Thursday, January 18, 2018

Yaki Da Akidar Ilhadi A Kasar Hausa

Keanakin nan ana kokawa da yaduwar akidar ilhadi tsakanin yan boko.
Ga wani karamin sharhi da na yi a kan wannan maudu'i a shafin Dr. Sheriff Almuhajir:
"Idan zan yi takaitaccen tsokaci na nawa gwagwarmaya da ilhadi sai in fara da cewa wannan ba dabon abu ba ne. A 1984, akwai abokin aikina lokacin da muke koyarwa a jami'a da ya ce mu lokacin da yake NYSC, ran 24 ga watan Disamba, 1983, ya gane cewa ba Allah! Musulmi ne kuma tare muke koyarwa a sashin ilmin halittu a lokacin. Ban yi mamaki ba don a lolacin shi dan gani kashe nin akidar gurguzu (communism) ne. Amma alhamdulillahi. Da ya kara shekaru ya dawo da imaninsa har yana hamsus salawati yanzu.
Ni kuwa, ilmin halitta da Qur'ani su suka kare ni daga tunanin cewa ba Allah kwata kwata. Saboda asalin karatuna na boko a sashin kimiyyar halittu ne kuma wannan akidar ta yi katutu a ciki. Amma sanin yadda "complexity" na kirar halittu (hadi da sammai da kasa da dukkan hakittu masu rai) yake da rayuwarsu ya ba ni yakini a karshe cewa akwai Mahalicci. Ina ga har na rubuta littafi a kai a 1984 wani abokin abokina ya lallaba ya salwantar da shi. Da yake a lokacin babu personal computer da tapareta muke aiki, sai na yo mawa wajen rubuta wani.
Na biyu shi ne Qur'ani. Haddace Qur'ani da fahimtar mu'jizojin da ke cikinsa, musamman lissafin surorinsa, da ayoyinsa da haruffansa ya ba ni yakini cewa ya fi karfin dan adam ya kirkiro shi. A nan ilmin kimiyya da uslubinsa ya taimaka min sosai.
Alhamdulillah. Ba don samun yakini kan wadannan abubuwa biyu ba, wallahi da tuntuni na bar shaanin addini gaba dayansa na yi zamana haka kawai.
Don haka ina godewa Allah kan abu uku:
1) Haihuwata da aka yi ga uba wanda ba abinda yake girmamawa a rayuwa fiye da addini, duk da yana baiwa ilminmu na boko nasa muhimmancin, yadda har nagama shekarun firamare bakwai bai bari na yi fashin zuwa makaranta ba ko sau daya, haka ma makarantar Allo har na sauke na tafi sakandare.
2) Karanta kimiyya. Wannan ya bude idanu ga sanin halittu kamar yadda yake dawwane a littattafan zamani ilmin halittu da ilmin fiziya.
3) Karatun Qur'ani da saurara wa manyan malamai a kan ma'anoninsa, musamman irinsu marigayi Sheikh Mutawalli Al-Shaarawi (R). Gaskata shi da abinda kimiyya ta gano a yau ya taimaka mun wajen karfafa imanina a kan saukakke ne.
Don haka ina ganin yakamata in ana son a yaki yaduwar ilhadi, dole a yi wadannan abubuwa hudu:
1) Tarbiyyartar da 'ya'ya bisa addini da nuna musu - a aikace - cewa ba abinda ya fi shi.
2) Sanin hujjoji na Qur'ani a kan matsaloli na imani guda uku: Na samuwa da kadaitar Allah, na annabta, da na hisabi. Wadannan, a fahimtata, sune mas'aloli da Qur'ani yai ta faman warwarewa a Macca. Duk tambayar da kafirai suka yi wa Annabi a kan ukun nan ne. Ba su da na hudu! Wannan ma na taba yin dogon rubutu a kai a 1986, ina ji.
3) Sanin ilmin halitta ta sammai da kasa da abubuwa masu rai duk - kamar yadda Qur'ani ya nuna - yana da muhimmanci wajen tabbatar da imanin musulmi. Don haka karatunsu da wayar wa mutane hankali a kansu a yau kusan ya zama wajibi don kaucewa ilhadi.
4) Rage shagaltar malamai da abubuwan da ke ragewa yara son musulunci kamar su rarrabe rarrabe, da kuma akidun da aka tabbatar suna kaiwa ga ta'addanci da sauran abubuwan kyama a wannan zamanin. Dole a mai da hankali wajen yin waazi dai dai da zamani in ana son yanboko su dawwama bisa musulunci ba tare da gardama. A sani duniya gaba take tafiya. Jiya ba za ta taba dawowa ba.
Fahimtata ke nan. Allahu aalamu. Wasslamu alalikum.
Dr. Aliyu U. Tilde

No comments:

Post a Comment