Friday, January 19, 2018

In Ba Doka, Ba Canji (2)

Na Dr. Aliyu U. Tilde
(Karanta wannan sashi na biyu gaskiya sai mai kwazo. Akwai tsayi, amma zai amfanar. Yana da kyau ya kasance makaranci ya karanta sashin farko tukuna)
Mu sha ruwa mu koma aiki.
Kashi na biyu kuwa na ganin ba na kasa za a zarga ba in ana neman gyaran lamurra da farko. Sama za a duba. Ni ma na fi karkata ga wannan raayin don shi ya fi dacewa da tabi'ar halitta da kuma tsarin mulki na zamani kamar yadda zan bayyana yanzu.
Cikin hikimar Allah da ya halicci jiki sai ya yi ƙwaƙwalwa ya lulluɓeta da ƙashi don samun tsaro, ya kuma ɗora mata nauyin gudanar da jikin ilahirinsa. Ya kuma sa a tabi’ar ɗan adam, ƙwaƙwalwar zai fara karewa in an kawo wa jiki hari. Nan da nan hannaye biyu za su je su kare kai don kar wani abu ya same ta. In hannu bai isa ba sai a haɗa da ƙafafu, a sa kan a tsakanin gwiwowi, a dora hannaye a kai, a yi tsit. Wannan ya cire duk wata tababa cewa kai shi ne shugaban jiki. Halin da yake ciki ne zuciya take amsawa da bugu ya sa mutane a fahimtarmu muke ganin kamar zuciya ce ke tunani.
In kai ya yi kyau, ya bai wa jiki jagorancin da ya kamata, to jiki zai yi kyau a al’amurransa. Dole jiki kuma ya bi umarninsa ba tare da ƙi ba in dai ana zaman lafiya. In ya ce da hannu ya ɗaga, dole ya ɗaga; in ya ce ya ajiye, dole a ajiye.
To haka ma yake a tsarin zamantakewar ɗan adam. Shugaba shi ne kai, sauran al’umma gangan jiki ne. Don haka ake buƙatar shugaba ya kasance wanda ya fi dacewa da biyan buƙatar al’umma na wannan lokacin. Da wuya al’umma ta cimma wani abu ba da shugaba da zai bata shugabancin da take buƙata ba.
Mutanen Sin (China) suna cewa rundunar jakuna dubu wacce take shugabanta zaki ne, ta fi rundunar zakoki dubu wacce shugabanta jaki ne. Shugaba.. Shugaba dai.
A wani lokaci bayan Annabi Musa (A.S) da Bani Isra’ila suka shiga tasku, sai suka buƙaci a musu Sarki wanda za su bi, ya jagorance su a yaƙi don su samu kuɓuta daga wahala. Shugaba, Shugaba dai.
A tsarin yau na demokraɗiya inda ake bai wa mutane daman zaɓen shugabanninsu kuma ake da tsarin mulki, an yi iya ƙoƙari wajen bai wa shugaba haƙƙinsa, duk da cewa akwai sauran ɓangarorin mulki biyu – Majalisa da ɓangaren shari’a. Tsarin mulki ya baiwa shugaba damar gudanar da hukumomin zartarwa gaba ɗaya. Shi ke naɗa shugabanninsu kuma shi ke da kalmar ƙarshe a duk abinda suke yi. Komi sai sun kawo masa ya amince kafin su zartar.
Hakanan, shi kaɗai aka baiwa iko da tattalin arziƙin ƙasa da harkar tsaro da tsare doka ta yadda buƙatu biyu mafi muhimmanci wajen cin yaƙi kowanne iri ne – kuɗi da mayaƙa – duk suna hannunsa don ya ba su umarnin da ya dace. Kusan ka ce a fannin tsaro da gudanar da dokoki in banda wanda ya shafi harkar shari’a, shugaba shi ne wuƙa shi ne nama ko mu ce masa shugaba mai cikakken iko.
Wannan shi ya sa zaɓen shugaban ƙasa a kowace ƙasa mai gudanar da tsarin shugaba mai cikakken iko ya fi kowane zaɓe jan hankalin al’umma don sanin in aka yi kuskure wajen zaɓensa, to fa za a jima ana shan wuya; in kuma aka zaɓi nagari, to ana sa ran za a dace.
