Saturday, February 3, 2018

Hattara Dai APC da Yan’arewa!

Jiya na karanta labarin cewa Kwamitin Sake Tsarin Zaman Nijeriya na jam’iyyar APC (APC Restructing Committee) wanda Mai Girma Gwamna El-rufa’i ya shugabanta ya mika rahotonsa ga Shugaban jam’iyyar, Mr Oyegun.
Kwamitin ya ba da shawarar a rikito da al’amurra goma daga dankin ikon Gwamnatin Tarayya a mai da su ga hannun jihohi. Cikin wadannan abubuwa har da batun yan’sanda da gidajen yari, da lasisin harkar maadinai da mai, da sauransu.
Hankalina ya tashi a kan lamurra uku da na lasafta amma dai zancen bai wa gomnoni ikon su kafa nasu rundunonin yan’sanda ya fi damuna don in an yi wannan mutane biyu su kwana da sanin za su sha ukuba a Nijeriya.
Kashi na farko sune yan’arewa da ke zaune a kudu da musulmin da ke zaune a jihohin Plateau, Benue da Taraba. Tabbas wadannan su shirya tattara komatsansu idan wannan shawarar ta APC ta samu karbuwa. Da ma yaya halin kura bare an bata tsaron garke? Yanzu ma yaya, balle a ce gwamnonin wuraren nan suna da yan’sanda masu dauke da makamai? Da ma majalisu nasu ne, haka ma’aikatun shariah a wadannan jihohin. Kawai an basu damar aikata ta’addanci: su yi doka kuma su zartar da ita.
Misali a nan shi ne irin yadda ake takurawa Hausawa a kudu, da bakin da suke zuwa can ci-rani ko sayayya. Legas ta yi kamari bisa wannan. Kungiyar OPC kawai za a yi wa rijista a matsayin yan’sanda su ci karensu ba babbaka. A zamanin Goodluck, mun ga yadda siddan kawai ake tsare Hausawa a Kudu-maso-Gabas da sunan yan’ta’adda ne su yi wata da watanni garkame kuma a kasa yin komi. Yau ba za a yi haka ba don shugaban kasa Bahaushe ne. Amma ko a karkashinsa, idan jahohin na da yan’sanda, shi ke nan, sai su fake da yancin yin doka da yan’sandan da suke da su su hanawa yan’arewa rawan gaban hantsi.
Irin wannan ya faru a jahar Benue kwanan nan. Na je na gani. Gwamnan ya kafa sansanonin horar da yan’ta’adda da yau yake amfani da su wajen korar Fulani. Kuma gwamnatin Buhari ta ba shi sojoji da yan’sanda da za su tabbatar korar ta wanzu don “a zauna lafiya.”
Wayyo Bahaushe! Kullum da barazana ake cinsa. Ba bafilatani mai kiwo yau a kasar Tibi, sai dai kasar Idoma. Duk an kore su sun dawo Jahar Nasarawa. Kaddara da Gwamnan Benue na da karfin yan’sanda, da abin zai fi haka muni. Yanzun ma ya cimma burinsa amma da taimakon Buhari.
Irin wannan ne su Dariye da Jang suka gagara aiwatarwa a Filato. Da suna da yan’sanda nasu na kansu, ko da akwai shugaban kasa da zai ba su sojoji da za su kare muradunsu don a zauna lafiya, da yau ba bahaushe ko bafilatani ko musulmi a Filato. Da Obasanjo ne, abinda ya faru a Benue da korar Filani da bai faru ba don yana da karfin hali da taratsin da zai iya takawa Ortom birki. Amma a wajen Buhari, sai mu ce kash, albasa ba ta yi halin ruwa ba.
To jama’a a yi hattara. Ina ganin kafa a dalilin Buhari da jam’iyyar APC su yi mulki a sha’afa ko a mika wuya bori ya hau kamar awaki in an mika musu dusa. Buhari zai gama mulkinsa watarana, amma kar a bari ya tafi ya bar mu muna da-na-sani. Wannan batun yan’sanda a jihohi matsala ce wacce duk jami’an tsaro sun ce zai haddasa fitina da danniya. Ko Obasanjo da Jonathan sun ki yarda da shi. Amma ga yadda lamurra ke tafiya, musamman abinda nake gani da idanu na yanzu haka a Benue, ni kam jikina ya yi sanyi matuka.
Sai kashi na biyu: yan hamayya za su dandana kudarsu idan gwamnoni suna da rundunonin yan’sanda nasu. Mun ga wannan zamanin su marigayi Sardauna. A samu sauran yan NEPUn da ke raye a sha labari. Ko wane mai mulki, in ba ya yi zalunci ba hankalinsa bai kwanciya, sai wanda Allah ya wa rahama. Ka ga idan gwamna na da majalisa, da yan’sanda, da kotuna, da gidan yari, shi ke nan, tuwo na mai na. Shi ya sa ka ga hatta gwamnoni Hausawa ke goyon bayan haka don burinsu na danniya ya cika.
Toh. Awakin Arewa an mika musu dusa, an ba su kuri’a a kasar yarbawa, nasu ya zama shugaban kasa. Yanzu kuwa lokaci ya yi da za a biya wa kura aniyarta. Wanda ya ci ladan kuturu, an ce, sai ya masa aski. Amma kuma Bahaushe, a kirarinsa ga k’uda, ya ce: kuda, wajen kwadayi a kan mutu.
Zan rufe wannan sharhi da nasihar babanmu, marigayi, Saadu Zungur, lokacin da yake jan kunnen yan’arewa kan kar su yarda da mulkin jamhuriyya da zai soke ikon sarakuna, ya ce:
Hakkin jama’a mu fada muku
Ku nadama ko ku yi dariya.
Dariyarku ta zam kuka gaba
Da nadamar mai kin gaskiya.
Dr. Aliyu U. Tilde
27 January 2018

No comments:

Post a Comment