Saturday, January 20, 2018

Wakar Dimame

1. A Facebook mutane suna tambayawa
2. Suna so na yo baituka ba k’iyawa
3. Dimame na wake shi ba dakatawa
4. Matsi d’ai suke mun awa takurawa
5. Na dai ba su amsa cikin girmamawa
6. Da yardarsa Allahu zan yo hadawa
7. Dazun ta zo mun wajen Nargutawa
8. Da baitinta sauri tana walkiyawa
9. Na dawo gida nan-da-nan wallafawa
10. Ga Allah guda taimako zan bidowa
11. Halitta bakwai yai su bai ko gazawa
12. Cikinsu halittarsa mu adamawa
13. K’asa ta mu ce kab mu zan shakatawa
14. Muna ci da sha har a kullum mayawa
15. Ruwa har da ‘ya’yan itace dadawa
16. Hatsi har na binne abincin dafawa
17. Na zafi da sanyi muna rarrabawa
18. Kabilu da dama ajam larabawa
19. Niimmu da yai mana sai shukurawa
20. Kasar Hausa noma na ci har sayarwa
21. Kasashe na Borno Nupe zan hadawa
22. Filani da Gwari kasa Jukunawa
23. Da sauran kabilunmu duk zan sakawa
24. Abincinmu wahid kala ba kidawa
25. Kamar ne ka iske ruwa na zubowa
26. Hakannan tuwo yake gun mai ciyarwa
27. Da manya da yara maza ban ragewa
28. Ga mata mukan mika kwano bidowa
29. Da’amin ga don kowace ta iyawa
30. Ta sa tun da zafinsa bai zan gushewa
31. Da laushinsa har ma ya zo gam hadewa
32. Miya ko da taushe da kuka kubewa
33. Mu auna ciki babu ko kyaftatawa
34. Mu cinye da yatsu muna lasasawa
35. Awa saniyata a gonar ciyawa
36. Tana ci da sauri tana had’amawa
37. A can za ta koshi tana hamdalawa
38. Ta kai gaisuwa safe duk kiwatawa
39. Hakan nan muke wa tuwo ba dadawa
40. Ga ci ba kamarsa abin kosasarwa
41. Nasiha gereni taho in gayawa
42. Idan za a yinsa a zan yalwatawa.
43. Kashi ukku zanto kaso gun rabawa
44. Kashi sawa almajirai saddakarwa
45. Kashi baiwa kowa gidan don kilewa
46. Kashi daya kau tanada don dumawa
47. Da sirri amarya ki zanka kulawa
48. Ki kama shi kam don ki zanka tunawa
49. A kul kinka mance nadama ka zowwa
50. Fito man sarai ni ka bar rurrufewa
51. Da karfinmu za nai riko har kwarewa
52. Da sannu ki bini cikin lalamawa
53. A kan maigida ki fice gun kulawa
54. Da safe idan ya taho sallamawa
55. Da wankansa, kayansa fes za ya sawa
56. Da jikkarsa ya yo shirin zai fitowa
57. Ki samai da fuska marar turbunewa
58. Kina mai raha har kina murmusawa
59. Ki ja hankalinsa da sannu ki cewa:
60. Abinci jiranka ya ke kai tahowa
61. Ya zo inda tebur yana tambayawa:
62. “Dafar me akai ne a nan an rufewa”
63. Ki ce mai ka bude da kanka ganowa
64. Ki bi shi da kallo ga murfi dagawa
65. Na kowane kwano yana juyayawa
66. Na farko karo da tuwon zafafawa
67. Miya tai da mai har da kanshi gamewa
68. Na biyu ga su kaji akai bankarewa
69. Da yajinsu jawur akai an rufewa
70. Ya kalleki yawu awa zai zubowa
71. A gefensu shayi na Nescafe ajewa
72. Da mug da flask kin aje ba gusawa
73. Ki zamna ya zamna kuna tad’ad’awa
