Thursday, January 18, 2018

Gaskiya Mun Canza

Yanzu nake hira da ma'aikata nake ba su labarin yadda a nan Arewa amana da zaman aminci ya canza a cikin shekara arba'in kacal da suka wuce.
Na ce musu lokacin da muke yara a firamare a karshen 1960s da farkon 1970s, a kauyenmu, a ma'auna, masu sai da hatsi ba sa saka kudin awonsu a aljihu amma sukan daga gefen shimfida ne kawai su ajiye. Haka zai rika taruwa har karshen wuni kafin su nade shimfidarsu su koma gida. Su Danjaji, da Abdulkarimu - Allah ya jikansu - da duk ma'auna haka muka ga suke yi kuma ba labarin wani ya musu sata.
Haka abin yake wajen masu tebur. Inuwa Gurji mai sayar da goro da kayan kanti, da Sale Maisuga, da Bara - Allah ya jikansu - duk haka suke yi. Kana sayen goro ko suga na taro ko sisi a gunsu, nan suke ajiye kudin a karkashin shimfidar tebur din kowa na gani. Kuma lokacin sallah haka kowa zai je salla ya dawo, da wuya ka ji an yi masa sata. Kowa na da aikin yi kuma lamurra na rayuwa ba su taazzara ba don gwamnati na taka rawar gani wajen share wa mutane hawaye.
Abin lura kuma shi ne mutanen nan ba ilmin addini ko dukiya mai yawa gare su ba. Amma akwai ibada da gaskiya da amana. Don haka, a da, sauran kabilu suke daukan maganar Bahaushe da alkawarinsa a matsayin jingina (collateral). A kasar Ibo, a 1982, wani Inyamuri ya gayamun mun cewa, a da, in bahaushe ya karbi dukiyarka, ka kwantar da hankalinka don komi tsawon lokaci zai dawo maka da ita. Allahu Akbar. Allah ka Jikan magabatanmu. (Hawaye)
Kash! Amma albasa bata yi halin ruwa ba. Yau idan mutum yana tafiya a lungu, samari sai su kwace wayarsa, ko a bi shi har gida, a kwankwasa kofa, a ce ya bude dole ko a balla kofar. In ya bude a masa fashin dukiyarsa.
Ga masu ilmi, na addini da na zamani, amma da kyar ake samun masu gaskiya, sai wanda Allah ya yi wa rahama. Arziki ya tsaya cak ba cigaba don ba wanda za ka baiwa amanar jari ko lura da dukiya face dukiyar nan ta salwanta. Don haka sai dai ka takaita harkarka zuwa abinda za ka iya lura da shi da kanka. Talauci, in ba gaskiya kamar a wannan yanayi, dole ya yi katutu saboda rashin aikin yi da zai haddasa.
Abubuwan da suka jawo wannan da yawa:
1) akwai lalacewar shugabanni wadanda yakamata a yi koyi da su
2) akwai yawaitar ilmin zamani da ke tsananta son duniya a zukata
3) akwai matsalar tabarbarewar ingancin ilmin zamanin da yake sa fiye da 80% na yara suna girma ba su san komai ba kuma ba su iya komai ba - an raba su da sana'ar iyayensu da sunan za a basu ilmin zamani su zama akawu amma cin amana ya hana
4) akwai soke biyan haraji da jangali wanda ya sa mutane suna iya zama siddan ba abinda zai tilasta su su nemi na kansu har su biya haraji - su dai a ba su kawai
5) akwai tabarbarewar ayyukan da gwamnati ke samarwa kamar wutar lantarki, da ruwa, da ingantaccen ilmi
6) akwai rashin baiwa noma da aikin ma'adinai muhimmanci a Arewa
7) sannan uwa uba, yaduwar cin hanci da rashawa a tsakanin jami'an gwamnati wanda ke kara ta'azzara matsalar talauci da cibaya, da facaka, da riya a cikin al'umma; dss.
Lokacin da muke samari a jami'a, mun aza idan aka koma wa addini wadannan abubuwa za su kau musamman in an dabbaka shari'a. Kayya. Kamar yadda muke gani, hatta malaman addini da yawa da gwamnonin da suka jagoranci dabbaka shari'a ba su tsira daga matsalar rashin amana ba. Ilmin addini la shakka zai taimaka don za a samu kalilan wadanda za su yi amfani da ilminsu a matsayin garkuwa. Amma shi kadai ba zai isa ba. Bugu da kari, dabi'un kungiyoyin masu danganta kansu da addini, ciki har da na yan ta'adda irin su ISIS da Boko Haram, sun kashe wa mutane da yawa guiwa don tunaninsu dole zahirin rayuwar al'umma ya koma kamar na zamanin da, duk da cewa abubuwa da yawa sun canza a shekaru dubu da dari hudu da suka wuce. Don haka banda gaba, da tashin hankali da yaki da talauci, ba abinda wadannan kungiyoyi suke haddasawa jawo wa musulmi.
