Saturday, January 20, 2018

YABON SAYYIDINA

Ta Dr. Aliyu U. Tilde
1. Ina mutan Muhammadi
Ga mu a shahrin mauludi
Na haihuwarsa Ahmadi
Sayyidina Muhammadi.
2. Ku zo mu waake Sayyidi
Manzo na Allah hamidi
Rahma garemu majidi
Nabiyyuna Muhammadi.
3. Mun yi baraa gun aalimu
Mahaliccinmu haakimu
Allah, Kadiiru Munazzimu
Da yay yiyo Muhammadi.
4. Tambayataa ni bashari
Bani hikmaa kal bahari
Baiti su zoo kal madari
Yayin yaboon Muhammadi.
5. Tsira amin/ci kullihi
Garai da duk/kan ahali
Gama da duk/kan sahbihi
Da ummatin Muhammadi.
6. Na zo da taa/rin sona
Kaza da duk/kar kauna
Waraqa al/kalamina
Zan yi yabon Muhammadi.
7. Ahmadu shi/fitila ce
Mu bar dukkan/ cece-kuce
Kowa ya bii/ shi ya dace
Tafarki nai Muhammadi.
8. Masu yabo domin kwabo
Su kan yabo domin rabo
Mu kam rabo domin yabo
Na sayyadinmu Ahmadi.
9. Allah ya nufoo/ rahmarsa
Ta sabka kan/ bayinsa
Da sun bace duniyarsa
Gaban zuwan Muhammadi.
10. Sai ya dauko Kur’ani
Ya ba Ruhinsa Amini
Ya kai gurinsa Amini
Sayyidina Muhammadi.
11. Cikin watan Ramalana
Duniya dare ba rana
Bakwai a kan ishiruna
Ya zo wurin Muhammadi.
12. Wannan sako na gaskiya
Daga Sarki Mai Gaskiya
Ya cancanci mai gaskiya
Dan Amina Muhammadi.
13. Shi shugabanmu Ahmadi
Tun fil azal an tanadi
Domin zamansa muqtadi
Abin koyi Muhammadi.
14. An wanke mar duk zuciya
Domin ta zam muhimmiya
Ta dau sako na gaskiya
Sayyidina Muhammadi.
15. Rabon shedan duk an cira
Jibrilu d’ai take jira
Sun yi gamo Kogon Hira
Faarin sakon Muhammadi.
16. Duniya ta zam sabuwa
Haske zai kore duhuwa
Kowa ya zo don karuwa
Wurinsa ya Muhammadi.
17. Haske ya maye Arabia
Dukkanta haar Syria
Kaza da Rumm har Persia
Sun dau sakon Muhammadi.
18. Ga kasashe na India
Kaza da dukkan Asia
Mu ma Africa mun biya
Tafarki nai Muhammadi.
19. Turai kaza Amerika
Da k’i da so ba shakka
Sakonsa sai son barka
Yana fice Muhammadi.
20. Jamaa sai/ mui godiya
Da baiwa/ mafificiya
Da Allah muu/ yas sanya
A umma tai Muhammadi.
21. Baiwa ce da duk al’ummu
Da sun so a cee sun samu
Amma mune aka bamu
Mu zam kason Muhammadi.
22. Godiya ga Allah wahidi
Salati biyayya ga wajidi
Mu riki sakon tauhidi
Na Sayyidi Muhammadi:
23. Babu ilah sai Allah
Mahalicci Shi Jalla
Ma’abudi da Kamala
Shi yay yi yo Muhammadi.
24. Littifinsa ne Kur’ani
Dace da dukkan zamani
Kyautar Sa cee Rahmani
Ga alummar Muhammadi.
25. Mu’jizarsa ce Kur’ani
Da ba mutum ko jinni
Zai yi shi koo da mu’ini
Sai dai Allahu wahidi.
26. Ya tattaro/ dukkan ilmu
Da hikma/ ta al-Hakamu
Amfanin Arab/ da ajamu
Na zamanin Muhammadi.
27. Da shi ya kira danginsa
Kan shi ya sa sahabbansa
Wasiyya ga duk mabiyansa
Har abadin Muhammadi.
28. K’aro da bin sunnarsa:
Bayani a kan sakonsa
Maganarsa ko yardarsa
Bare aikin Muhammadi.
29. Biyun ga suuu ne shiriya
In ka barsu kaaa bar hanya
Rike su tammm a zucciyaaa
Su ne sakon Muhammadi.
30. Ka zam mutum na salama
Ilmu, ibada ga himma
Don ci gaban al’umma
Ta Sayyidi Muhammadi.
31. Kauli kaza har amali
Ga kyau ka zam mu’ahhali
Ka zam mai kyan muamali
Da ummatin Muhammadi.
32. Zucci ka so Muhammadi
Cikin wuyaa ko dadi
Zam salati ga ahamdi
Da ahalin Muhammadi.
33. Ina ta kaiton/ halina
Babu yawa/ aikina
Sai dai bidar/ aljanna
Albarkacin Muhammadi.
34. Allah taya mun Rabbi
Ka sauwake min hubbi
Kwalwa ta zam ba gurbi
Cikin kaunar Muhammadi.
35. Kaza da dukkan ahlina
Su zam kaunar manzona
A cikin dare ko rana
Su zan rikon Muhammadi.
36. Kaza su so su ahluhu
Ashabuhuu siddiquhu
Umaruhuu Usmanuhu
Mukarraban Muhammadi.
37. A nan wajen zan dakata
Albarkacin wannan wata
Allah jikan magabata
Su zam hannun Muhammadi.
38. Gobe idan an tsanani
Kowa na neman tsani
Aiki ya gazaaa mizani
Mu sam ceton Muhammadi.
39. Na yi godiya gun Allah
Tsira amincin Allah
Su tabbataa don Allah
A kan Amin Muhammadi.
40. Ya rabbana salli ‘ala
Khairil anami man ‘ala
Alas samawatil ‘ula
Bi izni Rabbihil ‘ali.
41. Wa alihi wa sahbihi
Wa zaujihi wa hizbihi
Wa kulli aali hubbihi
Maassalamil akmali.
Tammat Bihamdulillah
4 January 2015

No comments:

Post a Comment