Saturday, January 20, 2018

Na Ga Malam Adamu Adamu, Ministan Ilmi

Alhamdulillahi jiya, na k'uk'uta, na je takanas-ta-Kano na kai wa yayana Malam Adamu Adamu ziyara a Abuja don mika masa wasu shawarwari da koke-koke da suka shafi gudanar da ilmi a Nijeriya.
Tattaunawarmu ta shafi matakan ilmi mai zurfi da na sakandare, tunda da su na fi sabawa. Babbar shawara ita ce a yi kokari a hanzarta zamanartar da koyarwa a manyan makarantu.
Wannan zai bukaci amfani da hanyar sadarwar zamani a komi ta yadda bayanai za su wanzu a tafukan dalibai da malamansu ba tare da tikar wahala irin wacce muka sha ba a zamaninmu. Yin haka zai warware matsaloli da yawa ya kuma kai ilmin matsayi guda da na sauran duniya. Amma fa sai an sha tanadi da aiki a kan malaman manyan makarantu duka, da sauran ma'aikatan jami'a, da dukkanin dalibansu, da dakunan karatu, da sauransu. Zamanin da malamin jami'a ko dalibinsa zai zauna bai iya komputa ko mallakarta ba ya wuce in gaskiya ake so.
Kamar sauran shawarwarin da na bayar, musamman kan tsarin jarrabawa da tsarin ilmin bai daya, da daidaituwar kalandar karatu, da ASUU, da tsaida karatun zuk'u da ake yi a matakin firamare da sakandare, duk su na kan turbar shirye shiryen da ma'aikatar ta ke haramar yi. Tafiya ce ta tadda mu je mu. Na yi farin ciki kwarai. Allah ya taimaka masa.
Na gaya masa musamman alkawarin da na dauka a nan Facebook, na cewa za a warware matsalar cunkoso a azuzuwan manyan makarantunmu, har na nuna masa hoton da aka buga na wani dakin karatu a ATBU wanda ya cika makil har da mata zamne a kasa da kuma yadda dalibai suke faduwa su some a ABU da UNIMAID a lokuta da yawa. Na nuna masa hanyar da za a warware wannan matsala cikin ruwan sauki. Na jaddada masa cewa alkawari ne na dauka kuma zan matsa masa sai na ga an cinma buri in sha Allah.
Na kuma dan kewaya gari don saduwa da wasu abokan don jin tsegumi na abin da ke gudana a karkashin kasa. Alhamdulillahi kowa na yi wa shugaban kasa kyakkaywan zato. Sai dai ya na bukatar addu'a Allah ya dafa masa, ya kara masa basira, da kare shi daga kwazazzabai da ramukan da a kullum ake gina wa masu mulki. Duk shukar da za a masa, Allah ya sare masa ita. Duk jifar da za a masa, Allah ya kare ta.
Wannan fatan, shi ne babban gudummawa ta kowane dan Nijeriya ke nan a yanzu. Ko ka yi Buhari ko ba ka yi shi ba, yau shi ne shugaba, halin rayuwarmu ta ta'allaka da taimakon da Allah zai ba shi. Sai gida ya zauna lafiya ba, runji zai zauna lafiya.
Dr. Aliyu U. Tilde
19 February, 2016

No comments:

Post a Comment