ya yi gaskiya.

No comments:

Post a Comment