Saturday, January 20, 2018

WAKAR ZABEN NAGARI

On my way back home from my BBC interview on my poem, Zaman Lafiya, last Friday, the composition of a second poem, Zaben Nagari, occured to me. As soon as I dropped my bag, I sat down to write its 110 verses that evening. The following morning, yesterday, I edited it and started to share it on Whatsapp. The review, mashaallah, was superb. Today, I humbly present the little contribution to my Facebook readers. The audio will follow shortly.
WAKAR ZABEN NAGARI
Ta
Dr. Aliyu U. Tilde
1. Bisimilla nai shirin waka
Bisa zaben mutum nagari
2. Allah ka taya mani Rabbi
Ka ban hikima kamar bahari.
3. Ya zan duk san da zan waka
Baiti su zubo kamar mad'ari.
4. Idan kuwa za ni rerata
Murya tai dad'i tana sihiri.
5. Da salati gun nabiyyina
Muhammadu Sayyidil bashari.
6. Da ‘ya’yanai da ahlunai
Da matanai da ke k'abari.
7. Da sahibinai sadiqinai
Uban A’i Abubakari.
8. Sannan ga Ummarul Faruq
Da ke adalci cikin lamari.
9. Ga Usumanu Zin Nurayn
Dattijo guda kamarmu dari.
10. Bare Ali da ke ahali, na
Batulu gwarzo a ran badari.
11. Jama'a ga lokacin zabe
Kasa kowa yana hadari.
12. Mu dai fatarmu ko yaushe
Allah, ka ba mutum nagari.
13. Kullum ko idan muna kuka:
Manya muna cikin hadari.
14. Sai manya su gyara muryarsu
Su ce: To ai muna nazari.
15. Aaf, ku daina ce nazari
Ciki makil da cin ushuri.
16. Kullum ba za ku gane ba
kun ci haram dubu da dari.
17. Ku bar karyar kuna nazari
Sai dai kyamar mutum nagari.
18. Da kaz zaka kac ci hakkinmu
Nakiri bugai ka sa mai mari.
19. Mu kam ba za mu yafe ba
Kun sa kasa cikin hadari.
20. Kwakwalwar sai ka ce ba’u
Jiki ko kamar na alfadari.
21. Kana takama da alfahari
Ka bar jama’a cikin fak’ari.
22. To ga ka ka bar duniya, yau
An kawo anka yar k'abari.
23. Walakiri kara jibga tai, RAM,
Kulki, sai ya nitse Sak’ari.
24. Zamna sha wuyarka a can
Nakiri ba ya jin hakuri
25. Ku tuba kudaina satan nan
Ku zan hali irin nagari.
26. Jama’a zanka yin darasi
kullum mu zanka yin guzuri.
27. Muma jama’a da sauranmu
Don ko sam ba mu son nagari.
28. Duk mai kirki idan ya zaka
Sai mu ce: wai akwai guzuri?
29. Kai dad’a ji mu shashashu
Yanci mun zub da shi da wuri.
30. Ran zabe har da ganyen mu
Mu zan ka fadin ina maiwuri?
31. Kai, dad'a ka ji mu shashashu
Mun sa yanci cikin had'ari.
32. Jama’a mu canza halinmu
A gun zabe mu dau nagari.
33. Shin wa ye mutum nagari?
Ga zance zan yi kan lamari.
34. Ko yaushe ka bai amanarka
Bai b'adda sulenka ko kadari.
35. Izan ko ya yi alkawari
Tabbas shi zai cika dawuri.
36. Idan ya hau bisa mulki kau
Zai yo aiki kamar Umari.
37. Mutum mai gaskiya ke nan
Sannan kau ga shi mai hakuri.
38. Halinsa kadan na kawo ma
A gida nai ko yana safari.
39. Hakan yake ba ya canzawa
Sa shi a rana ko k'amari.
40. Ya Allah ka shirye mu, don
Muhammadu Sayyidil bashari.
41. Mulki Allah ka ba da shiya
Haka, tun farko na ad-dahari.
42. Hakan kuma Shi yake kwata
Musamman gun mutan garari.
43. Kadiru ka kwace mulkinsu
Ka ba bawa irin nagari.
44. Dukkan kasa da tac ci gaba
Ka san zabe ake nagari.
45. Amerika sun yi yo zabe
Amma zabe sukai nagari.
46. Russia hada da New Zealand
Nan ma zabe akai nagari.
47. Bar Ingila in sukai zabe
Tabbas, zabe suke nagari.
48. Jamus, Faransa har da Holland
Kowa zabe ya ke nagari.
49. Bare kuma India babba
Da Pakistan cikin nagari.
50. Ga kasashen Afrikanmu
Su ma zabe suke nagari.
51. Nijer, Mali da Ghana kaza
Duk sun zabe irin nagari.
52. Amma banda Nijeriya, Ma-
gudi mukai muna fahari.
53. Handama, kwadai na naira ne
