Thursday, January 18, 2018

Kanawa! Ku Dauki Halinmu

Yau Kamar shekara 42 ke nan da na fara zuwa Kano. Har yau, ba garin da in na tinkare shi nake jin dadi da annashuwa kafin in shige shi, da yayin da nake cikinsa, kuma nake kewar fitowa barin sa kamar Kano.
A Kano na samu Nairata ta farko bayan na yi fatali da allin jami'a a 1993. A nan nake da manyan abokai wadanda ba zan mance da su ba. A nan nake da masoya rubutu na da mutanen da na dauka malamaina ne a wasu fannuka. Har lambar yabo (award) sun ba ni. Duk sati ina huldar kasuwanci da Kano, su ba ni, na ba su. Kai, in takaita maka magana, uwargidata bakanuwar cikin gamuwa ce, 'yar Daneji. Yanzu ma ta miko min kosai, wai in ci, da dadi. Na ce, to.
Ban fid da rai ba, watarana zan yi gida a Kano don wannan bakanuwar ta ba ni yaya biyar, hudu na raye. (Na farkon talaucin jami'a ya kashe shi)
Kai, in na ci gaba da magana, sai in tashi daga bazazzagi in ce ni Bakano ne.
Na karanta abinda malamina kuma jagabanmu na masu sharhin Hausa a Facebook ya rubuta game da Kanawa. Na kuma karanta rashin jin dadi da Kanawa suka nuna a kan haka. Ni an sa ni a tsaka mai wuya: cikin biyun wa zan goya wa baya? Masoyana da surukaina a wannan hannun, ko kuwa malamina da ke daya hannun? In soyayya ta motsa sai ta ce min canki Kanawa, in zazzaganci ya motsa ya ce canki malam.
Na so da a ce duk abin an yi shi cikin raha ya wuce. To amma zukata sun motsa. In da cikin raha ne da sai in ce wa Dr. kuma Malam Sheriff Almuhajir ya kara da cewa Kanawa gwanayen sace motar baki ne. Sun sace ta yarona, ba su san dara ta ci gida ba ne. Yaron da suka dauke wa motar, dansu ne. Na ce masa, "Oho. Danginka ne suka koya maka hankali."
Na zo Kano da motoci biyu bayan nan. Kuma a kowane karo, sai da suka gwada sace su. Daya, a kasuwar yan gwangwan ta Kingsway, daya kuwa ina cin abinci a Sultan Restaurant. Amma kun san kurwar bazazzagi ba wasa ba ce. Suka kasa. Zaria birnin ilimi. Yaro ka zo a baka lak'ani.
Kuma wani abin takaici da Kanawa, malam, duk da kirarin kudin da ake musu - mai mata mai mota, sun ba ni mata amma sun kasa tara wa yaron nan kudi ya sai wata motar. Ashe Shata ma bai san motocin zagezage suke sacewa ba, su canza fenti, su ce na su ne.
Kan da a Barno na ce an sace min mota, to da tuni sun ba ni sabuwa. Sai dai su kuma, daga take-takensu na bayinmu, suna iya sace min mata.
Shi ya sa nake son Zazzau - mai rimi mai Shehu. Ba satar mota, ba satar mata. Sai ba da ilimi kullum safiya. Ina ma da Kanawa za su dauki halinmu?
Kanawa, ku yi kirsimeti lafiya.
Dr. Aliyu U. Tilde
25/12/2016

No comments:

Post a Comment