Thursday, January 18, 2018

Ali Nuhu Da Sauran Ƴan’fim, Caffa Gare ku

Yanzu – kafin in shiga sabgar ranar – na gama kallon fim din Ma’aurata wanda Ali Nuhu da Hadiza Gabon suka fito a matsayin jarumai mata da miji. Fim din yana faɗakar da cewa soyayya bai kamata ta kasance don dukiya ba, sai don ƙauna da taimakawa juna, ta yadda in ɗaya ya shiga matsala, ya kamata ɗayan ya taimaka masa. A cikin fim din, an nuna yadda abokin Kamal da maigadinsa da mai aikinsa da ƴaƴansa duk suka tsaya tare da da shi lokacin da jarrabawar karayar arziki ta same shi, amma matarsa wacce lokacin da yake da hali yake matuƙar kyautatawa da hidimomi kala-kala ta rika wulaƙanta shi da nuna masa son kai.
Wannan hikaya ce da ake samu a rayuwar aure a duniya duka. Ta yi ma’ana saboda darussanta. Haka kuma sauran fina-finan Hausa waɗanda na kalla suke. In mutum ya kwantar da hankalinsa, ya cire hassada ko kushe ko halin nafi-iyawa, dole zai yarda da cewa a bayan kowane labari akwai darasi. To, sai ya ɗau darasin ya bar abubuwa na gazawa da ya gani a ciki waɗanda shi a ganinsa sun gaza wa iyawarsa, ko iliminsa, ko aƙidarsa, dss. Haƙiƙa Nabigha al-Nu’maani ya yi gaskiya da ya ce:
Na ba da raina ga wannan da in na zo masa
Zai karbi ƙoƙarina ya yafe gazawa.
Wannan uzuri shi ne wanda da yawa daga cikinmu muka gagara yi wa ƴan’fim. Kullum muna cikin kushe musu saboda wasu abubuwa na gazawa mu mance da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma da cike mana gurbi wajen cire mana kewa (leisure) bayan a shekaru arba’in da suka wuce wasa-wasa duk mun kawar da abubuwan cire kewa da shaƙatawa a rayuwarmu ta Hausawa. Wasu suna ganin ilmin ƴan’fim bai kai a kula su ba, ko suna yin wasu abubuwa saɓanin al’ada kamar sa ɗamammun kaya, ko rayuwar wasunsu yana ɗauke da munanan labarai, ko a ce ba su kai na Turawa kyau ba, ko suna kwaikwayon Indiya, ko a ce labarinsu kullum bai wuce soyayya da aure ba, dss.
To amma idan aka duba cewa shi fim kullum yana biyo rayuwar mutanensa ne, kuma duk abinda mutum zai yi ba ya wuce yawan damar da yake da ita ko wajen da yake ciki (environment), ni kam sai in ce ƴan’fim ɗin Hausa suna ƙoƙari. Duk abinda muka gani a fim rayuwarmu ce. Kanmu za mu zarga ba ƴan’fim ba. Mai laifi za a zarga ko mai ida saƙo? Batun ilmi bai taso ba, don ina ganin a yanzu kam sun yi nisa wajen naƙaltar aikinsu. In muka duba ƙalubale masu yawa da suke fuskanta dole mu jinjina musu.
Nawa suke da shi har da za su yi irin na Turawa? Mutane nawa ke zuba jari a harkar fim ko suke ba su gudummawa? Kuma mutane nawa za su iya cire kuɗinsu don su sayi fim mai tsada idan an yi shi? Akasarinmu za mu gwammace mu same shi a maho mu kalla ko mun san satowa (piracy) aka yi. Kuma ba mai baiwa yaran nan namu da ke yin fim gudummawar sisi, ba mutane ba ba kuma gwamnati ba. Nan fa Baba Buhari ya ce zai taimaka musu da gina ƙauye na musamman na zamani saboda bunƙasa harkarsu, wanda ba a yi wa ƴan kudu haka ba, muka kwance masa zani a kasuwa, muka yi mirsisi, muka yi ta kushe wa abin da yi masa barazana in bai janye shirin ba. To da aka janye, ci gaba aka samu ko ci baya?
Kaddara babu Hausa fim, da yau waɗanne fina-finai iyalanmu za su kalla? Kar mutum ya kalli kansa a matsayin maikuɗi ko babban ma’aikaci ko babban ɗan’boko. A’a. Ya duba al’umma na ƙasa wanda ba yadda za a raba su da kale-kalle don fidda kewa da kuma shaƙatawa. Rayuwa ba ibada ba ce ko yaushe. Da haka take da Allah ya yi mu mala’iku masu bauta masa ba hutu. Amma ya gwammace ya yi mu ƴan’adam wadanda suke da bukatu dabam-dabam bayan ibada kamar neman abinci, jima’i, abota, neman ilmi, shaƙatawa, dss. In mutum ba ya bukatar kallon fim, kar ya aza irin su Dr. Tilde da sauran irinsa ya-ku-bayi ba za su kalla ba. A ƙalla, gara in kalli fim duk yammaci da in je daba ina cin naman mutane.