Biyun sun dakushe nagari.
54. To ni kam Allah nake roko
Kasa INEC suzan nagari.
55. Kaza Sojoji da yansanda
Rahman: sauya su zan nagari.
56. S.S.S. ma da joji duka
Allah kasa su zan nagari.
57. Wanda duk yac ci zalinmu
Allah, batai dukkan lamari.
58. Na baya su cinye pansho nai
Ya zan hauka da ba wak’ari.
59. Ulcer, B.P. su kama shi
H.I.V, ciwo uban hadari.
60. Duniya kowa ya kyale shi
Yazo mutuwa cikin khamuri.
61. Gawa tai mu ba karnai
Sui warwaso suna garari.
62. Jama’a, kuce da ni amin
Amin amin cikin wutiri.
63. Ka canza halinsu, Ya Rabbi
Har ma su so mutum nagari.
64. Talakawa ma kacanza mu
Mu so mutum irin nagari.
65. Duk wanda kau yak ki canzawa
Jefa Narinka mai Sak’ari.
66. Halin gafiya garesu duka
Ko yaushe ba su yin shukuri.
67. Tabbas ga mu kan usuri
Rahman biyo da mu yusuri.
68. Rayuwa ta zanka yin sauki
A nan kauye da can haDari.
69. Ka sanya mu son gaskiya
Mu sha ta har mu kai sakari.
70. Munga Haza mun yi alkawari
Ya Rabbi, za mu yin nagari.
71. Jama’a duk ma su yin zabe
Za mui hali guda nagari?
72. (E!!!) Za mui hali irin nagari
Aliyu mun yi alkawari.
73. Mutanen Tilde sun ce man
Za sui zaben mutum nagari.
74. Jos Kwata ma ta yamma da mu
Sun ce mun sai mutum nagari.
75. Zariya sun taho tarya, ku-
ri'arsu za su ba mutum nagari.
76. Funtua, Gusau, Mafara sun
ce mun zabenmu sai nagari.
77. Bare kuwa Sokoton Shehu
Tun asali suna nagari.
78. Argungu, sannan mu zo Gwandu
Da Jega da Koko har Yauri.
79. Dakkarawan Zuru ma nagari
Kwantagoran ma suna nagari.
80. Bidda, Minna duk Nufawa ne
Kewano masu son nagari.
81. Bare na Kaduna har Katsina
Da Daura can akai nagari.
82. Kazaure garin aminina
Da Kano city suna nagari.
83. Hadejiya Dutse har Azare
Jama’are, Misau suna nagari.
84. Pataskumo Yobe zan sabka
Suma in ce: ku na nagari?
85. (E!!!) Kuwa du Muna nagari, don
Muhammadu Sayyidil Bashari.
86. Na Shehu Yerwa Maiduguri
Barnawa: shin kuna nagari?
87. Suka ce mun munga haza ai
Ali, kowa yana nagari.
88. Yola, Taraba, Gombe duka
Dangina za su wo nagari.
89. Bauchi ko an yi tushenta, a
Kasa a tsare muna nagari.
90. Nasarawa har Abuja Ben-
ue Kogi, da Kwara duk nagari.
91. Yarbawa ba munafurci
Sun ce sun dauki alkawari.
92. Inyamurai ku san cewa
Canji na nan tafe a gari.
93. Ku yiyo taro mu dafa mai
Mutum, kwaya guda nagari.
94. Shin wa ye mutum nagari?
Shi ne wanda ba shi son ushuri.
95. Bai cin hanci da yin sab’o
Bare zulmu da yin dakhari.
96. Kira Najeriyarmu duka
Mu zan zaben mutum nagari.
97. Shugaba, Kansila hakaza
Mu mai kuri’a muna fakhari.
98. Aminci zaya dawo mana
Da amana babu ‘yan bidiri.
99. Mui hobbasa a ran zabe
Mui samko da alfijiri.
100. Muje mu mika katinmu, ku-
ri’a, mu ba mutum nagari.
101. Sai mui dako a gun zabe, da
Tsare ta kamar muna badari.
102. Mu zan rakiya wajen taro
Hana mugu yin bakin kuduri.
103. Amma komai cikin ladabi
Ba cin fuska bare darari.
104. In an ce ga wanda yac ci,
ladab, ko za mu dau k’adari.
105. Nasihata da zan ke nan
Allahu zabam abun khairi.
106. Tammat, na tike ta a nan
Baiti ashara a kan na dari.
107. Ga talifi na almajiri
Na mutan Tilde maso nagari.
108. Sunansa Aliyu 'Danmama'
Kanin Iro uban Jaafari.
109. Ya Rabbi jikan iyayenai
Malam, da wanda ke zikiri.
110. Da Salati gun Nabiyyullah
Muhammadu Sayyidil Bashari.
Alhamudulillah.
20 December 2014
Picture: The composer of the poem with Malam Dahiru Jahun OFR, one of the most prolific poets in Northern Nigeria, when they met few minutes ago in Bauchi.

No comments:

Post a Comment