SAKO 3
MARABA DA DOKAR HANA SADAKA A LEGAS
Dr. Aliyu U. Tilde
A farkon wannan satin, gwamnatin Jahar Legas ta zartar da dokar hana baiwa mabarata sadaka a titunan garin Legas. Wannan dori ne kan dokar hana barar kwatakwata wacce aka kafa shekarun baya da matakin kwaso masu barar a mota daga legas din ana jibge su a manyan garuruwan Arewa, musamman Kaduna.
Dokar hana sadakar ta tanadar da daurin shekara biyu ga duk wanda aka kama yana baiwa mabaraci sadaka a titunan Legas. Ba hana sadaka dokar ta yi ba, don ta yardarwa duk maniyyaci ya kai sadakarsa masallaci ko coci ko gidajen gajiyayyu wadanda gwamnatin jahar ta tanadar.
Wani ya ji dokar ta zo masa bambarakwai. Dokar hana sadaka? In ma ba a ci sa’a ba sai ya dorawa Gwamna Fashola kaulasen don a ganinsa ya zama manna’in lil khairi, watau “wanda yake hana alheri”.
Ni kuwa a ra’ayina wannan doka ce da aka jima ana jiranta, wacce kuma za ta taimakawa al’umma fiye ma da dokar hana bara ko matakin kwaso mabaratan a maido su Arewa. Hukumomi sun sha yin dokar hana bara amma mabarata sun yi biris da wadannan dokokin tunda barar ta zame musu sana’a. Amma in aka hana mai bayarwa, ka ga mai bara in ya gama shan ranarsa yau a titi, gobe ma ya sha, jibi ya sha, ba tare da samun ko sisi ba, gata zai yi wa kansa kiyamul laili. Sai ya zauna a gida yayi ta rusawa Fashola ashar. Nan ma, in ya ga ba ci, sai ya daina ya doshi masallaci ko coci kamar yadda doka ta tanadar. Kaga ba duka ba zagi an kau da ganinsa akan titi inda yake sa kansa cikin hadari kuma yake zubar da mutuncin addininsa da na jinsinsa.
Na yarda cewa a gaskiya Fashola ya san kan tsiya. In ba mangala, me zai kai jaki gona? Farkon na ji irin wannan doka a kasar Nijer ne. Su mutanen Nijer in anyi obalod (watau cika mota da fasinja fiye da abun da doka ta tanada), ba direban jandarmai su ke kamawa ba. A’a. Ba ruwansu da shi in sun tsaiyar da mota. Fasinjan da aka yi obalod din da shi shi ne suke fitarwa suyi ta jibja sannan su hukunta shi. Ka ga gobe in ya zo tasha ya ga mota ta cika, ba zai ce a yi obalod da shi ba. Kan da Gwamna Sule Lamido na Jigawa ya gane ma, shi ma da haka ya yi.
Mu koma kan batun bara. Kamar yadda na ce, ina maraba da dokar hana bada sadaka a titi, ba ma na Legas ba, ko a titin Bauchi ne, in Gwmanonin namu suna da katabus din yin haka. Ra’ayina akan bara, sabanin almajirci, sanannne ne don na rubuta dogon sharhi a kai bariya waccar. Almajirci wani abu ne dabam. Shi ba bara ba ne, tsarin karatun muhammadiya ne da ake koyawa yara iya karatu da rubutu, da kuma karatun Kur’ani Maigirma, da haddace shi, da rubutashi. Bara kuwa it ace gararambar da manya da yara suke yi akan titi da guraren da jama’a ke taruwa, ana roko. Akwai almajirai da yawa da basa roko akan titi da matattarar mutane. Tsanani in suna yara sukan bi gidajen mutane suna ko dan kanzo. In ko sun kai shekara 14, to sai su fara sana’a kamar noma, dinkin hula, kasuwanci da sauransu kafin su karasa hada haddarsu. In sun cira gaba kadan sai aure, da iyali, da rayuwa kamar to kowa. Don haka nake da tsattsauran ra’ayi kan bambamta bara da almajirci.
