Saturday, January 20, 2018

Fulanin Tashi: Alamar Zaman Lafiya Ya Fara Dawowa

Bara war haka Fulani kalilan za ka gani a labi sun nufi kudancin Arewa daga gabas don tabarbarewar yanayin tsaro da rashin tabbas na abin da zabe zai haifar. Duk a nan muka jibge, yunwa da k'ishin ruwa suka hallaka mana dabbobi sai da ta kai manyan shanu da yawa sun yi ramewar da ake sai da su N3,000 zuwa N5,000.
Amma Allah ya canza al'amarinmu daga tsoro zuwa karuwar aminci kuma ba abin da za mu yi sai mu gode masa. Yau an fi sati daya Fulani na ta wucewa garke garke suna dosar kudu kuma ba za su dawo ba sai ruwa ya fara sauka.
Hakika wannan alama ce ta kwanciyar hankali. Allah ya kawar mana da mugayen da suke raba kan mutane da haddasa yake-yake tsakanin al'umma da barin Boko Haram su ci karensu ba babbaka a lokacin da manyan jami'an cikinsu suke ta kazamar sata a ofisoshinsu. Tsakaninmu da wadannan tsinannu sai Allah ya isa. Allah don girman zatinka ka saukar musu da bala'i irin wanda ka saukar wa Fir'auna da Hamana da K'aruna. Matsiyata jikokin azzalumai kawai.
Arewa mun ga bala'in da gaulancinmu ya jawo mana. Tsammani muke yadda muke son yi wa kowa adalci haka za a mana har muna da'awar cewa a bai wa wasu mulkin su d'ana. To Allah ya yarda ya ba su sun d'ana mu kuma mun ga zahirin hadarin da ke ciki. Tun shekaru 60 su Sa'adu Zungur suke gargadinmu amma hali na gaulanci ya sa muka yi kunnen uwar shegu da su. Allah mun tuba. Allah mun tuba. Allah mun tuba. Kar ka sake kama mu da abin da gaulayen cikinmu suke aikatawa.
Idan dare ya yi nisa, har talatinin dare, na kan ji karar motocin daukan kaya suna wucewa gabas, wasu kuma suna dawowa a kan babbar hanya da ta shiga Arewa-maso-gabas. A baya kuwa tsit kake ji da zarar sawu ya dauke.
Muna sane da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba game da Boko Haram kuma akwai yanuwanmu da ke sansanun gudun hijira da wadanda suke warwatse a gidajen dangi a wurare da dama a Nijeriya. Muna fata lamarin tsaro zai ci gaba da kyautata har kowannensu ya samu komawa gida.
Allah kadai ya san farin cikin da nake ciki ganin mutanen yankina da dangina sun fara ci gaba da rayuwarsu yadda suka saba kuma suka gada. Da na hango shanu a labi suna shigewa yau da safe, ban san lokacin da na garzaya gun su ba, na tsaya a bakin labin ina ganin shigewarsu, garke bayan garke, ina ce musu:
"Aku ye! Allah jippin on jam, kadin O wartira on jam",
wai,
"Sannunku! Allah sauke ku lafiya ya dawo mana da ku lafiya."
Amin ne amsarsu.
Dr. Aliyu U. Tilde

No comments:

Post a Comment