Saturday, January 20, 2018

TA'AZIYYAR ABUBAKAR LADAN ZARIA

Dr. Aliyu U. Tilde
1. Tabaraka Rabbana Kai ke da mulki
kaza Ikon da ya wuci kintatawa.
2. Da farko a tsari ka halicci kushewa
Rayuwa kau kayo ta a jarrabawa.
3. A duniya har kazalika ran Kiyamu
Ta Yaumul Hashri ran da ake gamewa.
4. Don karatu ne da na ji cikin Tabara
Ga Malam Maiwada haka tun dadewa.
5. Kowa ya sani rayuwa dad’a za ta kare
Dacinta har dad’inta suna gushewa.
6. Su kan yanke a kan wa’adi rubuce
Babu mai ikon dadawa ko ragewa.
7. Da zarar ya cika kowa bai tsayawa
Batu ne da anka yi shi da jaddadawa.
8. A Kur’ani hakaza a cikin hadisai
An nanata miraran ba kidawa.
9. Duniya ce muke bin ta tana gusawa
Ko ba gudunmu ta na gaba har gushewa.
10. Mutuwa kau tana biyo mu muna cirawa
Da sannu za ta cim mana ba dadewa.
11. Maganag ga Ta’ala yai ta cikin Kitabi
Gargadi nasa duniya ba mai musawa.
12. Ta taho ran Talata ta tarad da Malam
Abubakari na Maccido mai gushewa.
13. A nan Kwarbai ta Zariya anka haifai
A nan kuma ta taras shi yana jirawa.
14. Ziyarata ta karshe da nai gidansa
Na samai nan a kwance ba ko tsayawa.
15. Ya ce Tilde ciwo da tsufa sun ishe ni
Na ce Allah gareka ka zam rikewa.
16. Ashe ajali ne ke rika kewayarsa
Mun ban kwana wuni shida kan cikawa.
17. Da taz zaka yai kiran d'a nai Aliyu:
“Rike hannu jikin na dada zafafawa.”
18. Sai d’ansa ya kama hannu nai da sauri
Ya ce zan salati baba kana mayawa.
19. Nan habibuna ya dau Kalmar Shahada
Ashe mutuwa tana tafe ba jimawa.
20. Da kama hannun ba ai minti biyar ba
Azra’ilu yai aikinsa na kaddarawa.
21. Aliyu ya san baba ya tafi ba tsayawa
Tafiya kuma bai da ikon waiwayawa.
22. Da sauri ya lullube shi ya na salati
Sai ya ruga can gidansu ya na sanarwa.
23. Nan da nan duniya ta shaida tai asara
Gurbi nai Habu yana da wuyar cikewa.
24. Ran ashirin da hudu ga watan Disamba
Zancen rashin ya baje sai tausayawa.
25. Ga Fatihu shi ya sa shi a dandalinmu
Da ganin post din sai shiri ba dakatawa.
26. Zuwa Zaria ko a riski jana’izarsa
Hakki nai na karshe dad’a girmamawa.
27. Ina tuki zuciyag ga tana tuna shi
Da wakoki nai hawaye sai zubowa.
28. Idan na tuna zuwa nasa Bauchi tamu
Da zaman da mukai gidana shakatawa.
29. In na kamo baiti Habuna sai ya sabke
Idan ya dire na kan rika tambayawa.
30. Kad'an da kad'an mukai nazarinta wakar
Kadan da duhu yana dad’a haskakawa.
31. Tuki na ke tunani na dada zakkuwa mun
Sannan hawaye a kunci sai zubowa.
32. Niz zam saahibinsu fitowa Naibawa
Na kai ga Gada zuwa kuma Tamburawa.
33. Karfi, Imawa da Kura na wucesu
A motata da sauri ba dakatawa.
34. Ciromawa Dakatsalle ba zan tsaya ba
Gwarmai, Tarau, Kwana sai dai wucewa.
35. Kunkumi, Tashar Yari, hada da Gwanda
In nai tunani sai hawaye har Dogarawa.
36. Kwangila na wuce ta bisanta malam
Danmagaji Tukur-Tukur duk ba tsayawa.
37. A Kofa na dau hanya ta Jos domin in yanke
Zuwa Kwarbai da hanya ba tambayawa.
38. A can na ishe ana ta shirin a kai shi
Nai alwala nai jira don kammalawa.
39. Da Karfe goma cif anka fito da Malam
Cikin makara kan kafada an yo azawa.
40. Muhammad Kumo ya ce gafarta malam
Hotunan turo a Whatsapp don tunawa.
41. Ni ko da naa dauka sai in zan azawa
A Yanargizo hanya mara jinkirawa.
42. Farko mutan rakiyar su kadan ne
Kan kwabo sai jama’a suka zam fitowa.
43. A kai salla da wurwuri anka kai shi
Makwanci nai na k’abru da ba fitowa.
44. Cikin makwanci anka binne an du’a’i
A tsaitsaye an wa’azu a zam kulawa.
45. Rabbana tabbatar shi wajen su’ali
Tamabaya duk ya amsa ba figicewa.
46. Dansa Ibrahimu yaa rakani gidansu
Gaisuwa gun danginsa da girmamwa.
47. Tambayoyi kaninsa Ahmadu shi ya amsa
Na ‘yan jarida jikinsa ya na kadawa.
48. A tsaitsaye ya bamu tarihin habibu
Shekaru tamanin da biyu kafin cikawa.
49. Abubakar ya yi Middle kafin fitarsa
Ziyara kasashen Africa da zagayawa.
50. Dawowarsa ne ya wake dukan Africa
