Saturday, January 20, 2018

TUBA NAKE

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Sarii’i: ( - - v - - - v - - - - - )
1. Allahu Sarki na iso kan yardarka
2. Bahrin Sarii’i shi na ke son in waka
3. Buri garen tsisshen nufi sai dai naka
4. Farkonta har karshe ta zam kan yardarka
5. Na barsu bayi na taho nan fadarka
6. Na fadi kas karbeni ni ne bawanka
7. Bayi muke kullum a hurmin mulkinka
8. Dau’an wa karhan dole ne sai mun bi ka
9. Ni kam da so nai zakkuwa nan dominka
10. Dube ni Rabbi kar ka boye mun fuska
11. Labbaika Sarki na mayawa labbaika
12. Labbaika ba shariki da zai ban illa ka.
13. Riga garen duk ta rine don sab’onka
14. Duk nai duk’un wari na ke yau a gabanka
15. Kantar jiki har zuciya ma ta dauka
16. Ba ko kwabo balle a ce mun in ba ka
17. Ba ‘yanuwa kamun kafa don kai barka
18. Sai ni kad’ai can zucci ba d’ai tamkarka
19. Ba ayyuka sai dai na kaunar manzonka
20. Ya za ka mun? Shin za ka ce don sab’onka:
21. “Bar nan, tafi” don ban cikin mai da’arka?
22. Ko za ka ce mun ya Aliyu labbaika?
23. Na fadi na duje jikina dominka
24. Nai birgima har na jike dukkan fuska
25. Kuka nake da ma k ace mun, “Kai! Ya ka”
26. Wai ni Ali da ma a ce na yi ka
27. Ya laitani da nai biyayyar manzonka
28. Wauta garen don na bi hanyar makiyinka
29. Wannan guda wannan da ba ya kaunarka
30. Kai mun kashedi kar ya jefa ni wutarka
31. Duk na ki ji na bi shi palon sab’onka
32. Sun kai dubu k’aro dubu ba na shakka
33. Ba na kida don ko ina jin kunyarka
34. Mai kyau kadan ne wanda shi ne nab bi ka
35. Da za ka so zan ba ka domin yardarka –
36. Duk dukiya harma da ‘ya’ya zan mika
37. Sa duk d’iya, don dai ka ce mun labbaika
38. Nai addu’a ya Rabbi domin manzonka
39. Wannan guda sunansa ne bayan naka
40. Wannan guda ka ce: “Taho nan in ganka.”
41. Ya ko tahi har muntahar duk sammanka
42. Albarkacin sunansa ce mun nai barka
43. Murna ta zo don zan yi tsamman rahamarka
44. Murna nake na samu damar in koka
45. Raunin jiki har yai nawa gun bautarka
46. Ga zuciya ba ta yawan yin zikirinka
47. Ga lokaci saura kadan in same ka
48. Ya zan yi ne? Da ma ka mikan hannunka
49. Hali ya canza har na zam mai kaunarka
50. Himma ta zo har ma na iske bayinka
51. Wannan da su kai wa ruwan ni’imominka
52. Sannan ka karo don su samo yardarka
53. Shingen tsari ne maganin duk makiyinka
54. Da ma ka ce kai ma Ali zo in ba ka
55. Tuba nake, murna kamar ranar kallonka
56. Ga safiya ta zo fitar alfijirinka
57. Na hau Sarii na zo bidar albarkarka
58. Mustaf’ilun mustaf’ilun faauulaaka
59. Nai kwar daya baiti a kan son yardarka
60. Sittin da karin uku ina kan wutirinka
61. Tuba nake , tuba ko har in riskeka
62. Nai sallama: Tsira ta zam kan Manzonka
63. Karo iyaye har da dukkan bayinka.
Tammat bihamdillah
24 March 2015

No comments:

Post a Comment