Saturday, January 20, 2018

BULALAR GASKIYA

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Rajaz: ( - - v -/ - - v -/ - - v --)
1. Sarkinmu Allah na k'udirta zuciya
Yau kan Rajaz zan wo Bulalar Gaskiya.
2. Allahu Sarki shi kad'ai “Haqqul Mubin”
Sakonsa haqqu sa da Manzon gaskiya.
3. Tsari na sammai har k’asa tun fil azal
Tabbas ya na nan ne a hanyar gaskiya.
4. “Dau’an wa karhan” so da k'i yac ce, “Ku zo”
Sauri sukai domin su amsa bai daya.
5. Cewa sukai mun zo "ataina d'a’i’iin”
Komai ka zartar za mu bi kan gaskiya.
6. Yac ce sama zamto bakwai kwana biyu
Sannan ya ba dukkan su odar gaskiya.
7. Tauraruwa ba a k’ida yak k’awata
Wannan samar yai yo tsaro don kariya.
8. To ka ji ikon Maibuwaya Maisani
To mi ka taka har ka zan k'in gaskiya?
9. Sammai gare ka ko ko kas, kai ajizi?
Ba d’ai gareka ba ka yin ko tsintisya.
10. Ka zo a huntu za ka komawa haka
Karshen ka rami mai duhu ba dukiya.
11. Da za mu sa yin gaskiya mui tanadi
Da rayuwa ta zo da d'adin duniya.
12. Da babu mai kwana ciki ba ko tuwo
Da ba jahala bar ta zancen danniya.
13. Tamkar ka ba almajirai nama tuli
Kome yawa tai bai isa sai gaskiya.
14. Don gaskiya ce za ta sa ai yo rabo
Kowa ya samu har ya zan yin dariya.
15. Karya ko warwaso ta ke sawa ku ji
Manya su kwashe sui ta holewar tsiya.
16. Yara suna kuka suna wayyo niya
Da mun yi loma ko guda ko ‘yar miya!
17. Yara su zam tsinewa manya har abad
Dole a zamna babu canji duniya.
18. Mu ma na k’as din kar ka zancen gaskiya
Don mun rasa ne za mu koka ka jiya.
19. Da za a kawo yar amana adana
Cinye ta za mui nan da nan ba gaskiya.
20. Kirga a gwamnati babu sarki ko guda
Duk mu talakkawa muke wannan tsiya.
21. Kokenmu da wai ana yin danniya
Sarki da d'andoka da resden bai daya.
22. To yau fada mun gaskiya na tambaya:
Wa ye ya ke danne talakka duniya?
23. In za ka ban amsa ka zan yin gaskiya
Ce mun: "Talakkawa suke yin danniya."
24. An ba su ilmi tun a wancan zamani
Loton a ke cewa ana yin danniya.
25. Canji a kai sai munka zam jamhuriya
Ya'yan talakka mun haye can k'oliya.
26. Da ma a ce mun d'auki hanyar gaskiya
Da yau gaba d'ai ba talakka duniya.
27. Sai munka d'au hali na b'eraye duka
Fata a gun kowa ya kas Najeriya.
28. Hakki na milyoyin jama’a zai hada
Sannan ya sace don yana tsoron tsiya.
29. Kullum ya zamna yai tunanin can gida
Danga da yunwa sai ya tsoro zuciya.
30. Sata ya ke, k’ari ya ke, kwasa ya ke
Buri wadata babu dawowar tsiya.
31. Bai san tsiya na nan a gunai har azal
Ranar hisabi za ya zam ba dukiya.
32. Dukkan mutane za su zo nema a gun
Wannan fak'ir hakk'insu ranar gaskiya.
33. Dukkan ibada za a dauka ai rabo
Sannan ya k'are babu komai sai wuya.
34. Rannan Jahannam za ta ce, “Ya Excellency!
Antal aziz antal karim", sai hawiya.
35. Tun shekaru nai dalibi yai tsokaci
Burinsa yai ofis ya sace dukiya.
36. Mai ce mu gyara sai mu d’au gaba da shi
Sharri na dunya duk mu dora mai wuya.
37. In anka ce ga d'an vacancy sai ka ga
Mun dandazo kowa ya na son dukiya.
38. Ba d’ai na kirki saiko “illa man rahim”,
Ka san ko ba hanyar a zamna lafiya.
39. Yan takara sai alkawar ba ko daya
Wannan da zai dage ya zan mai gaskiya.
40. Azzalumai, sai dai ka toge ‘yan kadan
Sauran umuman ba su kaunar gaskiya.
41. Yau ga shi nan mun kai kamannin hawiya
Manya su tsine, mu mu tsine, bai daya.
42. Ni dai Aliyu nai hawaye don wuya
Don d’ai tunanin baya an yo gaskiya.
43. Ranar a Khartoum nai zugum ba murmushi
Na je bid’ar gurbin karatu can niya.
44. Domin Nawar domin Umar ‘ya’ya biyu
Domin guraben sun gaza Najeriya.
45. Sai, “Je ka can, ai babu gurbi ko daya"
Sai tak’ama sai ko wulakancin tsiya.
46. Dan nittuna can baya su ke zakkuwa
Najeriya neman karatu, dukiya.
47. Nai tsinuwa duk duniya Allah isan
Kan wanda duk yakkai mu wannan hawiya.
48. Kogi na Nilu na wucewa yai Masar
Ni ko hawaye ke zuba har zuciya.
49. Nai yo du’a’i Rabbi domin Adamu
Har ma da Nuhu har da dukkan Anbiya.
50. Albarkacin Musa da Isan Maryamu
Har ma da Ibrahim uban duk Anbiya.
51. Albarkacin Khairil Wara wan Jafaru
Sannan Ali har ma da Ahli bai daya.
52. Albarkacin littattafan nan su hudu
Allah ka shiryar zaluman Najeriya.
53. In sun k'i shirya sunka dage kan bata
Zan hallakarwa har zuriyyar bai daya.
54. Wallahi Sarki mun gaza mun ko gaji
Kai agajin kowa da ke son gaskiya.
55. Ya k’aumi nai rok’o ku ce amin duka
Kui wo salati kan fiyayyen Anbiya.
56. Kan su iyaye Rabbana kai sallama
Mu ko mu zam k'auna da son yin gaskiya.
57. Mui yo ta dunya har a Yaumil Haqqi don
Kai tausayi kai agaji ran gaskiya.
58. Tammat k'asida kan Rajaz na kammala
Hamsin takwas ne baituka kan gaskiya.
Tammat bihamdillah.
15 March 2015

No comments:

Post a Comment