Dole ne a yaki talauci ko ta halin kaka. Talauci da hali nagari ba a safai suke zama wuri daya ba. Duk inda talauci yake, to fa tarbiyya za ta tabarbare. Za ka ga cikin shege ya yi yawa, sata za ta zama ruwan dare da duk sauran munanan dabi'u da dan adam zai shiga yi don ya rayu - ko da kuwa akwai karin ilmin addini ko yawan wa'azi. Annabi (SAW) ya yi gaskiya da ya ce, "Talauci ba zai tasamma mutane ba face kafirci ya ce, "mu je tare."
A yaki da talauci kuwa dole ne gwamnati ta dauki nata kuma jama'a suma su dauki nasu. Dole gwamnati ta inganta ilmi, ta samar da lantarki da hanyoyi da kasuwanni da asibitoci da ruwan sha a birane; hakaza dole ta zuba jari ta hanyar tallafi iri-iri a abubuwan da za su bunkasa aikin gona da ma'adinai da masana'antu.
Su kuwa jama'a dole su yi abinda ya kamata na tilsata yara su yi karatu da koyon sana'a, da cusa musu raayin tsaida gaskiya da tsoron Allah, da himma wajen neman halal, da neman yin zarra (excellence) a duk abinda suka sa a gaba, da tattali, da tausayin al'umma da halin yakamata.
Abin bakin ciki shi ne yadda akidar "kasuwa-kawai" ta mamaye tunanin yan bokon da ke baiwa gwamnati shawara a cikin shekara talatin da suka wuce. A wurin wadannan mutane, an yi al'umma ne saboda masu kudi, shi kuwa talaka nauyi ne kawai wanda yakamata a bar shi yunwa da ciwo su rika kashe shi ko yawansa zai ragu. A cewar wani marar kunyarsu - Bernard Mendeville a karni na sha takwas kafin zuwan Adam Smith - "talauci abin ragewa ne ba abin kawarwa ba", kuma ba kunya ba tsoron Allah ya ce, "Idan fa al'umma za ta ji dadi, to dole ne mutanenta da yawa su kasance jahilai kuma matalauta."
Wannan shi ne tushen akidar "neo-liberals", watau yan "kasuwa-kawai", wadanda da shawarwarinsu gwamnati mai ci take aiki kamar yadda na baya suka yi. Don haka a daina yi mana wani romon baka. Wannan ita ce gaskiyar magana. Shekara talatin ana mana alkawari abubuwa za su yi kyau amma har yau ba mu ga wani abu ba banda kara tabarbarewar tattalin arziki. In an yi magana su rika daga kafada wai suna da ilmin tattalin arziki, amma ilmin bai amfani kowa ba banda yada talauci tsakanin al'ummarsu.
Wadannan yan akidar "kasuwa-kawai", sun mamaye gwamnati suna tabbatar da sai an aiwatar da shirye-shiryen da banda kara talauci ba abinda suke yi a kasashe masu tasowa, inji Bankin Duniya da hatta wasu daga cikin masana tattalin arziki na Asusun Kudi na Duniya.
Ga shi dai talaka ya yi zabe a 2015 don a kwato masa hakkokinsa amma wadannan yan kasuwa da suka mamaye gwamnati sun hana, sai kara jefa talakan suke yi cikin tsabar talauci da yunwa. Kura da shan bugu gardi da amsar kudi. Kudi kam suna amshewa ta hanyar karya Naira.
Don haka, aminci irin na da ba zai samu ba a yau sai talaka ya yi aiki biyu: farko, ya daure ya yi nasa aikin da muka lissafa a sama; na biyu, yaki da wadannan yan akidar "kasuwa-kawai" da suke hana gwamnati yin nata ayyukan da kuma satar kudin jama'a da suke yi dare da rana.
Hakika zamani ya canza. Muma kuma mun canza. Amma canjin ba na d'a mai ido ba ne.
To kar ka jira sai al'umma ta canza ko gwamnati ta yi daidai. Canza halinka yau kuma ka dukufa wajen neman halal sai inda karfinka ya tsaya. Sai ka ga duniya ta maka kyau.
29 June, 2016

No comments:

Post a Comment