Thursday, January 18, 2018

Da Rabon Kabawa Za Su Yi Bauta Wa Mutan Legas. Arewa A Yi Hattara

Ran 25 Maris, 2016, jaridu suka buga labarin wata yarjejjeniya ta noma da kasuwancin amfanin gona da aka cimmawa tsakanin Gomnatocin Jihohin Legas da Kebbi. A yarjejjeniyar, jihohin biyu na shirin samar da kashi saba'in cikin dari na shinkafar da Nijeriya ke bukata duk shekara.
A kiyasin Gomnan Legas, Nijeriya a shekara tana bukatar shinkafa wacce bata gaza ta naira biliyan dari da talatin ba.
Jaridu ba su ba da cikakken bayanin yarjejjeniyar ba. Amma dai na tabbata ba za ta kunshi abubuwa biyu ba:
1. Babu kattin yarbawa da za su baro Legas don su zo aiki cikin rana a gonakin da za a kafa a Kebbi, su duk'a suna ciron shinkafa da sauransu. Kabawa ne za su yi wannan.
2. Babu hekta guda ta Jahar Legas da za a yi amfani da ita. Duk da kasar Jahar Kebbi za a yi amfani, watau fadamunsu da suka kama daga kasar Argungu har zuwa Yauri.
3. Babu Bayarben Legas guda da zai zo don ya koyawa Kabawa noman shinkafa.
Ga kyakkyawan zato, abinda Legas za ta yi shi ne ta ba da kudi da za a biya ladar zufan manoma, da taki, da na'urorin noma da na gyara shinkafar. In komai ya yi daidai, to sai ta shigo wajen kasuwancin shinkafar a Nijeriya da kasar waje in ta kama, a raba riba da ita.
A ta fannin kudi, ba na jin Jahar Kebbi za ta yi raba daidai da Legas a harkar don kuwa yin haka zai kasance akwai kwara: Ga gona, ga zufa kuma ga jari?
A ganina wannan shiri yana dauke da hadari matuka kuma yakamata a sake nazarinsa ta fuskokin siyasa da tattalin arziki. Me ya sa sai Legas ta zo Kebbi don ta noma shinkafa? Me zai hana ta ci gaba da tara kudadenta kawai alabashin in Kebbi ta noma, Legas ta sa kudi ta saya, biliyoyin duk su dawo Kebbi?
Me ya gagari Kabawa ne kam a harkar noman shinkafa da sai sun nemi gudunmawar Yarbawa? Karfi ne ba su da shi, ko basira ko kudi ko dabarar kasuwanci?
Ina ganin cikin abubuwan da na lasafta, iyaka kawai a ce Legas na da kudin zuba jari a harkar. Ko? To wa yace Kabawa sai sun sadaukar da guminsu wa mutan Legas kafin su sami kudin noma shinkafa da sarrafa ta? Ba wasu kafofin samun kudin ne wanda za su wadace su ba tare da sun bautawa mutan Legas ba? Akwai.
Akwai bankuna kala kala wadanda za su ba da bashin noma ba tare da ruwa mai yawa ba. Ko satin da ya wuce, yayana Dr. Usman Bugaje ya yi bayani kan wani shiri da suka zayyana wa jihohin Arewa-maso-yamma wanda ya hada da Kebbi. Hasali ma, wannan Gomantin Tarayya ta ce duk mai son noma ya je ya karbi kudi a banki mai saukin ruwa. Ashe kuwa Kabawa ba su rasa hanyar samun kudin noma shinkafa cikin daraja da yanci ba.
Abinda kawai Kabawa suka rasa shi ne gomantin da za ta tsaya musu: ta tattaro majiya karfinsu, ta ba su filaye, ta hada kansu zuwa kungiyoyi, ta tsaya musu wajen samun bashin da za su sayi motocin noma, irin shuka, taki, magungunan feshi da yankan shinkafar da tanadinta, ta nemo gaggan yanbokonta masu kudi su kafa kamfunna na gyaran shinkafar kamar yadda tsohon gomna Aliero ya yi, sannan da yan kasuwan da za su sayi shinkafar su sayar wa duniya.
Wallahi yadda aka san Kabawa da jarumta wajen yaki tun zamanin da, yin abinda muka lasafta din nan ba komai ba ne in sun sa niyya. Abinda ya rage shi ne yadda za a zaburar da wannan niyyar, da ikhlasi da waccan jarumtar da suka gada tun zamanin Kanta da Abdullahi Danfodio, ba su je maula wajen Yarbawa ba don neman jari daga baya abin ya zame gori da zubar da mutunci da sai da yanci.
Wannan sako bai tsaya ga Jahar Kebbi ba. Mu a Arewa an ci mu da baki - ko in ce da buguzum - an kwace mulki a hannunmu na tsawon shekaru da yawa, an wulakanta mu an nuna mana kyama, an karya tattalin arzikinmu da karfin tsiya. Ko dazun nan na ji Kwankwaso na bayanin yadda ya karbi belin yara yan Arewa sama da arba'in, ciki har da masu shekara 13, wandanda Gomnatin Legas ta tsare tun lokacin da aka yi fadan Mile 12. Ga tsabar wulakanta yan Arewa masu motocin haya da masu kananan sana'a. In sun diro Birnin Kebbi da sunan zuba jari ba mu san yawan fankama, da gori da wulakancin da za su nunawa mutane a cikin gari da gonaki ba.
Yanzu kuma ga shi an zo da yan kudi kalilan za a kwace filayenmu ko a mayar da mutanenmu bayi masu leburanci a gonakinsu alhali kuwa muma za mu iya raya su in mun yi niyya. Kwanan nan gwamnonin kudu ke cewa ba za su bari a yi dazukan kiwo a jihohinsu ba. Amma su za su kawo kudi mu yi musu kwadago a gonakinmu. Tir!
Amma mai rabon shan duka ba ya jin kwab'o sai ya sha. Haka muka yi ta kokarin kan hankalin wasu yan siyasanmu a kan Abiola amma suka ki ji. Haka kuma malammai da yawa suka ta mana kashedi kan Obasanjo muka ki ji. To za a sake kwatawa in ba a yi hattara. Kuda wajen kwadayi ake mutuwa.
A yi hattara. Mu dai baki ne namu. Mun fada, ko a dauka ko a bari. Amma, wallahi, duk gwamnan da ya zame sanadiyyar bautar da mutanensa ko salwantar kimarsu ko darajarsu, ba za mu yafe masa ba har abada.
Dr. Aliyu U. Tilde
3 Yuni, 2016

No comments:

Post a Comment