Ƴan Nijeriya sun san da wannan ƙwarai. A kullum suka shiga wuya sukan tuna zamanin da wasu masu kirki suka yi mulki. Kuma sukan so Allah ya dawo da irinsu, kamar shugabannin farko. Ko a lokacin mulkin soja, mun ga yadda samun shugaba yake taimakawa wajen canza komai a lokaci guda in dai yana amfani da karfin ikon da aka ba shi. Murtala misali ne mai kyau a nan.
Yadda Murtala ya yi a 1975 aka aza Obasanjo zai yi a 1999. Amma kash ya kasa, ya bar ƙabilanci ya rinjaye shi sannan kuma ya shimfiɗa damar cin hanci a gwamnatin siyasa da ta wanzu har zuwa yau. Shi ya sa kuma a 2002, muka tsananta kira ga Buhari ya shiga siyasa don ya zame mana shugaban ƙasa, watau kai – ko head, inji Bature – don ya warware mana al’amurra.
A duk waɗannan misalai, babu inda ake tsammanin mu mutane za mu gyara kanmu tukuna kafin mu zaɓi shugaba da zai gudanar da harkokinmu mu gyararrun mutane. Shugaban muke nema ya jagorance mu a yaƙin gyara, kamar yadda Bani Isra’la suka yi, kuma kamar yadda jiki ke jira kai ya jagorance shi. In ba kai mai kyau, ai gangan jiki ko shari’a ba ta hawa kansa. Ai ka ga mahaukaci firi yake. Ba hukunci a kansa, walau na addini walau na gwamnati.
Wannan ita ce fatar mutanen Nijeriya da suka yi dandazo suka kori Jonathan suka zaɓi Buhari. Suna fata – ko ma ka ce suna da yaƙinin – cewa in ya hau mulki zai gyara. Shi ma kuma kamar yadda ya ce a Kaduna bara, “Za mu gyara.” To duk da yanzu ya ce abinda yake tsammani na munin gwamnati a da ya samu ya wuce haka sosai, zai yi wuya a ce zai samu rangwame a kan zaton da ake masa na gyarawa da kawo canji, allahumma sai dai abinda ba ikonsa ba ne kamar a fannin shari’a ko majalisa. A nan ɗin ma ana sa ran ya san siyasar da zai yi amfani da ita ko kambun mulkin da zai murɗa ya zamo sun masa abinda yake so.
Don haka, ina gangan jikin Nijeriya za ta duba in ta samu matsala na gudanar da doka? Sama za ta duba, wajen Shugaban Ƙasa, ta koka masa don ta samu sauƙi. Shi kuma, in bai riga ya yi ba, sai ya yi amfani da madafun ikon da suka dace ya biya buƙatar jama’a ba yanzu ba kawai har ma don kar matsalar ta sake faruwa nan gaba.
An ba shi duk abin da yake buƙata wajen yin haka. Shi ne Babban Kwamanda na dukkan mayakan Nijeriya. In ya ce su yi, su yi; in ya ce su bari, su bari. Wanda ya ƙi, an ba shi dama ya ladabtar da shi walau shi da kansa in babba ne kamar hafsan soja; ko kuma ya sa manyan wanda ya yi laifin su ladabtar da shi mai laifin kamar yadda doka ta shimfida.
Sannan shi ne shugaban duk sauran jami'an tsaro kamar na farin kaya, kamar su ƴansanda, SSS, NIA, Kostam, Civil Defence, Road safety, coastal guards, da sauransu. Shi tsarin mulki ya aje shugabancin wadannan hukumomi a hannunsa a matsayin amana zai yi amfani da su, kuma an yi su ne don su tare masa faɗa da ƴan iska marasa bin doka a ko'ina. Muna iya ma cewa babu wani nau'in laifi da mutum zai aikata daga Tafkin Chadi har ka dangana da iyakar Nijeriya a kan Teku wanda ba hukumar tsaro ko ma'aikata (kamar DPR) da aka kafa don hana shi. A taƙaice, akwai daruruwar ma’aikatu da hukumomi waɗanda aka yi don su taimaka wa Shugaban Ƙasa. Shi ke da ikon naɗa sama da mutum dubu shida a muƙaman gudanar da su.
