Saturday, January 20, 2018

MUHIMMIYAR SHAWARA GA DUK MA’ABOCIN CANJI:

A GUJE WA TASHIN HANKALI DON KAR A BA DA DAMAR DAGE ZABEN 2015
Ta
Dr. Aliyu U. Tilde
Hakika guguwar samun canjin shugabanci na ci gaba da kadawa a sassa dabam dabam na kasar nan. Mutane kalilan ne ke tababan samuwar wannan canji a zabe da ke tafi a wata mai kamawa. Kusan duk masana da jama’ar gari suna da yakinin cewa, in sha Allahu, ‘yan Najeriya wannan karon za su yunkura sossai don kawar da gwamnati mai ci yanzu, a samar da wacce a ke sa rai, bisa ga kyakkyawan zato, cewa za ta kwatanta mulki nagari.
Shi kubucewar mulki ba a ta dadi yake zuwa wa wanda yake kan gadon mulki ba. A lokutta da dama in ya tabbatar ya tafka ta’asa da yawa, shi da magoya bayansa za su gwammace a b’arar da kome kowa ya rasa a kan su mika mulki ga abokan hamayya. Mutane sun fara tsoron cewa kila haka zai faru a Najeriya.
Ana cikin wannan zullumin, sai ga Maibaiwa Shugaba Jonathan Shawara kan hulda da jama’a, Mr. Doyin Okupe, ya subut da baka, ya furta cewa akan su baiwa Buhari mulki gara su mika wa sojoji. Nan da nan, fadar shugaban kasa da jam’iyyar PDP suka musanta maganarsa suka nuna cewa wannan ra’ayinsa ne kawai. Amma, an ce magana zarar bunu ce. Kuma in ba rami, in ji makaho, to me ya kawo zancesa?
Bai kamata a yi sake har a yi wa mutane sakiyar da ba ruwa ba. Ya kamata jama’a su yi karatun ta natsu, su yi dogon tunani, su gano hanyoyin da za a iya bi a barar da kwaryar demokradiyya a Najeriya. In sun gano su, to ya zama wajibi su dukufa wajen toshe su.
A yanzu dai babu hanya mafi sauki da tabbas kamar hanyar d’age zabe, a yi ta shiriritar da al’amarin har wankin hula ya kai mu dare, a rasa ya za a yi, sai kawai a ce, to, bari a kafa gwamnatin hadin kan kasa, ko soja su ce sun gaji da iskancin yan siyasa sun kwace mulkin, kamar yadda suka sha yi a baya.
Dokar zabe ta 2010 wacce ke ci yanzu ta nuna cewa hanyoyin da kawai zai sa a d’age zabe uku ne: (1 ), ko dai a samu yanayi na tashin hankali da zai hana yi zaben ko (2), samuwar wata annoba ko (3) wani yanayi na ta-baci wanda ba a hango ba.
Wassu na tsammanin cewa za a yi amfani da rikicin Boko Haram wajen cimma wannan burin. Amma da wuya hakan ya faru don ba sabon abu ba ne, duk da dai an yi sakaci an bari sun shiga Baga sun samu tarin makamai kuma yau din nan ma suna kokarin shiga birnin Maiduguri. Abin da kawai rikicin Boko Haram zai iya haddasawa, a ra’ayi na, shi ne dage zabe a jihohin da ake fafatawa a Arewa Maso Gabas, ba duk Najeriya ba.
A kwanakin nan kuma an yi tsammanin maganar da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan tsaro, Col. Sambo Dasuki (mai ritaya) ya yi cewa zai yi kyau in Hukumar Zabe ta INEC ba ta kammala shirin zaben ba, to ta daga shi sai nan gaba kadan ta yadda za a yi shi ba tare da gazawa ba. Amma hukumar ta fito a take ta ce ita a shirye ta ke, ba za ta dage zaben ba daga watan Fabrairu kamar yadda ta tsara. Ke nan, wannan hanyar ita ma ba za ta biyu ba wa ga duk wanda ke son dage zabe.
Sai hanya ta karshe wacce muka fara ganin alamunta bayan abin da ya faru a Katsina da garinmu Bauchi lokacin da Shugaban Kasa ya zo kamfen. An yi ta jifar tawagarsa hatta a dandalin kamfen din da ledojin ‘pure water’, sannan bayan nan, wasu tsiraru suka fito kan titi suna yayyaga hotunan yan takarar PDP wanda ya sa nan da nan dubban yara suka bisu aka ci gaba da tafka wannan ta’asar.
Gwamnan Bauchi, Mal. Isa Yuguda, ya fito a kafafen watsa labaru ya yi jawabi cewa wadanda suka aikata wannan kazamin aikin yan jam’iyyarsa ce ta PDP, kuma sun yi ne da niyyar su bata mar suna su nunawa Shugaban Jonathan cewa ai ba yi da goyon baya a jaharsa. A takaice dai, in ji shi, siyasar bacel ce ta cikin gida.
Yaya aka yi Yuguda ya san da wannan dabarar? To, ya san cewa ba yau aka fara ba. Da aka yi zaben 2011, a jihohin Bauchi da Kaduna da wasu jihohin arewa da yawa, wasu sun haddasa tashin hankali ta yadda hukumar zabe ta ce ta dage zaben jahohin biyu, duk da cewa wanda aka yi a Bauchi ba wani mai yawa ba ne kuma yanayi ya lafa sosai. Da yawa suna ganin an yi haka ne don a bada dama a kawo dubban sojoji da yansanda da za su taimaka wa jam’iyya mai ci a tafka magudi don ana ganin in an bar gwamnonin biyu da talakawa ba za su kai labara ba.
Ashe ke nan duk wanda ke son lalata harkar zabe a najeriya abin da zai yi kawai shi ne ya samu magoya bayansa su tada hankali sai hukumar zabe ta ce ansamu tashin hankali a wurin don haka an dage zabe tunda tsarin dokar zabe ta ba ta ikon yin haka.
To ta wannan kafar ne nake jin sharri zai iya shigowa. Abin da ya faru a Bauchi ya nuna akwai wadanda ke cikin PDP da za a iya amfani da su a dage zabe, kai har ma da yawa a cikin yan APC din in sun ga kudi. Kudi yau ba komai ba ne a wajen mai son aikata aika-aika irin wannan.
Don haka, ina kira da babbar murya ga mutane, don Allah, don Annabi, don girman mahaifa, kowane dan Najeriya, a kowace jam’iyya yake, ya daure, ya danne kansa da duk wanda ya ke da iko a kansa, kar ya bari a harzuka shi ko ta halin k’ak’a kafin zaben nan, da ranar zaben, kai har sai hukumar zabe ta ayyana wanda ya ci zaben.
Ta kin yarda da harzuka ne kawai mutane za su rushe duk wani shiri na amfani da su wajen kawo cikas ga canjin da ya kunno kai. A sani in an yi rikici aka daga zabe ko aka yi juyin mulki, to jama’a ne za su cutu don su ne za a hanawa mulki na gari.
Ina fata, jama’a za su yi amfani da wannan shawarar, da fatar za a yi zabe lafiya, a kare lafiya, kasarmu kuma ta zauna lafiya.
Haza wasalam.
Bauchi
24 Janairu 2015

No comments:

Post a Comment