Total Pageviews

Thursday, January 18, 2018

Hana Shigo Da Motoci Ta Border

Mun jima muna walawa, yara da magidanta da yawa suna samun kudin kashewa a nan Arewa ta hanyar amfani da birdojinmu wajen shigo da motocin "Tourist".
Yau fiye da shekara talatin ba ma bukatar zama a Legas ko Patakwal kafin mu yi aikin agent ko shigo da mota. Jakarka kawai za ka dauka ka ketara Kotono ko Lome, ka zabi motar da kake so ka tukota zuwa boda, ka biya kudin duty kamar yadda ake biya a bakin teku, ka taho da ita gida, ka yi mata lasin, ka rika amfani da abarka. Duk manyan motocin da nake aiki da su ta haka na same su. Ta karshe kam ma ni na taho da ita daga Lome har gida.
Mun gode Allah mun gode wa Shugabannin baya da suka ba da wannan dama da ta amfani miliyoyin mutane. Sun san akwai bata gari da suke bin daji, suke kin biyar kudin duti cikakke. amma duk da haka suka gwammace su duba amfanin da al'umma ke samu, suka bar jami'an kostan su yi iya kokarinsu wajen dakile matsalar. Haka suka mana wajen samar da takin zamani. Mun gode musu. Ba ka san amfanin abu ba, sai ka rasa shi.
Mun gode wa wadancan shugabanni da ba su ce don ana laifi, kawai sai a hana abu ba komi amfaninsa. Daga samar da takin zamani har zuwa shigo da Tourist ta boda, sun hakura suka ci gaba da amfanar da talakawa.
Makwabtanmu ma na kasashen Nijar, Togo, Benin da Burkina Faso, duk sun amfana. Sun samu kudin shiga, kuma ya taimaka wajen dunkule tattalin arzikinsu da na Nijeriya. Dankon zumunci ya karu.
Yau duk wannan ya kau. Gwamnatin Buhari ta soke shigo da motoci ta kan tudu, sai ta teku. Mun koma shekaru sama da talatin baya lokacin da mu da ke nesa da teku ba mu da madogara sai can. Mazauna bakin teku bukata ta biya. Kukansu na raguwar harka tunda aka fara shigo da Tourist ta boda yau gwamnatin dan Arewa ta share musu hawaye.
Na san za a ce saboda dalilan tattalin arziki ne aka dau wannan matakin. To ina ba da shawara cewa Abuja ma yakamata ta koma Legas don can ne tushen tattalin arzikinmu. To ma, meye helkwatar kostan take yi a Abuja. Ta koma Legas kawai inda can teku take. Haka ya fi dacewa daga fuskar tattalin arziki.
In saboda tattalin arziki ne, me zai faru idan kasashen da kogin Kwara ke wuce wa ta cikin su suka ce su ma za su datse shi don noman rani da samar da wutan lantarki kamar yadda Ethiopia ke yi wa kogin Nilu yanzu?
Ina ga yakamata a canza wannan shawara da sauran shawarwari wadanda aka yi su don kawai hukuma ta gagara wanzar da doka. Kamar yadda na fada a matsalar soke sayen takin zamani, wannan gwamnati ce da aka zaba don ta yi gyara, ba don ta ce tunda ba za ta iya gyarawa ba, to a kashe abin gaba daya. Shi madori ba ya karyawa don gyara, likita ba ya kisa don magani.
In gwamnati ta dage a kan bakarta, ba abin da mu da wadanda za su rasa aikin yi sai mu dau hakuri na wani lokaci har Allah ya kawo sauki.
Dr. Aliyu U. Tilde
6/12/2016

No comments: