Saturday, January 20, 2018

Girbi Da Dadi, Samu Ne Da Wuya

Cikin abin da na koya ina yaro akwai wata waka da makwabtanmu na kabilar Buji na Jahar Pilato suke yi lokacin girbin dawa. Mahaifinmu, Allah ya jikan shi, yakan yi mana wakar lokacin girbin dawa, mu yi ta dariya musamman yanda yake kwaikwayon Hausar mutanen Buji:
Girbi dawa da dadi
Samu ne da waya
Nasara ya ce da sarkin Buji
Kada ka aje gashin baki
Yanzu da kaka ta yi kowane manomi na cikin annashuwar girbi da godiya ga Allah da ya nuna mana kaka. Duk da cewa ba a fara cin dawa ba, tuni aka fara cin wasu gonakin kamar na masara da shinkafa.
In masu karatu za su tuna, na taba nuno gonar ciyawar shanu da na shuka. To Allah ya sa an fara girbi. An gama da ta Brachiaria yau inda muka yi amfani da silasha wajen yayyanke ciyawar. Za a barta na tsawon kwana biyu don ta tsane ruwanta kafin a tattara ta a daure, dami dami. Gata nan a kwance a hoton farko.
Gobe in Allah ya kaimu, za mu yanke ta Chloris gayana. Ga hotonta nan a tsaye kafin a kwantar da ita gobe.
Wani abu da wadannan ciyayin shi ne shekara mai zuwa ba sai an sake shuka su ba. Sai dai kawai a samu takin kaji ko na shanu a zuba, in ruwa ya sauka sai su sake tohowa. Haka dai, haka dai, ko shekara 50 za a yi. Ciyayin da aka shuka tun zamanin su Sardauna a Cibiyar Binckiken Habaka Kiwon Dabbobi (NAPRI) a Zaria suna nan har yau.
Wadannan ciyayi ne masu daraja wadanda suke da amfani a jikin dabbobi. In da makiyaya za su samu tallafin filaye kamar hekta (kusan filin kwallo) biyar kowannensu, da tallafin gyaran filin, da isasshen iri na wadannan ciyayi, allabashin su makiyayan su ji da kwadago, da kakarsu ta yanke saka. Da sun daina taka sayyada zuwa kasashen yamma inda ba a maraba da su.
Akwai isassun dazuzzukan da za a yi haka da kuma kudin gudanar da ayyukan amma zuciyar ce ba ta da niyya. In akwai niyya sai dai ta satar dukiyar jama-a.
Abin mamaki shi ne 'ya'yan talakawa ne aka danka wannan mulki a hannunsu, amma sun kasa kishin jama'arsu da yan'uwansu talakawa. Allah ya isan mana.
Ga wadanda suka zage damtse suka yi kokari da damina suka shuka, suka noma, farin cikin lokacin girbi ya zo.
"Girbi dawa da dadi
Samu ne da waya."
Aliyu

No comments:

Post a Comment