Saturday, January 20, 2018

WAKAR MUNAJATI

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
(Ramal: - v - - / - v - -)
1. Ya ilahi ga Alinka
Na yi shaukin in ganeka
Na taho domin bidarka
Damuwa ta na gareka
Sauwake mani Mai Iyawa.
2. Ga dare nan ya rakoni
Ga duhu ya lullubeni
Ga shiru ya kewayeni
Ba ni barci don tunani
Zan wafati ba dadewa.
3. Rayuwata ta tsawaita
Tunda hamsin na shige ta
Ka ga sauran bai yawaita
Nai yakini ta kusata
Zan mace ba na jimawa.
4. Ka yi baiwa: ga iyali
Lafiyar jika, har na hali
Ba fakiranci, da mali
Duk halal ne babu zali
Godiya muke sai dadawa
5. Haihuwata har wafati
Na yi roko don salati
Ba ni sauki kulla waqti
Kar ka tsauraran hayati
Kulla yaimin in kulawa.
6. Ga jiya na ba ta baya
Ga shi yau na zo da kaya
Gobe za ai mun kidaya
Babu dangi babu lauya
Sai shafa'a nai bidowa.
7. Kai ka yo wannan halitta
Kai mu bayi duk usata
Masu sabo gun umarta
Masu roko don bukata
HannuwanKa da ba gazawa.
8. Mu fa sabo ne rabonmu
Kai ko yafewa Karimu
Shi mu ke sa ran Ka bamu
Duk yawan munin halinmu
Kar ka kai mu gurin matsawa.
9. Ga ibada ba amana
Sai riya k'aro hiyana
Ayyukan duk yan kadan na
Har muna kunyar mu nuna
Rayuwa duka ba kulawa.
10. Rayuwa dala ta laifi
Ran tsayawa ba tufafi
Ga Jahannama nan da zafi
Cin kwakwalwa kai ga jaufi
Ba rabo sai tausayawa.
11. Ka kira bayi dukkan mu
Mui biyayya don ta kai mu
Inda ceto ran kiyamu
Mun yi roko gun Rahimu
Yai agaji don girmamawa.
12. Sai fana’i ke gusowa
Duniya kau na cirawa
Bi muke ko da da yalwa
Ba mu koshi sai bidowa
Rabbana mun zam gazawa.
13. Da a na yara samari
Masu himma ga waqari
Ko da dai ba sa kirari
Ko da dan canji yasiri
Sun bidar baiwar yabawa.
14. Yan Adam ne kowanensu
Kai ka dau halin ka ba su
Sun yi tuba kullihinsu
Rabbana kai agajinsu
Sui ibada ba gazawa.
15. Ya Sami’u kaza Basiru
Jinkira mana ya Saburu
Mui dadin aiki kasiru
Har mu tuba wurin Gafuru
Lokaci kafin kurewa.
16. Ayyuka ko da kadan ne
Masu kyau ko da guda ne
In ka karba shamaki ne
Kar mu talfe kar mu kone
Gun azaba mai hadewa.
17. Mun karatu kan talatin
Mun yi buri gun talatin
Mun yi sab'o kan mu sittin
Gun ibada cakulatin
Bangwaro ba ma hayewa.
18. Ba ibada ba gadara
Ba gudu balle dabara
Laifuka duk za Ka tara
Ba Ka cuta d'ai da zarra
Gun hisabi kai ragewa.
19. Ka yi baiwa: ga iyali
Lafiyar jika, har na hali
Ba fakiranci, da mali
Duk halal ne babu zali
Godiya muke sai yabawa.
20. Na kira Sarkin salama
Na yi tuba nai nadama
Ba ni yarda in yi himma
Rayuwata ba zalama
In shiri ba na gazawa.
21. Rabbi kai mu wajen Muhammad
Don Shafa’a sai Muhammad
Annabawa duk Muhammad
Kai iyaye gun Muhammad
Ran da kowa bai iyawa.
22. Kai salati ba iyaka
Kan Muhammadu Annabinka
Har iyalinai kazaka
Muslimina su zo su ganka
Ran kiyamati ba hanawa.
Tammat bi hamdillah.
22 Fabrairu 2015

No comments:

Post a Comment