Thursday, January 18, 2018

Mu Hausawa Muna Da Matsalar Ko-oho Mai Hana Mu Cigaba

Mutum ne makanike, yana sana'ar fiye da shekara 30. Yana gyara babbar mota marsandi, misali. Amma ko filtar bakin mai ba zai iya ajewa don amfani a garejinsa ba, ko ya bude shago a garejinsa na kayan gyaran yau da kullum wandanda zai rika amfani da su don kastomominsa su rika samun biyan bukata ko yaushe, ko da ranar lahadi ne irin ta yau.
Komi ya bari sai bukata ta tashi, mai mota ya bai wa yaro kudi ya je shagon Nyamiri ya sayo. Idan ranar lahadi ce, sai dai kastoman ya hakura da tafiyar kasuwancin da motar za ta yi.
2. Mutum ne yana aikin gyaran AC na motoci da firij na gidaje da dakunan sanyi (cold rooms) na sama da shekara 35 amma ko lita daya ta mai da ake sa wa kompressor ba zai aje ba a kantinsa. Haka kawai zai yi ta gudanar da aiki ba ko sisi na jari. Sai in zai yi aiki ya karbi N500 ko N1000 ya sayo a hannun Nyamiri. Idan Nyamiran ba su bude ba, a taru a zauna - shi da kastoman - sai gobe. Dabarar ya bude shago a garejinsa na wadannan abubuwa ba ta taso ba.
Da wani zai ba su jari, kafin ka ce kwabo sun cinye jarin wajen hidindimun iyali da fankama a gari. A taru ana musu fadanci har su koma gidan jiya - wayam.
Amma dai a ce yau a gari a rasa wanda za a sayi filtar marsandi Atego a gunsa? Na.bugawa Nyamurin amma.cewa yake sai dai in bari sai ya dawo daga coci da rana? Da mutum daya zai ware shago guda na filtocin motoci dabam dabam, manya da kanana da ya share wa mutane hawaye. Wani ya bude na kayan firij da AC, dss.
Wai yaushe za mu hankalta ne? Shi ya sa nake yabawa Dangombe mai gyaran Honda a Bauchi. Yana gyara kuma yana sai da kayan gyaran a wani makeken shago nasa a garejin.
Mafita
Ina ga ba za a bar wannan abin hannun masu sana'ar ba kadai da tunaninsu. Dole yan'boko da shugabannin al'umma kamar gwamnati da sarakuna su shigo ciki.
Dole wadannan sassa na al'umma su fito da tsari na wayar da kan masu sana'ar hannu da nuna musu dabarun zamani na kasuwanci da kwatar kai. Hakaza, dole a kowanne fannin bukata ta rayuwa a samu amintattu wadanda za a bai wa jari don samar da abubban bukata a fannoni dabam dabam.
Ga matasa nan da ke kare karatu a manyan makarantu, ba aikin yi. Da za su cire burin samun aikin ofis na sata da biro, su dau wannan layin bisa gaskiya da mana da sun share mana hawaye.
In mun dau abubuwan nan da muhimmanci dole mu samu tsarin gudanar da su. In ba haka ba, in an bar su hannun talakawa da suke hannu-baka hannu-kwarya, to za a jima ba a samu biyan bukata ba. Kullum rai zai yi ta baci, kamar yadda nawa ya baci yanzu.
Manyan motocin sanyi hudu amma ba wacce za ta kai min kaya Gombe. Tir da al'umma marar kishin zucci. Manomanmu kadai ke da himma. Amma mu sauran sai lalaci da tarin hassada, dala dala.
Dr. Aliyu U. Tilde
9 July, 2017

No comments:

Post a Comment