Saturday, January 20, 2018

NASIHA GA BUHARI (III)

WAZIRCI
Ta Dr. Aliyu U. Tilde
Bahari: Hazaj
1. Kasidata ta yamma za ta duba
Waziranci ga mulki mai kwarewa.
2. Wazirci wajibi ne inda mulki
Idan ba shi daɗa sai danƙwafewa.
3. Gama shi shugaba komi halinsa
Na kyau, kwazo da himma ba gazawa -
4. Yawan aiki a kullum za ya sanya
Ya nemo hannuwa don tallafawa.
5. Wazirai ne ka aiki ko da yaushe
Su sa komi ya sambai ba naɗewa.
6. Suna kaiwa su kawo ko da yaushe
A kullum mas’ala tai warwarewa.
7. Ga Mamman nan na hango mas’ala tai
Ta yaya za ya sam mai tallafawa?
8. Da zai aiki kamar shi ko da yaushe
Talakkawa su zam sun walwalawa.
9. Amana zai riƙe, sannan kwararre
Da himma kar ya zam mai karkacewa.
10. Ace zai zo ta hannun yan siyasa
Da ciwon kai a nan ba mai musawa.
11. Kamar shi raƙumi ba ya fitowa
Ta allura idan zan bayyanawa.
12. Da jami’iyyu ukun nan sun yi maja
Da manya sun halarto gun rabawa.
13. Muƙamai kowane ya zo da jeri
Na sunayensa don samun shigarwa.
14. Ka watsar sai su koma sui ta gori
Suna su ne baraden taimakawa.
15. Su zam kurin idan zaɓe ya dawo
Da hannayensu biu za sui naɗewa.
16. Idan ka manta Allah sai ka faɗa
Ka ɗauka kai nadama ba jimawa.
17. A kullum shi mutum in bai da hali
Na kirki sai abokan hallakawa -
18. Fa ko ka ce ya kawo ma na kirki
Ruɓaɓɓe za ya kawo mai gazawa.
19. Ka bar zancen na nesa Muhammaduna
A CPC akwai 'yan munanawa.
19. Su kuraye cikin fatar tumaki
Su na neman amincewar shigowa.
20. Dare in ya zaka sai sui halinsu
Su cinye duk tumakin ba ragewa.
21. Da mamaki mutane sui ta kutse
Su ɗau nauyin da zai kai hallakarwa.
22. Muhamman shawara ce za ni ba ka
Ka noƙe in muƙami an biɗowa -
23. Da kurɗi ko sanayya ko siyasa
Hakannan ne a nassi ba musawa.
24. Tuzuru ne ya zo neman a ba shi
Amana wai ta mata yai ajewa.
25. Iri nai in ya nema sai ka ba shi
Muƙamin leburanci don gwalewa.
26. Muƙami kowane nauyi dabam ne
Ka auna don ka baiwa mai iyawa.
27. Idan ka ɗora nauyi kan kumama
A kullum ka sani zai durƙushewa.
28. Da wus’ah Rabbana ke nasa mulkin
Da dai baya rabo mai danƙararwa.
29. Ƙwararru dole ne kai tanadinsu
Su zam ma ginshiki gun aiwatarwa.
30. A kullum kar ka dau kayan tirela
Ka ɗora kan amale: Bai iyawa.
31. Hakannan ma tirela don ƙiyayya
Ka ce wai mangala ce za ta kaiwa.
32. Asara ce ka janyo ittifaƙan
Hisabi na jira komi daɗewa.
33. A mulki duk muƙami in ka ɗauka
Ka sa ma mai muhalli mai cikawa.
34. Кwararru ma idan ka ba su nama
Wuƙar kar kai garajen mallakarwa.
35. Кwararren in ya zam ba ya amana
Ka korai nan da nan ba dakatawa.
36. Da ɗai kar kai tunanin za ka kunya
Ka zam ka nuna halin mai tirewa.
37. Hakannan ma kashedin 'yan siyasa
Su kawo ma ƙwararru sui kulawa.
38. Hakannan jami’ai ma kar ka barsu
“Civil servants” da haƙƙin aiwatarwa.
39. Amana kar ka ɗauka du ka ba su
Nadama za ta zo ba a jimawa.
40. Riƙe wus’a da ƙarfi kar ka ƙyale
Asiri ne na Allah mai ƙwarewa.
41. Hakannan kar ka saurin yin aminci
A kullum sa ido don jarrabawa.
42. Biyun nan in ka kama za ka dace
Ina ma gargaɗin mai tausayawa.
43. Da fatata a zucci kulla yaumin
Ta’ala kar ya bar Mamman ga kowa.
44. Ya kai mai agaji kan duk lamurra
Idan sun zan wuya yai sauwakewa.
45. Da ƙarin sallama kana da tsira
Bisa Manzonsa har ranar tsayawa.
Tammat bihamdillah
12 March, 2016

No comments:

Post a Comment