Saturday, January 20, 2018

Za A Gyara Wannan, In Sha Allahu

Dazu na ga wannan hoto a wall din d'ana, Adamu Tilde, inda aka nuna yan jamiar ATBU a kasa suna daukan darasi. Wannan ba bakon abu ba ne hatta a jami'o'i da suka kai shekaru 60.
Sati biyu da suka wuce, a Jami'ar Ahmadu Bello, Samaru Zariya, turmutsutsi aka yi wajen shiga laccar wani kos na Physics a Faculty of Science lecture theatre. A nan 'yar wani abokina aka matseta har ta some, aka kwseheta magshiyyan zuwa asibiti, rai kokoi, mutu kokoi.. A can ta farfado da kyar. Abin mamaki shi ne tun da asuba ake zuwa kama wuri a wannan tiyatar ranar da ake da wannan kos din.
kuma wani abin bakin ciki da ban tsoro shi ne wadannan dalibai wadanda su ne manyan gobe, a cikinsu aka samu wanda ya sace mata wayarta lokacin da ta fadi...
Amma ni ban ga takaici a wannan hoton ba. Abin shaawa na gani. Yau, don ci yarda a ilmin boko da shaawarsa, har ga 'ya'yanmu mata zaune a kasa suna nemansa. Alhamdulillahi. Tabarkalla.
Saura da me? Ina tabbatar wa masu karatu ba da jimawa ba za a gyara wannan abin, muddin yayana, Adamu Adamu, ya ci gaba da kasancewa Ministan Ilmi. Za a san yadda za a yi a tabbatar cewa a kan duk darussa a jami'o'in Nijeriya, bisa ka'ida, ba inda aka samu foye da yara 200 a cikin dakin karatu. In ko an samu, to VC din ya kuka da kansa.
Za a cimma wannan buri ta hanyar raba daliban tsakanin malamai fiye da daya, ko ma me wannan zai bukata ta hanyar kara malamai ko janyo manyan malamai su ma su rika koyarwa a wannan matakin. Bayan haka, ga.hanyar sadarwa ta zamani da jami'o'in yakamata a ce sun fara amfani da su wajen koyarwa tuntuni. Zamanin da za a rika cunkoso da sai da handout yakamata a ce ya wuce.
In sha Allahu za mu ga abin da za.a yi. Amma dole irin wadannan abubuwa su zama tarihi a zamanin canjo. Za a.gyara, in sha Allah.
Dr. Aliyu U. Tilde
15 February, 2015

No comments:

Post a Comment