Sunday, January 21, 2018

Yanfashi a Kasar Hausa

Na jira cikin dare har na yi barci ban ji dirin babbar motar da ta kai
yoghurt Kano da sauran garuruwa ta dawo ba. Yakamata a ce ta iso wajen
karfe 12 na dare tunda mun yi waya da magariba suna shirin barin
Kano.
Da safe sai na kira na tambaya ko lafiya? Sai yara suka ce mun lafiya.
Barayi ne suka datse hanya kafin gadar Wudil na tsawon lokaci jiya
bayan lisha. Ganin haka, da kuma da ma barci shi ma yana neman
satarsu, sai suka juya Kano suka kwana.
Mu da muke sashin Arewa-maso-Gabas da Arewa-ta-Tsakiya, sau da yawa, a
da, mukan yi mamakin jin barayi na fashi a manyan hanyoyin Arewa-maso-Yamma saboda dalilai uku.
Na daya dai ba su da dazuka irin namu ta
yadda dan fashi zai bace cikinsu kafin ka ce kwabo. Tabarkallah, a Kasar
Hausa, duk inda ka duba filin gona ne a gefen hanya ya tafi har iyakar ganinka. Da rani kuwa filin Allah ta'ala ne kawai a shimfide. Sau nawa nake shiga motata in
mata kik, ta tashi, daga Zaria mu doshi Sakwwato cikin dare, ko Argungu
mu isa da Asuba, ba ma tsoron komai sai dai na bacin motar? Sau nawa zan
bar Sakkwato da Magariba in nufi Jos, ko bauchi, balle kuma Zaria ko Kaduna ba tare da tababa ba?
Mu kuwa a gurarenmu akwai dazukan da kai kanka in kana tuki a cikinsu,
ka san sai kiyayewar Ubangiji. In ka bar Kano, kana shiga dajin
Falgore ka san addu'a ta kama ka har ka iso Jos; haka in ka bar Bauchi
za ka je Yola; Ko Gombe za ka Maiduguri; Ko Yola zuwa Jalingo; Ko Jos
za ka Abuja, balle kuma a ce ka nufi Makurdi ko Ilorin. Ko wannan motar da ta
fita zuwa Abuja a zangonta na farko cikin zagayenta na sai da Yoghurt,
ai sun iske motoci sun tsaya cirko-cirko tsakanin Barde da Keffi suna
jiran yan fashi su bude hanya. Wannan bai bani mamaki ba, don kuwa na
san a rina. Amma Wudil? Haba jama'a!
Na biyu, Arewa-maso-Yamma bata da yawan kabilu kamar sauran Arewa. A
shekarun baya, na aza musulmi ba zai taba aikata mummunan laifi kamar
fashi ba. Hasali ma, fashi muna ganin kawai 'yankudu ne suke
yinsa, musamman Inyamurai da rikakkun Yarbawa irin shegun Legas din nan.
Amma a samu bahaushe, ko bafilatani, ko Kanuri yana fashi ai abu ne da
wallahi ba mu taba zata za mu ganshi a rayuwarmu ba. Kai in ma za a
samu a Arewa, kila sai dai cikin kananan kabilunmu wanda addinin
kirista bai ratsa jikinsu ba.
Amma ina? A kwana a tashi, sai ga nesa ta zo kusa. Ba kabilu ba kawai,
ba kuma cikin yan iskan mazauna birni ba, fashi da makami har ya zama
al'ada cikin mutanen daji, Filani da ko kadan ba a sansu da aikata
abun kunya ba balle muggan laifuka irin wannan. Inji wani mawaki,
"karyar wa'de-wa'de ta kare ga dan Filani na sai da giya." A lokacin
nan giya ce abun mamaki a ga bafillace na yi; a yau, har fashi ya shiga yi. Yan'uwansu
Hausawa su ma sun sa kai. Sau da yawa ka ji kauyawa sun datse
hantse hanya tsakanin Takai da Wudil, ko tsakanin Wudil da Kano, ko
tsakanin Gusau da Mafara. Abun ba a cewa komai.