Don haka, in wadannan jami'an suka gaza don son rai ba don wani dalili wanda ya fi ƙarfin hukuma ba kamar talauci, to fa laifi a karshe dole shugabansu ya ɗau nauyin gazawarsu
Misali, mutane sun yi ta kokawa kan yadda aka shiga matsin man fetur da yadda aka bar jami’ai suke sharholiyarsu ba mataki da aka ɗauka na hana su, kamar wancan misali na labarin da Dr. Almuhajir ya bayar a NNPC na Damaturu. Shiga matsalar man kanta abu ne da yakamata a ce an kauce masa ta yadda ba sai an shiga mummunan matsatsi irin wannan ba. Wasu sun ce ai gyara ake yi kuma kowa ya san gyara na da zafi. E haka ne, in mai gyaran ya yi abinda ya kamata ba. In aka kawo masa gyaran targaɗe, to kar ya ce sai ya karya gaɓar ɓas kafin targaɗen ya gyaru.
Misali na biyu shi ne cewa bankuna suna cutar ƴan Nijeriya wajen canji duk da cewa suna samo canjin nan a farashin gwamnati don su sayarwa mabuƙata da gwamnati ta amincewa. Shugaban ƙasa tun watanni da suka wuce ya ce za a hukunta duk bankin aka samu da haka, amma har yau abinda kowane banki ke yi ke nan, ko a jikinsu. Wannan ya jawo tsadar kayayyaki da arzurta bankuna ta hanyar haram da jawo reni wa gwamnati. Da an hana bankunan zamewa “blackmarket”, da wasu abubuwan ba su yi tsada wa talaka har haka ba.
A waɗannan misalan da ire-irensu, abinda za mu so mu ga Shugaban Ƙasa ya yi shi ne ya hana faruwar waɗannan abubuwan ta hanyar amfani da madafun iko isassu da doka ta ba shi cikin zafafawan da mutane suka san shi da shi. Yin haka shi zai gyara wa kowane ɗan iska zama. A tawa wautar, ga abinda nake tsammani Shugaban Ƙasa zai yi, misali, a kan matsala irin ta Yobe da muka ambata a sama:
Ya kira manyan jami’an ƴansanda da na NNPC ya ce musu duk inda aka kawo labari da hujjar ana karkatar da mai zai bukaci shugabannin su kori commandan da ke wurin. In bai yi ba kuwa, shi Shugaban za a sauke. Mu talakawa kuwa a ce ana neman haɗin kanmu wajen kawo koke bisa hujja yankakkiya kamar hoto ko video. Ya nemi wasu mataimakansa ya ɗora su kan bibiyar wannan umarnin. Wannan ba zai ɗaukeshi awa ɗaya ba. Shi ke nan. Ya yi muzurai, ya bar mitin ɗin ba sallama.
Da zarar mataimakansa sun kawo hujjoji a wuraren da aka yi haka, to fa Babban Sifeton ƴansanda ya shiga uku balle kuma Shugaban NNPC. A guje za su tafi su ladabtar da kowaye da ke son jawo korarsu daga muƙaminsu. Ga kuma mataimakan shugaban ƙasa na bibiya sai an zartar da ladabtarwan. Da haka, ɗan mai kaɗan da ake samu kowa zai yi layi ya saya. Ba masu duron balle tsallakawa da shi waje har lokacin da zai wanzu a ko’ina.
Amma muddin ba irin wannan matakin shugaba Buhari ya ɗauka kan waɗannan abubuwa ba, ba abin da zai faru. Canji zai zame tatsuniya kawai. Wannan shi ne tsarin doka da ƙarfinta. In bai yi amfani da ita ba, talakawa ba su da yadda za su yi sai dai su ci gaba da kokawa har zaɓe ya zagayo. In sun ga za su sake zaɓensa ya ci gaba da shugabanci su zaɓe shi; in kuwa sun ga akwai wani wanda ya fi shi dacewa, sai su sauya da shi wannan ɗin, Yaya ya jefar da kwallon mangwaro ya huta da ƙuda.
Don haka a ce za a ɗorawa talakawa nauyin ɗaukan doka a hannunsu don a wanke Shugaban Ƙasa, wannan ba adalci ba ne. Haka nan kuma su talakawa su ƙosa har su ɗau doka a hannunsu, a rajin kansu, kamar yadda suka yi wa wani ɗan majalisa a Ningi jiya – suka bi shi da jifa – a gaskiya, shi ma ba daidai ba ne. Ya kamata su yi karatun ta-natsu su duba menene mafitar da doka ta ba su. Tabbas akwai mafita fiye da guda, daga kira har kiranye, wancan don a tattauna da shi a gaya masa damuwar mutanensa, wannan kuma don a kakkaɓo shi daga majalisa in ya ƙi.