To, ina ga katon da yake baje nakasarsa a fili yana nuna wai ga abun da Allah ya maida shi don kawai a tausaya masa a bashi kudin kashewa? Kuma inda Legas kachaukau dinta za ta taru yau ta bashi kudin Alhasan Dantata, ba godewa Allah zai yi ba ya hakura ya zauna a gida. A’a. komowa gobe zai yi yana nuna dungun hannusa ko tsiyayayyun idanunsa yana cewa a bashi don Annabi. A dole ga shi shi ne wanda Allah bai yiwa gata ba. Subhanallahi. Can gida kuwa ya yi asusu sai tara kudi ya ke yi jiddin-wala-hairan har ya sayi motoci da gidaje, abunda akasarin yake roka ma basu da shi. In ko baka bashi ba, wani mabaracin ma har zambonka zai yi, ya ce wa ‘yan uwansa mabarata, “wannan maciji ne” (wai don ka daga hannu ka ce ya yi hakuri), ko ya kiraka “Shago” (watau mai hanu dunkule kamar dan dambe), da dai sauransu.
Inda za ka gane bara ba tilas ba ce shi ne Malam Bahaushe ne kawai yake yin ta a Najeriya. In an ce Malam Bahaushe, ana nufin musulmin da ke Arewacin Najeriya kama daga kasar Nupawa har zuwa Sakkwato da Barno. Ka taba ganin wani dan kabilar kudu ko tsakiyar Najeriya yana bara, ko da kuwa musulmi ne? Wannan aikin sai mu, da yake mu muka fi rena wa Ubangiji. Don haka aka renamu a kasan nan, ake ganin mun fi kowa ci baya da talauci.
Wasu sun dauka wai bara musulunci ne. Wanda ya ce haka ya yi wa Allah karya. Daga Bakara har Nasi ba inda aka ce wani ya mai da bara hanyar cin abincinsa ko tara arziki. Abunda nassi ya yarda da shi shi ne mabukaci ya baraici daidai da bukatarsa inda yake zaton samun biyan bukatar musamman ma a tsakanin danginsa ko abokan zamansa na kusa wadanda yake da hakki kan dukiyarsu kamar yadda ya zo a Kur’ani. Amma ya tashi takanas ta Kano ya tafi wani gari da sunan bara wannan al’adar Malam Bahaushe ce da take barar da mutuncin jinsinsa gaba daya. Dole ne sauran kabilu da ke bashi sadaka Allah ya daukaka su a kansa, don maganar Annabi ba za ta fadi kasa banza ba, da ya ce hannu mai bayarwa yana sama da hannu mai karba.
To in musulunci bai yarda da bara ba, me zai sa ba za mu marawa gwamnatocinmu baya ba wajen tumbuke wannan mugunyar itaciya da take zubar mana da mutunci? Na yi murna mutane sun fara fahimtar haka don ban ji wani mai mutunci da ya ce Fashola ya yi laifi ba. Ni kam yamun daidai. Fata nake sauran gwamnoni su goyi bayansa, musamman na kudu, kafin dokar ta hauro nan Arewa.
Sai dai kuma wani hanzarin da ba gudu ba. In a Legas akwai gwamnati mai karfi, a nan Arewa bamu da gwamnatoci da za su iya aiwatar da doka, kowace iri ce kuwa. Kai dai a bar gwamnoninmu wajen yin gululu a zabe da sayar da hakkin jama’arsu samanan kalilan wa ‘yan kudu. Nan kam ba wanda ya fisu. Amma da sannu za su taho da abunda suka yi gululunsa ranar Kiyama.
A karshe muna jinjinawa Gwamna Fashola don wannan gagarumin taimako da ya yi wa Arewa. Muna kuma yi masa fatan Allah ya kara masa basira da hazaka.
Ba karambanin da zai sa in sake baiwa wani musaki sadaka a titin Legas. Ina sauka filin jirgi a Ikeja, zan kama zip din lalitata in ja, zeeep. Ba sadaka, sai a masallaci, in na yi niyya.
Tilde,
15 May 2011