Saturday, January 20, 2018

DUNIYA

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Munsarih: ( - - v - - - - v )
1. Zan sallama na zo gun ki
2. Kan Munsarih zan wak’enki
3. Zan so ki ban du kunnenki
4. Sarki guda mahaliccinki
5. Yai taimako gun wak’enki
6. Da can ina bak’o gun ki
7. Farko ki san nai hangenki
8. Har na yi shawar in gan ki
9. Na sha wuya gun begenki
10. Bak’o ta ya zai zo gun ki?
11. Don jin kalamin zancenki?
12. Ko zan ji taushin muryarki?
13. Har dai na kai in aure ki
14. Na zam a kullum sai na gan ki
15. Domin yawan bin sawunki
16. Maa lii hadaf illaa fiiki
17. Har kin sani na kaune ki
18. Sannan da ciwon in so ki
19. Amma gudu ne aikinki
20. Yangarki gun mai kaunarki
21. Karfinsa duk zai same ki
22. Bai ko da himma sai naki
23. Bai ko da dangi bayan ki
24. Duk wanda yacce bai son ki
25. Jefar shi zan don kaunar ki
26. Kafin na zo ai sun bi ki
27. Duk sun fadan labarinki
28. Duk hannuwa sun kai gun ki
29. Sun mai da ke sabon gunki
30. Sun dau kud’i duk sun ba ki
31. Har martaba don kaunarki
32. Sun yar da ilm sun ko bi ki
33. Sun hau rawa don gangarki:
34. Tuntun tutun tuntuntuntu
35. Ayyaraye ayyediide
36. Sun dulmuye gun koginki
37. Da-na-sani ne kyautarki
38. Duk alkawar ba ya gun ki
39. Nai sallama ban kaunar ki
40. Ban sake neman kallon ki
41. Bar ma batun zan aure ki
42. Don na gani kin zam kirki
43. Bi na ki ke don na k’iki
44. Kin ba ni kyautar kayanki
45. Wak’a ki ke don in bi ki
46. Kin alkawar in na bi ki
47. Komai ya zo man kan sauki
48. Mota da mata kyautarki
49. Iko da izza sa mulki
50. Suna, bajinta ba hakki
51. Naira, Dollar makil banki
52. Tsire, abinci, alkaki
53. Duk za su zo in na bi ki
54. Yawo ko har in kai Turkey
55. In bi ki Paris in gan ki
56. Tsoro garen in na bi ki
57. Yasar da ni za ki d’aki
58. Don babu tabbas kamnarki
59. Dauka ki ke sai an bi ki
60. Sannan ki yasar halinki
61. Dunya ki na ban mamaki
62. Da ma a ce kyan nan naki
63. Har kyan hali duk na gunki
64. Da na cene miki labbaiki
65. Amma tuni nai wayonki
66. Munin hali har ma aiki
67. Duk kyan jiki banzan aiki
68. In ba hali ai ba kirki
69. Kyawun maciji ne naki
70. In an taho ki sararki
71. Sai ai macewa ba miki
72. Sammu ya na nan bakinki
73. Na bar ki ban a kaunarki
74. Na dau Ta’ala Sarkinki
75. Don babu shakka ya fi ki
76. In alkawar bai tamkar ki
77. Shi zai cika har yai auki
78. Sam ba ya renawa aiki
79. In na kira zai ban d’auki
80. In tambaya zai ce dauki
81. Ba ya duhu sai dai haski
82. Kullum ya na nan gun aiki
83. Bayi ya ke baiwa hakki
84. Sannan ya kyauta Maikirki
85. Da za ni kwaso daud’arki
86. Dala dubu duk laifinki
87. In zo garai don na bar ki
88. Ban sake neman kallon ki
89. Fes zan zame duk Ya wanki
90. Ban son ki ban son mai son ki
91. Ba na shiga duk harkarki
92. Na dauki Sarki madadinki
93. Tammat ga wakar nan taki
94. Baiti na Asma’u a kanki
95. Mustaf’ilun faauulaaki
96. Fata guda gun Sarkinki
97. Jinkai a ranar kaitonki
98. Karo Salati Maimulki
99. Kan Mustapha Manzon hakk’i.
Tammat bihamdillah
23 March 2015

No comments:

Post a Comment