Thursday, January 18, 2018

Kwankwaso: Garkuwar Arewa

Kafafen watsa labaru na waje sun ruwaito ziyarar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai jiya garin Ile-Ife tare da jakadan kasar Nijer a Nigeria don jajantawa Hausawa wadanda rikicin satin da ya wuce ya shafa. Mu ma muna mika jajenmu gare su.
Wannan ba shi ne karo na farko da Sanatan yake jefa kansa cikin ayyukan taimako ga tsirarun al'ummunmu wadanda ake zalunta a kudancin Nijeriya ba. Kan ba a mance ba - dan'adam kuwa mai saurin mantuwa ne - ya kai irin wannan ziyara lokacin da aka yi fada a Mile 12 har ya taimaka da karbo belin yaranmu da aka tsare bayan taimako na kudi da ya bayar.
Yabon gwani ya zama dole. Kwankwaso - kamar yadda muka saba kiransa - yana cikin manyan Arewa kalilan wadanda za su iya fitowa su danganta kansu da mutanensu a cikin halin rikici. Akasarinmu mun gwammce mu yi shiru mu yi ta sambatu a boye ko dak'uwa cikin duhu wai don kar daya bangaren su zarge mu da kabilanci, miyarmu ta siyasa ko mukami ta baci. An sha a yi rikici a zalunce mu, mafi yawa ko tari ba sa iya yi.
Ga dukkan alamu Kwankwaso bai damu da irin wadannan zarge-zarge ba duk da cewa shi dan siyasa ne. Haka ake son namiji. Ina fata zai ci gaba da wannan hali nasa mai matukar kyau har ma ya jawo wasu manyan cikin wannan kokari. Abin da Arewa ta ke nema ke nan tun shekaru don mutanenta su fita maraici.
Kan da ina da iko, da na nada shi "Garkuwar Arewa." Ina fata wadanda suke da wannan halin za su yi masa wannan karimcin. A wannan shafin nawa, ni kam na ba shi. Saura su dada masa.
Dr. Aliyu U. Tilde
15/3/17

No comments:

Post a Comment