Thursday, January 18, 2018

Sun Je Lafiya, Sun Dawo Lafiya

Shanu sai shigewa suke, sun dawo daga yamma inda suka ci rani.
A kwana a tashi wannan zai zama tarihi amma mutane na cikin gaggawa. Zaunar da shanun Nijeriya da Ma'aikatar Ayyukan Noma da kanta ta kiyasta sun kai miliyan 19.5 ba wasa ba ne.
Amma in hukumomi na da niyya, a kwana a tashi sai ya yiwu. Ana bukatar dazukan kiwo (grazing reserves) a kowace karamar hukuma a yawancin Arewa. A wadannan cibiyoyin kiwo yakamata a fara canza irin shanun da wasu wadanda suka fi namu gab'a da saurin girma da madara da nama.
Dole me kuma a wannan karon sababbin irin su zame wadanda za su iya jure wa rayuwa a yanayinmu ne ba irin wandanda Turawa suka kawo mana a baya ba kamar Frisians da sauransu wadanda kuma mutanenmu suka gagara rikewa tun zamanin Sardauna zuwa yanzu don rashin dacewarsu. A kasashen Indiya da Amurka ta Kudu akwai nau'in shanu masu kyau amma siyasar kasuwanci ta duniya da mulkin mallaka na zamani ya hana Turawa kawo mana su da fari.
Daga inda makiyayi ya ga saniyar da ta cika wadannan ka'idoji, to har rokonka zai yi ka ba shi iri don nasa shanun suma su amfana.
Daga nan sai batun kiwon gona, watau ranching. Sai a sama wa makiyaya filaye nasu na kansu tunda idan iri ya inganta ba sai an tara shanu da yawa ba za a amfana. Ka ga da filin hekta hudu ko shida, makiyayi zai iya lura da shanun da za su ishe shi rufin asiri.
A takaice ke nan. Amma ana bukatar hakuri da juna, da lokaci, da yin abinda yakamata wajen hukuma kafin hak'a ta cimma ruwa. Dole hukuma ta samar da tsaro, da filaye, da irin shanun da suka kamata, da magunguna da sauran abubuwa na wajibi. Nan da shekara hamsin ana iya cimma gaci in an sa himma.
Lokacin nan, sai dai a rika labarin wahalar da ake sha yanzu.
Mun gode Allah da suka je lafiya bana suke kuma dawowa lafiya. Allah kai mu kaka.

No comments:

Post a Comment