Da ba ƴan Hausa fim da yanzu ba waɗanda muke kallo banda fina-finan ƴan-kudu da na Indiya da na turawa ta hanyoyin sadarwar zamani wanda ba wanda ya isa ya hana. Ai da farko na Turawa da Indiya kawai muke kallo. Sai aka kawo na Nijeriya (ƴan-kudu) muka raja’a can, kafin namu suka fara kuma suka ci gaba ba tare da dakatawa ba duk da kushen da muke musu. Yau ga shi nan a cikin al’ummarmu, akasari masu kallon fim na Hausa suke kallo a akasarin lokutta. Ashe kuwa ƴan Hausa fim sun share mana hawaye.
Ni a ganina, ya kamata mu bada namu gudummawar wajen inganta aikinsu a maimakon kushe musu ko da yaushe. Kuma duk abinda zai inganta aikinsu mu zame masu goya masa baya duk da ba za a bari su wuce gona da iri ba. Su ma kuma ya kamata su riƙa saurarawa. Su ɗauki shawara mai kyau wacce za su iya. Fim aiki ne na adabi. Dole idan ka yi wani ya soke shi walau ta hanyar hassada ko ta hanyar gyara. To in an yi suka sai a natsu a duba jauharin maganar, a ɗauki na ɗauka, a yar da na yarwa.
Ina fata Allah ya taimaki ƴan’fim dinmu wajen ƙara musu basira, da himma da hikimar misalta abubuwa da za su taimaka wajen cigaban al’ummarmu, ya kuma raba su da sheɗanu da za su karkata sana’arsu zuwwa hanyar halaka. Akwai halakakku a kowace sana’a, a kowane gari, kila ma a kowane gida. Ƴan’fim mutane ne kamar mu ba mala’iku ba. Duk abinda suke misaltawa ba wanda ba ya faruwa a rayuwarmu, sai ma abinda suka rage. Yadda muke addu’a Allah ya ci gaba da inganta halayenmu da na zurriyarmu, su ma mu sa su a ciki, don cikin al’ummarmu suke.
Wasu a nan za su ƙalubalance ni cewa in gaskiya ne, zan iya barin ƴaƴana su yi fim ko zan iya auren ƴar fim? Amsata a nan ita ce: idan akwai wani ko wata a cikin ƴaƴana da za su so yin fim, ba kawai zan ƙyale shi ya yi ko ta yi ba, har kwarin gwiwa zan ba su iya ƙarfina bisa sharuɗɗa da zan kafa masu kamar yadda nake ba su kwarin gwiwar samun ilmi da yin wasu sana’o’i. Idan kuwa don auren ƴar fim ne, tabbas, ban ga laifin yin haka ba da a ce hali ya kama in yi hakan in ina sonta kuma na yaba hankalinta.
A karshe, ina miƙa caffata da jinjinawata ga wanda – a ra’ayina – ya fi nuna fice wajen juriya da hazaƙa a gudanar da harkar Hausa fim, gwarzo Ali Nuhu, da daukacin mutane na da da na yanzu da ke cikin harkar irin su Sani Danja, Adam A. Zango, dss, da kuma masu aiki a bayan fage don inganta harkar irin babban aminina Alhaji Sani Muazu. Allah ya muku albarka.
Ware takwara da na yi wajen yabo ba son kai ba ne. Tabbas shi ne mutum daya da nake ganin ya fi naci kana bin. Tun da ya fara, ya dage a kai, bai daina ba har yau kuma yana ba da shugabanci nagari ga masu tasowa. Ba abin mamaki in an samu mai suna Ali ya zama gwarzo. Ali gadanga ƙusar yaƙi. Garga!
Ire-irena da yawa suna yabawa gudummawarku muna kuma yi muku fatar alheri. A yau in aka tsare ni aka ce waye na sani a fina-finan Turawa ko Indiya ko Nyamurai, zan rantse ban san wani ba in banda wanda nake jin mutane suna ambata. Amma idan ka tambaye ni gwarajena a cikin ƴan Hausa fim, mazansu da matansu, zan ba ka jerin sunaye masu yawa – na da da na yanzu, dukkansu daga jinsina na ƙasar Hausa. Ahamdulillahi, ba don ƴan Hausa fim ba da ina nan yanzu ina kallon wasu mutanen dabam da al’adunsu, ina mai da su abin koyi, hakaza ƴaƴana da iyalina.
Kar a gajiya. Gaba dai, gaba dai.
Dr. Aliyu U. Tilde
11 Yuli, 2017

No comments:

Post a Comment