Saturday, January 20, 2018

Ga Iyaye Na Koyawa Yayansu Sata

Duk mutumin da ke son zuriyarsa da alheri ba zai sa 'ya'yansa a kan mummunar tafarki ba sai dai ya cece su.
Iyalin mutum su ne mutuncinsa kuma mafakarsa ta karshe a rayuwa. Don haka duk abinda zai shafe su na sharri hakkinsu ne a kansa ya kare su matukar iyawarsa.
Wannan ita ce tarbiyar da mutanen Arewa suka gada. Ba yadda za a yi uba ko barawo ne shi ya ja yaransa ya sa cikin sana'ar satarsa. So yake kullum 'ya'yansa a ce na kwarai ne. Allah ya jikan magabatanmu. Sun bar mana tafarki nagari. Kai har ya kai da yawa daga cikinsu in ba su yarda da halal din dukiyar 'ya'yansu ba, ba sa yarda su karbi kyautar 'ya'yan.
Kash! Sai dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Tun zamanin Abacha muka fara ganin yadda iyaye suke jawo diyansu don su taya su tafka satar dukiyar jama'a. Irin tsiyar da 'ya'yan wasu gwamnoni suka yi ta yi abin ba a cewa komai. Yaro ne zai sayawa dadironsa mota ta miliyan hamsin a Abuja, ko ya saya mata gidan miliyan dari biyu, ko ya cika but din mota da dollars ya je party, da sauransu. Wadannan yaran, iyayensu sun gama hallaka su.
A karshe dai ga abin kunyar da ya fito wannan satin na badakalar kudin makamai wanda Sambo Dasuki ya jagoranta. Ga 'ya'yan Bafarawa da Bello Halliru a ciki. Dan baya kadan mun ga gwanina Sule Lamido da 'ya'yansa a tsare. Na san kuma ba karshenta ke nan ba.
Akwai gwamnan da ya baiwa dansa kwangila, yaron bai yi ba kuma aka nemi tirzaza akantan ma'aikatar ya salwantar da file din. Da akantan ya ki aka kashe shi. In Allah ya so, ranar da bincike zai gangaro kan gwamnoni, jinin wannan bawan Allah ba zai tafi a banza ba.
Allah ka kare mu da zuriyarmu gaba daya. Ka kyautata tarbiyyarmu da ta mutan kasarmu.
Muna fata wadanda suke kan mulki yanzu da wadanda za su yi a gaba za su kiyaye darajar iyalansu kuma su dawo kan turbar da ma'aikatan farko yan Arewa suka dora aikin gwamnati a kai na rikon amana da sadaukar da kai.
Dr. Aliyu U. Tilde

No comments:

Post a Comment