Saturday, January 20, 2018

Shirin Kwankwaso da Ganduje Ya Yi Kyau

Na ji dadin shiga tsakani da gwamnoni suka yi don sasanta Sanata Kwankwaso da Gomna Ganduje. Sulhu shi ya fi, in ji mahaliccinmu. Wannan ita ce fatarmu tun bullar wannan fitina.
Masu sharhi kan siyasar Kano sun nuna cewa yan zuga ne suka sa abun ya ta'azzara tun da fari kuma a yanzu ma ba su ji dadin sulhun ba. Ni a nawa karamin tunanin, laifin manyan nake gani in har za su bar mabiyansu suna tunzura su zuwa halaka.
Gomna Ganduje yakamata ya san shi Gwamnan mutum sama da miliyan ashirin ne. A cikin wannan yawan jama'a Allah ya dau mulkin ya ba shi, shi kadai. Zai zame babban cin amanar ubangiji idan ya bari wani abu ya dauke hankalinsa har ya jawo masa matsala ta yadda mulkin jahar zai gagare shi. Dole ya yi aiki da kowa kuma mutanen Kwankwaso sun zame kanne a gunsa da ya zame dole ya nuna halin wa garesu kamar yadda zai nuna wa masu daawar goya masa baya. A karshe, kar ya mutumta sila. Kwankwaso shi ne silar mulkinsa, duk da cewa Allah ne ya bayar. In ya rena sila, ya rena mai bayarwan ne.
Shi kuma abokina Sanata Kwankwaso, yakamata ya gane cewa ya kai matsayin da siyasar Nijeriya ce zai sa a gaba, gadangadan, ba ya rika waigawa baya yana kallon matsayin gwamnan Kano ba. Alhamdulillahi, ya wuce nan. Ya yi ya gama lafiya. Yan Nijeriya sun shaida mai aiki ne, ya yi an gani. Kuma cikakken dan siyasa ne don munga yanda ya jagoranci yakin wargaza PDP. A kyakyawan zatonmu, yana da rikon amana gwargwadon halin da mulki a Nijeriya zai bukata duk da cewa an adam ne, ba zai cika goma ba.
Yakamata Kwankwaso ya sani cewa a nan Arewa, yana daga cikin nagaba a wadanda muke musu fatar shugabancin kasar nan a nan gaba in Allah ya yarda. Muna ganin kamar shi ne Tinubunmu. Ai da aka kasa kuri'u na tsaida dan takarar shugaban kasa a APC, wa ya fi shi kuri'u banda Buhari?
Don haka, kar Kwankwaso bari siyasar Kano ta rage masa kima a idanunmu. Kar ya rika gudu yana waiwaye. Tsakaninsa da Kano, dattijantaka. Fakat!
Don Allah kar wadannan shugabanni namu guda biyu su sake irin wannan abin kunya da kauyanci. Zubar da girmansu ne a wurinmu.
A karshe, su biyun su san ka'idar sabawa sulhu a musulunci: wanda ya ketare iyaka a tsakaninsu ya sani al'umma za ta janye goyon bayanta gare shi, kuma Mahaliccinmu ya ce a yake shi sai ya dawo kan lamarin ubangiji na sulhu.
Wannan kukan kurciya ce...
Dr. Aliyu U. Tilde
22 March, 2016

No comments:

Post a Comment