Abun damuwa a gaskiya wajen mutane da yawa da nake tattaunawa da su, waɗanda kuma sun fi ni ilmi da gogewa a aikin gwamnati, ita ce ta rashin kuzari da Shugaban Ƙasa yake nunawa wajen amfani da madafun ikon da tsarin mulki ya ba shi ta hanyar da za su dace da cimma manufofinsa. In kuwa bai yi haka ba, ya ci gaba da dogaro da kansa, mutane da yawa suna hangen cewa ba zai cimma burinsa da na masoyansa yadda ya kamata ba.
A ko yaushe ana nuni da yadda shekara ɗaya bayan zaɓensa, har yanzu bai canza shugabannin ma’aikatu masu muhimmanci da yawa ba. Har yanzu suna ƙarƙashin mutanen da waccar gwamnati ne suka naɗa su. Kuma daga muƙaman da ya naɗa, in ka cire kaɗan irin na Yaya Hamid Ali da Janar Burutai, ba wasu masu yawa waɗanda naɗinsu ya gamu da maraba mai yawa a cikin jama’a. Da yawa dai ba yabo ba fallasa ne, wasu kuwa sai dai mu yi gum don bakinmu da goro.
Tsammaninmu a da shi ne zai zaƙulo mana irin su Hamid Ali da Burutai kamar ɗari biyu waɗanda ya jima da sanin halinsu a soja da muƙamai dabam dabam da ya riƙe, da kuma a cikin gwagwarmayar siyasar da ya yi na tsawon shekaru goma sha hudu. Hakaza kuma ya nemo matasa masu jini a jika da za su gudanar da manufofinsa cikin tsarin zamani na ilmi, hikima da dacewa. Mun ɗauka zai yi wannan duk da yanayin siyasar gambizar da ta kawo shi mulki.
Waɗannan gwaraje su muke sa rai, a da ɗin, za su zo su hautsuna tungar azzalumai, duk ɓerayen da suka yi ta sace mana dukiya su yi ta neman wurin ɓuya, waɗanda kuma suke da niyya su ji tsoro su daina. Irinmu masu surutu kuma mu ja daga a jaridu da sauran kafofin sadarwa mu yi ta fallasa su, da zuga a rubuce-rubucenmu har sai ɓerayen nan sun rasa wurin shiga, sun bayyana, an kame kowanne an buge, ya mutu har abada, a huta da mugun iri. Da zatonmu ke nan tun 2002. Ai ka ga da aka dace, su Janar Burutai da Magu da Yaya Hamid Ali lallai sun cika ƴaƴa. Sun kawo wa Yaya Buhari nasara a fannoninsu. Allah ya saka musu da alheri.
Amma ba a yi nisa ba har dattijai sun fara kokawa da wasu da ke kewaye da shi, suna zargin cewa ƴan cin hanci ne, kamar yadda Farfesa Ango Abdullahi ya yi bayani kwanaki. (Professor Ango kuwa ba yaro ba ne. Farfesa ne kuma Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello tun muna ɗalibai na digirin farko. Don haka ya san abinda yake faɗa.) Ana kuma cewa waɗannan sune suke yin lis ɗin ɗaruruwan mutane da ake baiwa shugabancin ma’aikatu a yanzu. In an bari haka ta ci gaba, to kar a koka da talaka don talaka ya yi nasa da ya danne yunwar cikinsa ya zaɓi canji. A kuka da shugaba.
Muna fata Shugaban Ƙasa zai saurara ya yi gyare-gyaren da suka kamata don ya yi aikinsa yadda ya kamata. Shi ne kanmu, shi aka baiwa wuka da nama, shi ne mai cikakken iko. Shi ne kuma za a fi kokawa da shi in ba a cimma buri cikakke ba.
A karshe babban abinda za mu taimaka ma Yaya Buhari da shi abu biyu ne: faɗa masa gaskiya da yi masa addu’a ta alheri. Ƙin faɗawa shugaba gaskiya saboda kwaɗayi ko soyayya sharri ne babba da ke cutar da shi kuma alama ce ta raunin zuciya. Allah ka tsare mu.
Za mu ci gaba da gaya wa mulki gaskiya, kamar yadda muka yi wa shugabannin baya tun 1999. Amma a matsayinsa na amininmu, dan’uwanmu kuma shugabanmu, yi wa Yaya Buhari addu’a ya zama dole ga dukkan mai hankali a cikin mu don in gida bai kwana lafiya ba, runji ma ba zai kwana lafiya ba.
18 Afrilu, 2016

No comments:

Post a Comment