74. Bukatunki kab can a zucci had’owa
75. Yana fara santi ya zamzam fitowa
76. Kina masa weji kina tambayawa
77. Yana godiya har yana barkid’ewa
78. Idan kinga kwalwa kusan birkicewa
79. Muradunki kan hikima zan fad’owa
80. Da sauri zai biya duk bukata cikawa
81. Dumame da sirri garai zan kulawa
82. A ce mar dimame da hausar kanawa
83. A Hausa a ce zazafe inda kowa
84. “Ari mai wuta biu” gabas anka cewa
85. Fulani ko baaldi suce tun dadewa
86. A ci nai da d’ai ba a tir sai yabawa
87. Wuni za ka wo sai ruwa za ka shawa
88. Da aikinka tsab je ka ba cutatarwa
89. Ana ce da yunwa gari ko kulawa
90. Cikinka a take sai ruwa kai azawa
91. Gaya wa abokai asirin ciyarwa
92. Da tsabta da lada kaza kosasarwa
93. Dimame da baaldi zazafe zan gayawa
94. Ga yara karatu ya zam sauwakewa
95. Ciki tsab da hantsi break har rufewa
96. Ga NEPA sun dau wutar ba sanarwa
97. Da haske na safe “free” ya fitowa
98. A kyautar sa Allah da ba mai tsarewa
99. Da ba a biya Jalla ba ya hanawa
100. Ni’immu ga bayi su mora dadewa
101. Mu d’ora a zancen dimame kumawa
102. A barrak da fareti don jarrabawa
103. Da manya da yara da safe fitowa
104. Suna sanya kaki shiri zak kwarewa
105. Ana ba da oda kafa na bugawa
106. Wuri duka rab raba ka ke ji amowa
107. Da hantsi a ce ai “atanda” tsayawa
108. A sa hannuwa baya ba mai gusawa
109. A dau lokaci mai tsawo gajiyarwa
110. Maza duk da farko kamar sui dadewa
111. Awa biu ba ai ba alamun gazawa
112. Da daidai-da-daidai su kan wo zubewa
113. Da wanda ya karya da shayi fitowa
114. Da mai shan kunu nan da nan sai zubewa
115. Da mai kwai da koda kaza sun gazawa
116. Da teba ta kulle Ibo sai bajewa
117. Bayarbe da pomo ya kai durkusawa
118. Tibi ko sakkwara ta sa sunkuyawa
119. A nan ne na hango maza ba kad’awa
120. Awowi biyar ne sukai ba gazawa
121. Komanda ya sara da ba tamtamawa
122. Ina so in ganku a ofis tambayawa
123. Da me kunka karya da safe fitowa?
124. A cewar su sirrin mu ba bayyanawa
125. Da roko komanda ya na lalamawa
126. Ga oga fadar ta su: ba fallasawa
127. Dimame muke swahe ba dakatawa!
128. A nan ne comanda ya zam mai sanarwa
129. Yana ba da oda a barrack kulawa
130. A duk safiya soja sui zafafawa
131. Dimame abincinsu ba maimusawa
132. Fa kaumi ku ma ku zamka kulawa
133. Dimame aminci ku zamka bugewa
134. Da salama ku zamna ko ba laulayawa
135. Ina ba ku shaida ina tabbatarwa
136. Dimame sadiqi abokin rikewa
137. To tammat fa waka muna son ajiyewa
138. Dari, arbain sa biyar baitatawa.
139. Uban Abba yaita kabar musasawa
140. Ina godiya gunsa sarkin ciyarwa
141. Jikan su iyaye, dimame na dawa
142. Sukan ba mu shi tun muna rarrafawa
143. Ka sa su a Janna dawam ba fitarwa
144. Ka karo salati da yawa ba kidawa
145. Bisa Mustapha shugaban annabawa.
Tammat
4 Fabrairu 2015

No comments:

Post a Comment