Saturday, January 20, 2018

Wakar Doka, Tushen Zaman Lafiya

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
(Mutadarak: - v - - v - - v –)
1. Na yaba Rabbi mai jin kira
Jalla, Allahu mai gafara
Kauda duk muguwar kaddara
Ga ni bawa ina yin bara
Ba mu doka a Najeriya.
2. Zamani ne na yau zan fada
Kin biyayya jahala dad’a
Zuciya har idan ta kad’a
Ba abun yi awa ai fad’a
Babu zancen zaman lafiya.
3. Zan yi zance kamar shagube
Yau fa doka mu san ta zube
Duk k’asa gashi an rarrabe
Masu mulki suna lalube
Yanda za mui zaman lafiya
4. Gaskiya zan fada ka’ida
Lalube ba shi yin fa’ida
Lafiya za ta zo har gida
Babu karya bare za’ida
Gun Aliyu maso gaskiya.
5. In ka so zan kwatanta maka
Lafiyar duniyar nan duka
Yin gini ne cikin ayyuka
Ginshiki tubali bincika
In da kyawu gini lafiya.
6. Tubali in ya “bend” ka jiya
Du gini za ya zam laulaya
Ko siminti a ce bai jiya
Babu karfi tsayo zai wuya
Sai zubewa ga baki daya.
7. Duk kasashe muhimmai gama
Masu yalwa da dadin zama
Cigabansu a kas har sama
La sihir kullaha innama
Sun bi dokarsu ba zamiya.
8. Ka’ida ce suke bi duka:
Dora doka bisa kayuka
Martaba, dukiya, rayuka
In ka take su ka sha daka
Rayuwa yari ba lafiya.
9. Kowane gunsu daidai shi ke
Mai talauci biyayya ya ke
Maikudi, tajiri bai sake
In ya laifi hukunci ake
Martaba ba ta sa yafiya.
10. In kasa ka ga ta sunkuya
Ka ga manya suna yin tsiya
Ba tsaron rai bare dukiya
Cin mutuncin mutum ba wuya
Kar ka sa ran zaman lafiya.
11. Kasashe da dama na Ifrik’iya
Sa kudanci na Sudaniya
Har kasar tamu Najeriya
Libya, Santa Ifrikiya
Babu doka bare gaskiya.
12. Larabawa mutan Eshiya
Ga Yaman nan zuwa Syria
Afghanistan hado Chechniya
Ran mutum sai ka ce kurciya
Hargitsi ba zaman lafiya.
13. Mun dadewa da shubka kasa
Mun zata cigaban duk k’asa
An gina muko mun farfasa
Mun barar ba rabo mun rasa
Sai nadama marar gaskiya.
14. Parpaganda ta yanci: ruwa!
Munka sha har muna yin rawa
Mun yi tatil muna yin juwa
Nan da nan munka wo mantuwa
Mun yi waka ta sharholiya:
15. “Yau talauci fa zai daukaka
“Dukiyarmu rabon muduka
“Maida sarki abin caccaka
“Malami, tajiri su duka
“Martaba sai a jumhuriya.
16. Keta doka ya zam ka’ida
Gun mutane da yanci guda
Kangarewa adon maigida
Kan jimawa gari sai kid’a
Rusa mulki muna fariya.
17. Dan talakka kamar tsautsayi
Ya yi mulkinsa mai laulayi
Tangadi, magiya, ga layi
Babu kishi abin tausayi
Cin amana da son danniya.
18. Babu doka ta kaya da rai
Martaba babu sai dai garai
Magudi ba shi zaben kwarai
Jahili ga shi nan sakarai
Ba shi kaunar maso gaskiya.
19. Da yana son zaman lafiya
Sai ya zamto rikon gaskiya
Sanya doka da yin tarbiya
Masu laifi su zam sun biya
Ka ji tushen zaman lafiya.
20. Sai mu bunkasa duk ayyuka
Baiwa yara abin daukaka
Babu gilla da kwaya duka
Sai biyayya, rashin laifuka
Duk kasa kwance sai lafiya.
21. Mu talakka batun gaskiya
Inda son rai cikin zuciya
Hargitsi za shi zo ba wuya
Bin mu doka zaman lafiya
Ka ji kalma batun gaskiya.
22. Mas’ala ko idan ta zaka
Kar mu saurin zama harzuka
Mui ta haushi kamar karnuka
Muna keta doka muna hallaka
Rayuka, dukiya kun jiya?
23. Yanda doka ta ce yan’uwa
Za mu tai inda mai unguwa
Hakimi ba bari har zuwa
Can ga sarkin kasa mui kuwa
Don muna son zaman lafiya.
24. In ko laifi akai wa kasa
Dukiya ko ko rai an rasa
Kotu ce za ta yanke masa
Rayuwa ka’ida ce musa
Hankali za mu zam lafiya.
25. Mui ta watsi da duk rarraba
Mui hadewa da juna gaba
Mu jama’a zuwa shugaba
Rayuwa babu ko fargaba
Za ta dawo kamar can jiya.
26. In ko cewa muke mun kiya
Kowane zai bi son zuciya
Yi da gangan muna fariya
Wai babu doka a Najeriya
Ture zancen zaman lafiya.
27. Masu laifi iri dai suke
Sata da biro kisa ma yake
Shi da harbi ka bar bincike
Zuciya mai bidar mallake
Duniya ba zaman lafiya.
28. Dukiya, martaba, rayuka
Kar mu bata ukun su duka
Gun kalami mu bar zantuka
Duk amana mu zan mun rika
Mui ta himmar zaman lafiya
29. Karshe kirana ga Sarki daya
Kai salama ga duk duniya
Agazawa ga Najeriya
Duk mu zamna cikin lafiya
Kowa da kowa gabaki daya.
30. Zan takaita a gun nan haka
Ga talatin da d’ai baituka
Fa’ilun, Fa’ilun bincika
Gargadi gun mazo laifuka
Masu rushe zaman lafiya.
31. Mustapha Rabbi kai sallama
Kansa manzo dad’o sallama
Kan iyaye Ka zan Ka gama
Har da mu duk cikin sallama
Duniya, lahira duk daya.
Tammat bi hamdillah.
26 Fabrairu 2015

No comments:

Post a Comment