Saturday, January 20, 2018

NASIHA GA BUHARI (II)

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
IKO TUSHEN MULKI
39. A bayan nai batu kan tsoratarwa
Da horo kan batun ranar tsayawa
40. Ina son in taɓo tushe na mulki
Da ba shi babu mulki mai daɗewa.
41. Cikin manyan sifofi ba kamarsa
A nassi na gani ba na musawa
42. Fa mulki ba ya ƙarko sai da iko
Ya zamto shugaba zai sa cikawa.
43. Umarni in ya bayar za a ida
Ba zai zam sakare fanko na yarwa.
44. Dalili: ko da yaushe can Kitabi
Sifar mulki da iko ke tahowa.
45. Idan mulki ya zamto babu iko
Da reni za ya ƙare ba jimawa.
46. Mashawarta, ministoci, asistan
“Civil Servants” su zam ba sa kulawa.
47. Dasisa kowace sai sun kitsata
Su zartar tunda sarki bai tsayawa.
48. Jaridu, rediyo, sauran kafofi
Na sadarwa “scandal” ba ƙidawa.
49. Haƙiƙa dole sai an zage dantse
Gama wannan hali na nan ga kowa.
50. Sanin da can hukuma an watanda
Da holewa kurum ba tsawatarwa.
51. Bare kuma shugaba ya zam yana yi
Yana doka yana ɗan gyangyaɗawa.
52. Kamar ya ba da dama kulla nafsin
Ta barci har ta minsharin nutsawa.
53. Hakan nan in ya zam shi ba ya sata
Ido nai za a kiwo don ɓatarwa
54. Kirari, dariya duk za a ba shi
A kullum don ya rafke ai bajewa.
55. Mashawarta, wazirai kowanensu
Ga duk furcinsa: haƙƙun za su cewa.
56. Fa ko ƙarya ya shirga sai su rantse
Su ce: nassi sahihi ba musawa.
57. Idan ko gaskiya ce sai a ɓoye
A kange har ya zam ba ya jiyawa.
58. Abubba za ya zam bai san da su ba
Kafa duk za su toshe ba isowa.
59. Da ya zam yartsana sai sarrafawa
A kullum sai a sata ba tsayawa.
60. Abun ɓoye da sannu sai ya watsu
Na ƙas kowa ya zam mai ɓarnatarwa.
61. Abubba su huɗu ke kai ga wannan
Ka saurara na jera don sanarwa.
62. Na farko in ka ɗau babban muƙami
Maha’inci ya karɓa yai riƙewa.
63. Ka san ba yadda za kai don ya canza
Tabi’a na jini ba ta gushewa.
64. Da fayil ya taho kan teburinsa
Ka san in ba kuɗi ba ya wucewa.
65. Kaza in dogari ne shi a fada
Kuɗaɗe za ya karɓa kan isarwa.
66. Idan ya kai iyaka gun riƙarsa
Da sunan mai gidan zanka cewa.
67. Na biu ne shugaba in bai da horo
A saɓa mai ya zam bai tsawatarwa.
68. Mutum ne zai yi laifi sai ya kyale
A kan so ko sanayya ba ya cewa –
69. A korai, sai ya sake babu kunya
Gadara shugaba bai horataswa.
70. Rashin horo yana cutar da mulki
Ya zare mai laka yai laulayewa.
71. Rashin horo a mulki bai yi kyau ba
Alama ce ta bawa mai gazawa.
72. A tarihin ƙasar sam ba kamatai
A mulki ba ya shi gun raunanawa.
73. Idan horo ya kama maimakonsa
A dau kyauta da niyyar lallabawa
74. Irin wannan yana cutar da mulki
Abu Tayyib ya ce sai ai kulawa.
75. Ukun sai shugaba in bai da himma
Idan ya sa hannu bai bibiyawa.
76. Ana iya canza komai ko a danne
Ana aiki da kurdi mai sayewa.
77. A nan tilas ya zam na ma kashedi
Ka miƙe kar ka zam ba ka kulawa.
78. Ka ɗau hali na wancan jarumina
Abu Hafsin Umar mai bincikawa.
79. Umar in yai umarni za ya bi shi
Ya san ba jami’i mai dakatarwa.
80. Huɗun kau dole ne tantance komai
Gabanin sa hannu don tabbatarwa.
81. A nan ne wajibi samun gwaraje
Su dudduba gabanin rattabawa.
82. Kwararru ne da saurin yin karatu
Da kwalwa mai kusan tai walƙiyawa.
83. Кwararru ne da ilmi har fasaha
Amintattu da ba halin gazawa.
84. Idan ba su fa aikin zai yi cikas
Abubba duk su cushe ba sakewa.
85. Huɗunnan naka ne in ka kiyaye
Gaba ɗai kai riƙo ba ɗai na yarwa:
86. Maha’inta ka kore, kai ta horo
Da himmar bibiya, sai tabbatarwa.
87. Huɗunnan tabbaci ne babu shakka
Ga dukkan shugaba mai son hayewa.
88. Ta’ala nai kira domin Rasulu
Gare ka ya agaji yai taimakawa.
89. Dawaman yai aminci har da tsira
Musamman kan fiyayyen annabawa.
Tammat bi hamdillah
3 March, 2016
______________________
Sashi na uku zai fito gobe ko jibi in sha Allah

No comments:

Post a Comment