Saturday, January 20, 2018

GODIYA GA ALLAH

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Muqtadab: ( - - - - / - - v - )
1. Farko Allah/ zan ambata
Waka zan yo kan godiya.
2. Ni kam Tilde za nai yabo
Kyauta ba wai don na iya.
3. Baiwa jibgi kan d’an Adam
Kowa ka mai nan duniya.
4. Farkon baiwar shi khaliqu
Yin bayi bayan ba daya.
5. Sai fifiko gun d’an Adam
Kan duk mahluqai bai daya.
6. Ilmi har rai har rayuwa
Kyauta kyauta ba ma biya.
7. Haske kullum nan duniya
Zai kai yamma tun safiya.
8. Don mui nema doron k’asa
Mui walawa ba ma biya.
9. Tsirrai su ma sui tanadi
Na abinci ga dukkan duniya.
10. Wa zai kawo wannan duka?
Ce: sai dai Allah shi d’aya.
11. In mun aiki mun kai gaji
Fa duhu zai zo nan duniya.
12. Don mui barci hutun jika
Da gab’ob’I duk sui lafiya.
13. Wannan sauyi wa zai mana?
Sai dai Allah Sarki d’aya.
14. Ga iska baiwa ko’ina
Domin shak’ar duk duniya.
15. Ba mai ikon yai handama
Ba sai ka kawo dukiya.
16. Sannan ba rai in ba ruwa
Tsirrai, dabba baki d’aya.
17. Teku, kogi har korama
Yai yo su ruwa har rijiya.
18. Ba mai ikon yai handama
Baiwar Allah mai duniya.
19. In da ya ba yankasuwa
Ka san da yau mun sha wuya.
20. Mutuwa za kai in ba kwabo
“Shares” duk sai dai mai dukiya.
21. Balle ko a ce azzalumai
Da sun shake kowa wuya.
22. In ba za kai partinsu ba
Nishi ka san zai ma wuya.
23. Fa ruwa zai zam zinariya
K’uri’a, dollars sai ka biya.
24. Shegu Allah bai ba su ba
Ikon na gu nai shi daya.
25. Shi zai iska, da ruwan sama
Tsabta ba mai shi duniya.
26. Ya ce: “Hal antum shakirun?”
Sarki mun gode bai daya.
27. Bayan rani sai damina
Yalwa ta sabko duniya.
28. Noma na abinci ba kida
‘Ya’ya na itace ba wuya.
29. Mu dai kullum sai ci muke
Dammai, Kwando duk safiya.
30. ‘Ya’ya, yara manya duka
K’oshi za mui, mui lafiya.
31. Baiwa jibgi ba ta k’ido
Ta kai halin mui godiya.
32. Amma kullum sai kangara
Ba ma kaunar bin gaskiya.
33. “Kutilal insan! Ma akfarah!!
Aya tai tir halin tsiya.
34. Bayan baiwa don mu duka
Ya banbanta gun d’ai-d’aya.
35. Ga dogo yai ba ko dari
Ga kau guntu mai dukiya.
36. In kai kukan ba dukiya
kallo ‘ya’ya har lafiya.
37. Sai ga tarin mai dukiya
Kurdi dala ba lafiya.
38. Ya kwan kwance sai dai haki
Zai so canji yai lafiya.
39. Ko ko Haifa ce bai yi ba
Shi d’ai zai zauna duniya.
40. Zai so cewa ba dukiyar
Yai ‘ya’ya tari fariya.
41. Sai mui lura mui hankali
Baiwa bambam nan duniya.
42. Ba bawa mai baiwa duka
Sai yai rok’on Allah daya.
43. Kullum zamto ba korafi
Sai dai shukra kai godiya.
44. Kar dai shedan yai ma zuga
Renin baiwar Sarki daya.
45. Wannan zai sa kai hassada
Ciwo babba gun zuciya.
46. Mai sa B.P. yai can sama
Sawu, hannu sui shan-Iya.
47. Sharrin hasid ko “iza hasad”
K’are shi a kai nai shi daya.
48. Duk mai kyashi zai hallaka
Zai tab’ewa tas duniya.
49. Sarki Allah nai addu’a
Kawo sauki gun rayuwa.
50. Kowa Sarki kai agaji
Yalwarka ta kai mui dariya.
51. Duk mai ciwo yaye masa
Har sai yaz zam mai lafiya.
52. Kai yo tsira kan Annabi
Angon Dije har Mariya.
53. Manya su ma saka musu
Aljanna kai su gaba daya.
54. Tammat waka duk baituka
Hamsin-sitta kan godiya.
55. Maf’ulaatun mustaf’ilun
Muqtadab bahri ba tambaya.
56. Ban kwana nai nan zan tsaya
Allah sarki nai godiya.
Tammat bihamdillah
16 March 2015

No comments:

Post a Comment