Abu na karshe, shi ne Arewa maso Yamma sun fi koina yawan jama'a
cikin Arewa. Tunda garuruwansu na da girma kuma kauyukansu kusa suke
da juna, sun fi sauran gurare samun daman kawo dauki da saukin kama
masu laifi. Ashe ba a nan take ba. Abun ya zama ruwan dare gama
duniya. Kuma tunda maza sun zama mata kuma ba mai niyyar kai wa
danuwansa dauki, yan fashi hatta a Arewa-maso-Yamma sa ci karensu ba
babbaka.
Amma duk wannan damuwar ta zamanin yanzu ne kawai. In an duba tarihi
kafin zuwan turawa, ai nan ne ma yanfashi suke sheke ayarsu. A wani
fannin ma, gara yanfashin yanzu. A da, kusan kowane daji a kasar Hausa
cike ya ke da yanfashi. Za su tsare matafiya, su wawashe musu dukiya,
kuma a lokuta da yawa su mai da su bayi. Yanfashin wancan lokacin sun
rika, don har tawagar sarakuna suke hanawa sakat. Akwai shekarar da a
zamanin Sarkin Musulmi, Abdu Danyen Kasko, lokacin hukumar daular
Sakkwato ta yi rauni, tawagar kyautar shekara-shekara ta sarakunan
gabas ta kasa tafiya Sokoto saboda tsoron zaratan yanfashi da ke cikin
dajin Rugu da sauran dazukan da ke hanyar Sakkwato. A lokacin, dajin na da yawa sosai don Shehu Abdullahin
Gwandu da tawagar mutum biyar da suka bar Sakkwato da niyyar
komawa Madina sai da suka yi tafiyar sati biyu a ciki ba mahalukin da
suka gamu da shi banda giwaye da sauran namun daji.
A yau ma hukunci ya yi rauni shi ya sa fashi ya dawo kasar Hausa. Ba a
hukunta mai laifi. Yoto wa zai hukunta shi, bayan mahakuntan kansu
barayi ne, ko mu ce gaggan yanfashi ne su ma? A zamanin turawa kuwa
zuwa lokacin su Sardauna, hukuma na da karfi. Dandoka daya kawai ake
da shi a gari amma tsit ka ke ji. Mai lafi kuwa, ko ya shiga daji,
dandokan nan shi kadai, ko dogarin sarki, zai zakulo shi. Allah sarki.
Jiya ba yau ba. Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba.
To ba yanda muka iya. Tafiya dai ba za mu daina ta ba. Ba mahalukin da
zai hana mu walawa da neman halal. Ga bankuna nan sun sauwake
al'amurra. Ta hanyar waya sai ka yi tiransifa na kudi zuwa abokin
huldarka a gari mai nisa, ba tare da ka dau miliyoyi a bayan mota ba.
Nan gaba kadan, na'urar POS za ta wadata. Duk wanda ya sayi hajarka ba
sai ya biya nakadan ba. Sai kawai ya sulluba katin ATM dinsa a jiki,
kudin su shiga ba tare da wuri na gugan wuri ba. Yanfashi sai dai su
kare da karbar wayoyin matafiya da dan canjin da ke aljihunsu. Wayoyin
su ma kwanannan za su zama hadari a hannun yanfashin don kuwa in
kowace waya aka sa mata 'bi sawu', watau tracker, to za ta tseguntawa
mai ita inda ta ke, wuf sai jami'an tsaro su diran ma danfashin. Daga
nan su yanfashin za su gane ba riba a harkar ta su. Kafin a jima sai
su bar harkar tunda dai don lada ake salla.
Allah ya dawo mana da aminci a Arewa da sauran Najeriya baki daya.
Abun da ya rage shi ne kowa sai ya dau matakan tsaro da kiyayewa.
Matafiya, a dawo lafiya.
21 Satumba, 2013

No comments:

Post a Comment