K’adiman har ga turawan mallakewa.
51. Cinikin bayi kaza haka yai bayani
Fasihi har idonmu suna tud'owa.
52. Da jarin da Ingila tas saka domin hanashi
Da jayayyar Faranshi wajen zak’ewa.
53. Jamus, Sipaniya, Potigi har Amurka
Bare Esha har kasashen Larabawa
54. Karshe Habu ya ce Allah yai halinSa
Muyassiru yaz zaka don sauwakewa.
55. A Turai an ‘yanta bayi har Amurka
Bak’i ya san Ilmi kazaa ga walwalawa.
56. Kazaa kuma yai bayanin wagga sabga
duhun yakin duniya mai hallakarwa.
57. Da yadda ‘yan Africa sukai shigarsa
Mutuwa hutu gurinsu abin bidowa.
58. Da yadda akai gumurzu Turai da Esha
Ga Indiya sa da Burma wajen macewa.
59. A karshe yai kiran Turawa da karfi
Don taimakawa Africa wajen hadewa.
60. Kaana Habu ‘yancin kai yai wa waka
Kiranai don ci gabanmu da karfafawa.
61. Da waka tai ta ukku ya wa gwarazen
Africa kasa guda ba bangarewa.
62. Kuma ya kira duka manyan kasashe
Su kawo na su daukin ba dakatawa.
63. Ya ja kunnen Amurka cikin dabara
Ga Lincoln ya yi shaidar tausayawa.
64. Ya ambaci daular can wace ba kamarta
Karfi da kurdi gaba daya ta fi kowa.
65. Da tai sama tafiya ta ke ba tsayawa
Ta na mai da duniya duka sa’idawa.
66. Karshe k’as anka ganta marar darajja
Ta durkushe gaba daya sai macewa.
67. Na taba ce Habu Allah gafarta malam
Wace daula ce? batunka na zam rikewa.
68. Ya ce: Romawa nai nufi don can k’adimu
Ba d’ai daula kamarsu ta maguzawa.
69. Dube ta yau ta gama ba a batunta
Gun Balascouni ta koma ko mafiyawa.
70. Na ce sadaqta Abubakar ni na fahimta
Allah ya k'aro ilmu da budadawa.
71. Mun zancen k'asida ta al’adun kasarmu
Cikinta yai zurfin fahimta har kwarewa.
72. Ya kira kowa ya tashi ya ba da himma
Ga ci gaban al’adunmu da ke gushewa.
73. Masaka, makeranmu kaza manoma
Takalma har tufafin da muke sakawa.
74. Basira, ta’abiri da murya sai Habuna
Baiwar Mutanabbi garai bar tambayawa.
75. Tammamu, Buhturi kawo ga Shauki
Jinjina za sui gareshi da durkusawa.
76. Gun fasaha Imru’ul Qaisi ya cira mai
Kaza Farasdaqu har da dukkan sha’irawa.
77. Gun waka Habu na sha’awar Mu’azu
da Zungur yai batunsu da girmamawa.
78. Shin a Africa gaba daya za mu samu
Mawakin da yah hadeta da kewayawa?
79. Sannan da diwaninta guda a wake
Da ba fajirci cikinsa da aibatawa?
80. Allah jikan shi ka haskaka kwanciyarsa
Hadamu da shi gaba daya ran tsayawa.
81. A tutar Sayyidinmu mijin Hadiza.
Muhammadu Shugaban duka Annabawa.
82. Diyansa da yab bari sha daya duniyan nan
Aliyu har da Maryam Jalalu ka tallafawa.
83. Abdulrahman, Musa kawo Muhammad
Da Ibrahim game su da tausayawa.
84. Da Abdullahi, Fatima sa Hadiza
Hauwa’u, A’i tsare su da tabbatarwa:
85. A kan sunna ta Manzo har da ilmu
Sana’a, amana Rabbi Ka zan dadawa.
86. Ga Bilkisu matarshi da ke takabba
Kawo mata agajinKa da bai gushewa.
87. Hakika kaninsa Ahmadu yai jawabi
Sahabi dangi gare shi maso rikewa.
88. To Allah taya su su zan rikewa
Ka arziki zuciyarsu da tausayawa.
89. Dade su da arziki hakuri da yalwa
Nauyin marayun a kullum ba ajewa.
90. Mu ma aminai kazalika ma abokai
Mu zam masa addu’a gun ambatawa.
91. Da kai dauki ga ahlinsa bisa bukata
Ta boye da wacce za su yi bayyanawa.
92. Ni ma Mujibu na kira Ka cikin daren nan
Rika mani nau diyan bayan gushewa.
93. Ka sa su a gaskiya kana da dina
Sui ilmi kuma sui halal ba cutatarwa.
94. Kaza dukkan maraya da ya ke kasar nan
Sanya shi bisa ga hanya Mai Iyawa.
95. Mu ma iyaye Rabbi haskaka zuciyarmu
Da annurin shiriyarKa da bai dishewa.
96. Kasarmu ta zamna lafiya domin salati
Fitinnu duk su barmu mu zan natsawa.
97. Taaziyyar Sahabi nan niya zan tike ta
Baiti yawan asma’u da ba dad’awa.
98. Aminin Abubakar Ladan Dokta Tilde
Ya k’irota daren bakwai bayan gushewa.
99. Allah jik’an iyayena kaza duka salihina
Da salati kan fiyayyen Annabawa.
Tammat bi hamdillah!
Kano
9 Disamba 2014

No comments:

Post a Comment